Connect with us

BIDIYO

AREWA HIP-HOP: Mawakan Arewa Ba Su Da Hadin Kai – Abokina X_Dough

Published

on


Tare da Umar muhsin Ciroma 08104314052, [email protected] Intagram @smartkid.skd_official

Shahararre kuma sanannen wakin hausa hip hop Ahmad Ibrahim Babajo wanda aka fi sani da Abokina X_Dough, yayi maganganu masu mahimmanci musamman akan yadda mawaka arewa kansu yake a rabe, ya kuma ba samari shawara da su daina kwaikwayon al’adun turawa musamman gurin shigar su sadan kunne da dai sauran, ya bayyana hakanne a wani muhimmiyar tattaunawar da sukayi da wakilinmu Umar Muhsin Ciroma, ga yadda hirar ta kasance:

Toh da farko dai masu karatun mu zasu so susan cikakken sunanka, da kadan daga cikin tarihinka.

To ni sunana Ahmed Ibrahim Babajo

Kuma haifaffen garin kaduna cikin birnin zazzau, a Kaduna na girma, mu a gidan mu mu biyar ne mata hudu ni kadai ne na miji.

Ko zamu san abun da yaja hanka link aka fara waka?

Toh ni gaskiya tin ina yaro mutun ne mai sha’awan jin wake wake da kokarin rera wa, da baran manta ban a fara yin waka a studio tin ina dan Jss 1, gaskiya wakan lokacin ta karbu sosai a makarantan mu lokacin.

Ko zaka iya gaya mana sunan wakar?

Sunan wakan TIRED OF RUNNING.

A wani shekara ta fara waka?

Na fara waka ne a shekaran 2009.

Zamu so muji kadan daga cikin tarihi karatun ka?

Ni nayi firamari dina a Capital School dake kaduna, daga nan kuma na koma karshi dake Abuja nayi sakandiri, sana sake dawo wa kaduna nayi imperial college, nayi karatun a Ghana telecom unibersity, anan nayi jami’a.

Ya kake gurin kokarin hada waka da karatu.

Abu ne mai wahala gaskiya, amma haka nake kokartawa.

Koza iya lissafa mana sunanyen wasu daga cikin wakokinka?

Darasi

Illuminati

Tuwon zafi ft NT4 ghana

My life

Yallabai ft Classik

Lobe me later

Kwanan nan na saki wani sabon midtape Album Mai suna AOTM akwai wakoki goma sha shida16, ya fita yana kasuwa.

DARASI na daya daga cikin wakokinka da suka karbu matuka ako ina musamman nan arewa, ko zaka iya gaya mana darussan da suke kunshe a ita?

Darasi waka ce dana yi da Freestyle inda a cikin nake gabatar da kai nag a al’umma baki daya.

Me Kalmar AOTM take nufi?

Ma’anar AOTM Aboki on the Mic.

Wasu irin kalubale kake fuskanta a matsayinka na mawakin arewa?

Gaskiya mawakan arewa gaba daya bamu da hadin kai, kuma bama samun karfin gwiwa daga manyan mutanen arewan.

Ko zaka iya gaya mana dalilin dayasa kace mawakan arewa basu da hadin kai?

Eh, ni ma bansan dalilin da yasa Babu hadin kai a tsakanin mu ba.

Amma wani kokari kake na ganin kun samu hadin kai gaba daya?

Idan mun hadu ina cire girman kai inje mu gaisa kuma in basu kwarin gwiwa kuma ina nunan musu da ina yin haka ne saboda dikan mu ‘yan arewa ne. ni kwata kwata ban gasa da kowa ko in hada kaina da wani dika ni banyi haka.

Zaka iya gaya mana wasu daga cikin lambar yabo daka samu daga lokacin daka fara waka kawo yanzu?

Eh, Har nagama secondary school ni nake cinye best artist a wancan lokacin, kuma na samu Kaduna best rap actist 2016, da dai sauransu.

Wani irin kalubale ka fuskanta daga lokacin da ka fara waka?

Na samu matsaloli da dama a gun dangi na, Saboda na fito daga babban gida a zaria

Kuma bamu gaji sana’ar waka ba. Dan haka ban samu goyon baya ba daga yan uwana a harkan waka, Duk wakoki na ni ke rubutawa kuma nike daukan nauyin kudin buga abuna.

Ya ka kalli duniya lokacin da aka fara gayyatar ka wasanni?

Gaskiya na samu kwarin gwiwa da a ka fara gayyata na wasanni a biya ni Kuma a karramani yanda ya kamata.

Wani irin kokari kake don ganin ka faranta ma masoyanka musamman ta hanyar sada zumunta?

Ina kokarin sada zumunci ga masoyana a kafofin sada zumunta, Ina kokarin amsa wasikun masoya kuma na mai da musu martini dik wanda zan iya saboda sakonni ke shigowa iri iri da yawa sosai daga Nijeriya har sauran kasashen African.

Baya ga wakan da kake yi kana da wani sana’a ne?

Ina sana’ar kai kawo da ababen hawa kamar mota da keke napep Wanda ake mun aiki dasu, Sai shows da featuring da akayi, Kuma a harkan wakan a kasamu Dukiyar da ake sana’ar dasu.

Ko zamu iya sani sunan wasu muhimman garuruwan da kaje wasanni?

Kano, Kaduna, Sokoto, Kebbi, Abuja, Nasarawa, Jos, Zamfara, Minna, Katsina, Lagos.

Daga yanzu zuwa nan da shekara 5 wani kalan hidima kake shirin ma Arewa hip hop?

Nan da shekara 5 insha Allah zamu sa duniya hankalinta ya karkata akan hausa hip hop.

Kana da kungiya ne ko kana zaman kanka?

Bani da kungiya ni kadai nake A buna amma Amma ina da kyakkyawan mu’amala da arewa mafia, mun fahimci juna dasu.

A matsayinka na shahararren mawakin hip hop kuma abin koyi ga wasu al’umman, wani irin shawara zaka bama matasa masu tasowa wa’inda suke da ra’ayin waka?

Shawarana shine matasa suyi kokari su bada himma wajan makaranta da kuma su daina kwaikwayon mawakan kasashan waje.

Ko za muji dalilin da yasa kace matasa su dai kwaikwayon mawakan waje?

Saboda da yawan matasan mu suna karya harshe kuma suna son shiga irin nasu, Saka dan kunne, Ass down da sauran su, Wanda ba al adan malam bahausha bane.

Toh bari mu dan taba nishadi kadan akan abun daya shafe ka, wani kalan mota kafiso? Wani irin abinci kafiso? Wani kasa kafi sha’awar kaje?

Ina sha’awar black Car.

Abinci kuma inason tuwo da Miya.

Ina sha awar zuwa America dan karo ilimin harkan waka.

Daga karshe kuma me zaka cema masoyanka?

Ina ma kowa fatan alkhairi kuma a ci gaba da bamu goyan baya shi zai kara min karfin saka Hausa a cikin map din duniyar mawaka, Kuma su bini a social media na domin samun sababbin wakoki na. Instagram ddough_abokina. Twitter da facebook ma haka. Na gode.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai