Connect with us

KASUWANCI

Yadda Na Samu Alheri Da Noman Shinkafa –Jega

Published

on


Tsohon shugaban ma’aikata na jihar Kebbi Buhari Jega ya bayyana cewar ya samu alheri daga yin noman shikafa, akarkashin shiringwamnatain tarayya na yadda take taimakawa da kudaden rance.

Jega ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) bayan da Ministan yada labarai da kuma al’adun gargajiya Alhaji Lai Mohammed da wata tawagar ‘yan jaridaan zagaya dasu, a gonar ta shinkafa mai kilomita 20, kusa da Birnin Kebbi, ya ce ya shiga harkar gona bayan ya yi ritaya daga aiki.

Kamafanin dillancin Nijeriya ya bayyana cewar Ministan yada labarai shi ne ya jagoranci ‘yan jaridu zuwa Kebbi, a wata ziyara ta ganewa ido, akan ci gaban da ka samu dangane da aikin gona, a jihar, Kamishinan aikin gona ne Alhaji Mohammed Dandiga ne ya jagorance su lokacin da suke kewaya gonar.

Tsohon ma’aikacin ya ce, ya shiga harkar noman shinkafa ne bayan yayi ritaya daga ofis, sai kuma ya yi amfani da damar da gwamnatocin tarayya da na jihohi, suka bullo da shi ta hanyar bada rancen kudaden noma.

NAN ya ruwaito cewar tsarin da babban bankin kasa ya bullo da shi na ba mnaona rancen kudaden noma, shugaban kasa Muhammadu Buharinne ya kaddamar da shi, a Birnin Kebbi ranar 17 ga watan Nuwamba 2015.

A karkashin tsarin CBN ta ware naira Bilyan 40 daga cikin Naira bilyan 220 da aka ware domin kananan masana’antu, za a ba manoma ne akan ribar kashi 9 cikin 100 ko wacce shekara.

Shi tsarin yana smar da kudade irin shuka, taki, sauran kayayyakin noma, da kuma bada shawara ga manoma wadanda suka yi rajista.

Jega ya ce yana farin cikin domin yana da gonaki uku na shinkafa a wurin da yake, akai mai eka 13, eka 10, da kuma eka 7.

Lokacin da ake gyara amfanin gonar a shekarar 2017, ya samu buhu 400 daga gona mai eka 13, 200 daga gona mai eka 10.

Jega ya bawa ma’aikata shawara su yanke shawarar yin noma bayan sun yi ritaya daga aiki, kuma ya kmata su fara da wuri, tun kafin su yi ritaya daga aiki.

 


Advertisement
Click to comment

labarai