Connect with us

KASUWANCI

Gwamnati Za Ta Tallafa Wa Masu Noman Dankalin Turawa

Published

on


Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na bayar da gaggarumin tallafi ga manona dankalin turuwa don kara yawan dankalin da suke noma wa da kuma bukasa karuwar kudaden shiga gare su a wannan shekarar ta 2018.

Shugaban kungiyar masu noman dankalin turawa na kasa (Potato Farmers Association of Nigeria, PORFAN) Cif Daniel Okafor, ne ya furta haka a zantawarsa da ‘yan jarida ranar Litinin a Abuja.

Ya ce, tuni gwamnati ta shigar na kungiyar cikin tsarinta har kuma ta raba wa manoman irin dankalin turawa mai inganci tare da jure cuttutuka.

Okafor ya kuma bukaci manoman dankalin dasu bayar da bayanan girman gonarsu da jihar da suke gudanar da noman ga ma’aikata masu daukan bayanai domin gwamnati na shirin amfani da wadannan bayanai domin tallafa wa jihohi wajen bukasa noman dankali a kasar nan.

“Ba kamar yadda lamarin yake a da ba, a halin yanzu manoma za su rinka hurda ne kai tsaye da babban bankin kasa na CBN tare da banki aikin gona “Bank of Agriculture”

“Gwamnati na shirin bayar da tallafin kudade domin kara yawan dankalin turawan da ake noma wa da kayan aikin noma, za a kuma samar da wurin bayar da hayan Tarakta a dukkan kananan hukumomin kasar nan.

“Gwamnati ba zata aiwatar da shirin kai tsaye ba, za mu karfafa wa manoma kafa kungiyoyi tsakaninsu domin bayar da kudaden da kayayyakin noman ta hannunsu”

“Zamu samar da kanfani na musamman domin kula da bayar da hayan Taraktan da kayyakin akin noman rani da sauran abubuwan da zasu taimaka mana wajen cimma burinmu na bunkasa noman dankali turawa gaba daya” inji shi.

Okafor ya kara da cewa, duk lokacin da manomi ke neman wani taimako game aikin noman dankalin turawa, wannan kanfanin ne zai ba shi kai tsaye.

Tuni bankin noma (BOA)  ya raba Naira Bikiyan 262 ga manoma 140,000 a cikin wannan shekarar.

“Cibiyar da zamu samar su zasu kasance tsakanin manoma da masu sayan abin da suka noma, in sun karbi kudaden sai su cire nasu su bamu sauran, zasu kasance tsani tsakanin manoma da masu sayan amfanin gonan don kada a cuci manoma” inji Okafor.

 


Advertisement
Click to comment

labarai