Connect with us

BIDIYO

Bilinbituwar Hukumar Tace Finafinai Ce Ta Sa ’Yan Fim Kai Gwamnati Kotu –MOPPAN

Published

on


Daga Nasir S. Gwangwazo

An bayyana cewa, irin bilinbituwar da hukumar tace finafinai ta jihar Kano ke yi ce ta sanya masu sana’ar shirin fim a jihar su ka yanke shawarar garzawa gaban kuliya manta sabo, domin kare hakkinsu da su ke zargin hukumar na tauye mu su.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin sakataren hadaddiyar kungiyar masu sana’ar shirin fim reshen jihar Kano, Malam Salisu Muhammad, wanda a ka fi sani da Officer a zantawarsa da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta wayar tarho.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 27 ga Fabrairu, 2018 ne dai babbar kotun jihar Kano a karkashin jagorancin Mai shari’a Nasiru Saminu ta bayar da umarnin haramta wa babban sakataren hukumar tace finafinai na jihar, Malam Isma’il Na’abba Afakallah, tauye hakkin wasu ’yan fim ko kama su ko cin zarafinsu har sai kotun ta yanke hukunci ko ta kammala shari’ar da su ka shigar gabanta.

Cikin wadanda a ke karar akwai kuma kwamishinan shari’a kuma antoni janar na jihar da kwamishinan ’yan sanda da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da mataimakin babban sufeton ’yan sanda mai kula da shiyya ta daya da kuma shugaban kwatimin zamanantar da kasuwancin fim din Hausa da hukumar tace finafinai na jihar Kano ta kafa, Alhaji Hamisu Lamido Iyantama.

Ganin yadda hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta yi ta fadi-tashin zuwa gaban rundunar ’yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar a karkashin jagorancin Hon Muhuyi Magaji, amma ba tare da hukumar ta cimma burinta na tabuka komai ba, sai Salisu Officer ya ce, irin wannan bilinbitwar ce ta sanya masu sana’ar shirin fim su ka fahimci cewa tamkar ganin bayan sana’arsu hukumar ke son yi.

Yayin da ya ke karin haske kan dalilansu na garzaya wa kotu, Officer ya bayyana cewa, “abinda ya faru shi ne ita wannan ‘court order’ ta na alamta masalaha. Na farko akwai rashin fahimta daga ita hukumar tace finafinai da mu ke gani kan iyaka hurumta da huruminmu. Akwai rashin fahimta kan kasuwancin masana’antar.

“Mu mu na ganin cewa ba ta da hurumi kan maganar kasuwancin finafinai kan yadda za mu yi da kayanmu da yadda za mu sayar ba. Na biyu, wajen cimma masu satar fasaha, a tunaninmu hukumar Kano ba ta da wani hurumi da za ta ce ga yadda za mu yi mu bibiyi hakkinmu a wajen wadanda su ke yi ma na satar fasaha tunda akwai hukuma ta kasa wacce a ka ajiye ta musamman don ta bibiyi irin wadannan abubuwa na satar fasaha, wato ita ce Copy Right Commission, sannan ga mu mu kuma masu kaya.

“Na uku, a ganinmu hukumar tace finafinai duk a dokokinta babu inda a ka ce ta shigo harkokin kungiya ko mu zo mu yi rijist da su ko ga yadda za mu taka rawa. Mun san cewa hukumar ta na da hakki na tace dukkan finafinan da mu ka shirya, kuma ta na da alhakin yiwa kamfanoni da masu sana’ar rijista, amma banda kungoyoyinmu. Don haka mu ke so kotu ta tsame hannun hukumar tace finafinai ta jihar Kano a cikin harkoki da ayyukan kungiyoyinmu. Wadannan ne abubuwa uku da mu ke kara a kai.”

Ya kara da cewa, “hukumar tace finafinai ta dauki yaranmu ta kai su kara a wajen DSS cewar sun je sun yi kame na wadanda ke tura kayanmu, wato ’yan downloading. Wadannan yara su na karkashin inuwar kungiyarmu ta Film Image mai kular ma na da bangaren hakkin mallaka. Ya kai su a kara a kan sun je sun kama wadancan barayin zaune da su ke satar mu su finafinai su na sayar wa mutane a wayoyi kuma ma su ka iza su su ka je gidan rediyo su ka ce hukumar tace finafinai ta ba su dama su tura duk finafinan da su ke so.

“Mu kuma mu ka ga a kan kayanka, ita hukuma da ba ta da hurumi bai kamata ta zo ta kai kara ba. Mu ka halasci wannan zama da hukumar DSS, wadanda su ka fahimci cewa, abubuwan nan kamar mun fi hukumar tace finafinai gaskiya kuma hakki na mallaka a kan wadannan kayayyaki (finafinai) namu ne, sai su ka salame mu.

“Daga baya sai su ka (hukmar tace finafinai) sake kai kara zuwa rundunar ’yan sanda. Su ma su ka gane cewar, kamar mun fi hukumar tace finafinai hakki a kan abinda su ke kara, sabosa alkali ne ya ci tara ya kuma ci tara. Saboda haka ’yan sanda su ka nuna wa hukumar tace finafinai cewa, duk wani alkali ko ’yan sanda za su iya daukar doka ko da ta hukumar ce ba tare da ta sanar da su ba su yi amfani da su.”

Salisu Officer ya kuma yi bayanin cewa, ita ma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta dan janye jikinta daga batun ne saboda ta fahimci maganar ta na gaban kotu a yanzu.

Bisa zargin da a ke yi na cewa, sabanin Afakallah da Officer ne ya haddasa duk wannan rikicin na son zuciya, sai ya ce, shawarar da zai bai wa Afakallah ita ce, bai kamata saboda wani sabani a tsakaninsu ba ya shiga wahalar da gabadayan ’yan kungiya ba, idan har hakan ya zamo gaskiya.

Officer ya rufe maganarsa ya na mai cewa, “a gaskiya da farko (hukumar tace finafinai) bilinbituwa ta ke yi, saboda ni kusan ma har na yi tunanin kamar ba su da lauya, domin da su na da lauya ba za a je ga wannan zagaye da a ka dinga yi daga SS zuwa poloce da ga police zuwa anticurruption. Da su na da lauya ba za a je ga wannan zagaye-zagaye ba.”

 


Advertisement
Click to comment

labarai