Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane Hudu A Bauchi

Published

on


Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ciki wani sanarwar da suka fitar wa manema labaru a Bauchi sun shaida cewar sun kama wasu ‘yan fashi da makami su hudu, bayan fashi da makami suna kuma yin garkuwa da mutane.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarum wadda Kakakin shalkwatan ‘yan sandan jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya sanya wa hanu kana ya raba mana.

Ya ce “A ranar 6/02/2018 wasu ‘yan bindiga sun yi dirar mikiya wa gidan Dakta Abubakar Gambo da ke Liman Katagum a jihar Bauchi inda suka yi masa fashi da karfin dole na kudi har (N350,000:00)”.

“Bayan nan kuma suka yi garkuwa da shi, inda suka je suka boyeshi a dajin Zungur inda suka killace shi har na tsawon kwanaki uku a wannan dajin, daga bisani ya yi kokarin kubutar da kansa daga garesu,”

Kamal ya shaida cewar bayan nan kuma, wadanda suka kaman sun sake jewa domin yi wani Usman Adamu fashin babur dinsa kirar Boder da wasu da dama da abun ya shafa.

DSP ya ce, samun rahoton lamarin ne kuma ya sanya jami’ansu baza komarsu inda sashinsu na musamman masu yakar fashi da makami da masu garkuwa da mutane wato (FSARS/AKU) suka yi nasarar kamo Idris Haruna 27, Hassan Adamu 30, da Abubakar Jabbo 20, sai kuma na karshensu Salisu Umar aka Babangida 32 a kan wannan zargin.

DSP ya bayyana cewar dukkanin wadanda suka kama sun amince kan laifukansu da bakunansu, wadda ya ce za su kaisu gaban kuliya domin fuskantar shari’a, kan laifukan fashi da makami da kuma kasance masu ta’ada hankuan jama’a hade.

 


Advertisement
Click to comment

labarai