Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yadda Muka Kashe Manajan Gidan Mai A Bauchi’

Published

on


A ranar 14/2/2018 ne rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta baje wa manema labaru wasu jerin miyagun da suka aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka.

Daga cikinsu har da wasu mutane biyar da rundunar ta samu nasar kamewa bisa laifin kashe manajan gidan mai hade da yin fashin a gidan man da ke kan hanyar Jos a cikin garin Bauchi.

Da yake bayyana wa manema labaru yadda suka samu nasarar, Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya bayyana cewar a ranar 16/12/2017 ne wasu ‘yan bindiga dadi wadanda suka haura mutane hudu inda suka kai hari gidan mai na KAMS hade da kashe manajan gidan man domin tangardar da ya nemi kawo musu a lokacin da suke neman yin fashi a gidan man.

Ta bakinsa “’yan bindigan sun kai farmaki ne gidan man KAMS Unibersal Concept Ltd. Da ke hanyar Jos rod a cikin garin Bauchi, inda suka kashe Manajan gidan man mai suna Usman Suleiman mai shekarun haihuwa 35 a duniya,”

Datti ya ce, bayan nan kuma, sun sake nausawa zuwa kauyen Guru da ke cikin garin Bauchi inda suka rike wani matashi mai suna Muhammadu Salisu mai shekaru 25 inda suka taresa hade da yi masa fashin wayoyinsa manya har guda uku da suka ha da kamfanin Tecno T401,

LG Mobile dai kuma wata wayar guda kamfanin Samsung.

Datti, ya shaida wa manema labaru yadda suka yi nasar cewar a sakamakon binciken sirri da kuma kwakwaf da sashinsu na musamman na (SIB) suka gudanar kan wannan batun sun yi nasarar kame wasu mutane biyar ciki har da mace da suke zarginsu da hanu dumu-dumu kan wannan laifin.

Wakilinmu ya labarto cewar wadanda suka shiga hanu kan zargi kisan kai, fashi da makamin su ne Onyeka Dabid wanda aka fi saninsa da suna ‘Swag’ shekarunsa  27, Onyeka Okeke mai shekaru 30 a duniya,  sai kuma Grace Otopa  42 (mace) da Happy Henry 32, sai kuma

Okechukwu Ezissi 42 dukkaninsu kamar yadda ‘yan sandan suka bayyana cewar a Bauchi suke da zama.

Da muke zantawa da wasu daga cikin ‘yan fashin da aka kaman, sun tabbatar da laifinsu hade da kuma bayanin yadda lamarin ya auku daga farko har zuwa su yi nasarar hallaka shugaba gidan man KAMZ da ke Bauchi “Ni sunana Onyeka Dabid tabbas mun yi fashi a wannan gidan man kuma mun kashe Manajan gidan man a lokacin da muka je yin fashin,”

Onyeka ya daura da cewa “Mun kashe manajan gidan man ne don bamu samu kudi ba, ya yi kokarin hana mu kudi ne sai muka kashe shi, daga cikin mu hudun da muka je wannan harin daya daga cikinmu ne ya kashe shi, mun masa dukan tsiya ne har ya mutu”.

Ya ce, bayan fashi suna dan irin hawa mashina suna kwace ababe a hanun mutane, “mukan hau mashin idan muka ganka da abu a hankuna sai mu dan kwace, muna irin wannan dalibar”.

“Ni asalina dan jihar Anambra ne ina aikin Fenti ne a cikin garin Bauchi, matata duk suna can da ‘yan uwana a can garin namu”.

Grace Otopa  daya daga cikin matan da suka yi wannan fashin wanda aka kaman, ta bayyana cewar ita ba ta daga cikin ‘yan fashin kawai sun sanya tane, sai dai kuma Onyeka ya karyata ta, inda ya ce tana cikinsu “da ba ta cikinmu da babu abun da zai sanya na sanyata a cikin maganar, ita aikin da take yi mana shi ne tana zuwa ne ta dudduba yanayin wajen da za mu kai farmaki daga bisani sai mu kuma mu zo”. A cewar Swag.

Baya ga wannan ‘yan fashin, DSP Kamal Datti ya kuma shaida cewar sun yi nasarar kama wasu gangan barayin da suke balle shagona don yin sata wa jama’a “A ranar 05/02/2018 rundunarmu ta samu korafi daga wani mai suna Auwalu Rabiu wanda ke zaune a kauyen Yashi, a karamar hukumar Alkaleri ya kawo mana korafin cewar wani ko wasu wadanda ba a san ko su waye ba sun balle masa shano inda suka sace masa wayoyi da daman gaske a cikin shanon, shagon nasa na wannan adireshin,”

“Dukkanin wayoyin da aka sacen, na mutanen da suka kawo a yi musu caji ne, domin shi wanda ya kawo korafin sanarsa kenan cajin wayoyin mutane,”

Kamal Datti ya bayyana cewar da suka himmatu wajen aiwatar da bincike kan lamarin wanda sashinsu na ‘D–skuad’ sun yi nasarar kamo wasu a unguwar Bayan Gai da ke Bauchi a bisa wannan zargin.

Wadanda suka shiga hanun kan wannan zargin sun hada da  Abubaka Muhammed mazaunin unguwar Nasara Jahun, Bauchi, Yahuza Adamu da ke kauyen Bara a kirfi.

Kamal Datti ya shaida cewar dukkaninsu wadanda suka kaman sun amince da laifukansu.

Ababen da aka kama daga wajen barayin sun hada da wayoyin hanu kala daban-daban guda 35, ababen cajin waya guda 12, abun jin sauti guda biyu, layukan waya guda bakwai, gidajen layukan sim guda hudu, Card Readers guda bakwai, batiri guda 13 da kuma gidajen waya guda hudu.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewar wadannan nasarorin suna daga cikin yunkurin da shugaban ‘yansandan na jihar Bauchi ne CP Sunusi Lemu, sun kuma bayyana cewar za su gurfanar da wadanda suka kaman a gaban kuliya domin fuskantar shari’a daidai da laifukansu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai