Connect with us

LABARAI

Manoman Nijeriya Ne Na Baya Wajen Fitar Da Amfanin Gona A Kasashen Waje

Published

on


Nijeriya ita ce ta baya daga cikin Kasashen Afruka da ke fitar da albarkatun amfanin gona a kasar Ingila wanda hakan yake zaman babban kalubale ga manoma da abin da suke nomawa da kuma ita kanta Gwamnatin Tarayya.

Misis Patricia Obichukwu kwararriya a sha’anin amfanin gona da sarrafa su wadda ke zaune a kasar Ingila ce ta bayyana hakan a yayin da take gabatar da lacca a taron horas da manoma yadda ake sarrafa albakatun gona da kuma fitar da shi a kasashen waje wanda Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta Kasa ta shirya a Sakkwato.

Ta ce kasar Kenya ta na da manoma 1846 da ke fitar da amfanin gona a Ingila a yayin da Ghana da Kamaru suke da manoma 124 da kuma 9 da ke kai kayan gona a Ingila. Burkina Faso suna da 146, Kodebuwa 355, Egypt 671, Afrika ta Kudu 1797 yayin da Nijeriya babu wani manomi ko kamfani da ke fitar da kayan gona a Kasar Ingila. Muna son daga darajar Nijeriya shi ya sa muke gudanar da wannan horon domin magance matsalar da ta dade ta na ci mana tuwo a kwarya.” Ta bayyana.

Ta ce a na samun makuddan kudade idan aka fitar da amfanin gona a kasashen waje amma abin takaici an bar manoman Nijeriya baya sosai wajen fitar da albarkatun gona a waje. Don haka ta ce wannan horon na da manufar kawar da gagarumar matsalar da ake fuskanta.

Patricia ta kuma ilmantar da mahalarta taron hanyoyi da dabaru daban-daban kan yadda za su inganta nomansu tare da sarrafa su yadda ya kamata daidai da bukatun kasuwannin duniya.

Ma’ikatar Ciniki, Masana’antu da Saka Jari ta Tarayya ce ta shiryawa taron na kwanaki uku a otel din Dankani domin horas da manoman Sakkwato yadda za su bunkasa noman dankali, yaji da wake tare da sarrafa su daidai da bukatun kasashen duniya. Ma’aikatar ta shirya taron ne tare da hadin guiwar wata kungiyar da ke hada kasashe da kasuwannin duniya wadda aka fi sani da Global Gap da kuma Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Kasa (FACAN)

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Nijeriya (FACAN) Bictor H. Iyama ya bayyana cewar kungiyarsu na iyakar kokarinta domin ganin sun ilmantar da manoma dokoki da sharuddan fitar da abarkatun gona a kasashen waje. Ya ce idan aka inganta kaya aka sarrafa su yadda ya kamata bayan adana su a muhallin da ya dace to kai tsaye za a iya fitar da su a kasashen waje ba tare da wata tangarda ba.

A jawabinsa Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu na Jihar Sakkwato, Hon. Bello Isa Ambaruru ya bayyana cewar Gwamnatin Jiha za ta ci-gaba da kokari domin ganin ta bunkasa aikin gona a matsayin babbar hanyar samun kudaden shiga.

Ambarura wanda ya bayyana cewar Nijeriya ta na da kasar noma mai kyau, ya kuma bayyana cewar taron yana da matukar muhimmanci kuma an yi shi a daidai lokacin da ya dace musamman a wannan lokaci da Nijeriya ke kokarin bunkasa tattalin arzikin ta.

A jawabinsa Babban Sakataren Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta Tarayya, Edet Sunday Akpan wanda Misis Oluronku ta wakilta ya bayyana cewar ma’aikatar su na kokarin ganin an kara bunkasa ayyukan noma tare da fitar da su a kasuwannin duniya.

Ya ce sun shirya horon ne domin Gwamnatin Tarayya ta na bukatar manoma su rika samun riba mai yawa daga albarkatun noman da za su rika fitarwa a kasuwannin duniya sun kuma fara da Jihar Sakkwato a matakin farko.

Da yake gabatar da jawabi, Dakta Bello Dogon-Daji, Sakataren Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Kasa ya bayyana cewar Jihar Sakkwato ta na da albarkatun noma masu yawa wadanda idan aka inganta su za a samu alheri sosai a kasuwannin duniya. Ya bayyana cewar idan manoma suka bayar da kulawar musamman ga horon da za a ba su za su samu amfani fiye da tsammanin su. Ya kuma bayyana wannan horon a matsayin mataki na farko na magance kawar da matsalar fitar da amfanin gona a wajen kasa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai