Connect with us

LABARAI

IBB Da Saraki Sun Shawarci Hukumar FRSC Da Ta Kara Kaimi

Published

on


A ranar Litinin data gabata ne, tsohon shugaban kasa na mulkin Soja janar Ibrahim Babangida, mai ritaya ya shawarci hukumar kiyeye haduddar ta kasa (FRSC) dasu tashi tsaye wajen tunkarar kalubalen dake kan mayan hanyoyin kasar nan.

Babangida a ya bayar da wannan shawarar ce lokacin da yake jawabin sa a taron bikin cika shekaru takatin ta kafa hukumar da ya gudana a babban birnin tarayyar Abuja.

Ya yi nuni da cewa, alummar kasar nan tana kara karuwa,inda hakan kuma zai kara zama babban nauyi akan hukumar.

Babangida wanda tsohon Ministan wuta da tama   Malam Murtala Aliyu, ya wakilce shi a wurin taron yace yanada yakinin cewar, hukumar zata magance kalubalen dake gabanta, inda ya buga misali da nasarorin da hukumar ta samu tun lokacin da aka kafata a shekarun baya.

Shi ma a nashi jawabin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki wanda Sanatan APC mai wakiltar Zamfara ta Arewa Tijani Kaura ya wakilce shi ya taya hukumar murna akan nasarorin data samu a cikin shekaru talatin da suka wuce.

Saraki yace, kara fadada ayyukan hukumar da kuma kara yawan ma’aikatanta, da kuma rungumar fasaha, ya zama abin koyi ga sauran hukumomin gwamnati.

Ya kuma tunatar da hukumar akan kalubalen dake a gabanta, inda kuma ya yiwa mahukuntan hukumar alkawarin  samun goyon bayan Majalisar kasa.

Shi ma Ministan babban birnin tarayya Malam Mohammed Bello, wanda jami’I a ma’aitar Mista Christian Oha,ya wakilce shi a wurin taron yace, barnin tarayyar ya amfana da ayyukan hukumar sosai.

Bello yaci gaba da cewa, ayyukan da hukumar take yi sun taimaka wajen yadda ake yin tuki a Abuja.

Sai dai ministan ya yi nuni da cewa, akwai jan aiki a gaban hukumar wajen magance yawan yin gudu da abin hawa da wasu masu abin hawa ke yi da kuma rashin bin ka’idojin yin tuki a birnin tarayyar.

Ministan ya kara da cewa, mahukuntan birnin tarayyar, zata ci gaba da dangantar dake tsakanin ta da hukumar don magance kalubalen yin tuki a babban birnin tarayyar.

A nashi jawanbin, shugaban taron kuma tsohon Shugaban Ma’aikata na Tarayya Alhaji Yayale Ahmed yace, hukumar ta kasance wadda ake girmamawa sosai a kasar nan saboda bin ka’idojin da suka kafata.

A cewar Yayale,“ ya kamata mu jinjinawa hukumar akan gudanar da ayyukanta tukuru, a bisa wannan kuma ya kamata su sanar da kawunan mu cewar kare hanyoyin mu daga hadari abune da ya rataya akan kowa.’’

Shi ma mai masaukin baki kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Boss Mustapha,ya jaddada aniyar gwmanatin tarayya  wajen kara hukumar karfi don ta kara samun sukunin gudanar da ayyukanta.

Mustapha,wanda ofishin sa ne ke sanya ido akan ayyukan hukumar yace, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki akan kada su gajiya wajen gangamin fadar da kan ‘yan kasa akan kiyayen titunan dake kasar nan daga aukuwar ha durra.

Shi kuwa jami’I mai ilimantar da alummar gari  na hukumar Mista Bisi Kazeem, yace kimanin kashi tsa’in bisa dari na fasinjoji da kayan da ake daukowa a motoci, suna kara zama dauyi ga hukumar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai