Connect with us

LABARAI

Ba Wanda Ya Isa Ya Hana Ni Zama Shugaban Nijeriya –Sule Lamido

Published

on


Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma daya daga cikin masu neman Jam’iyyar PDP ta tsayar da su neman Shugabancin Kasarnan, Sule Lamido, ya ce, ba wanda ya isa ya hana shi zama Shugaban kasarnan a zabe mai zuwa.

Lamido, ya yi wannan furucin ne a wajen wani taro na bude Ofishin kamfen din shi na neman Shugabancin kasa a Birnin Kudu, ta Jihar Jigawa. Idan har nufin Allah ne, ba wanda zai iya hana ni  kasancewa Shugaban kasan nan.

Ya kuma bayyana cewa, shakka ba bu, za a fafata neman Shugabancin kasar nan ne a shekarar 2019, a tsakanin wadansu mutane biyu, duk cikansu Musulmai, Fulani, tsaffin gwamnoni sannan kuma tsaffin Ministoci a kasar nan a lokuta daban-daban.

“Kai ba bu fa wani dan adam a doron duniyar nan, wanda ya isa ya hana nufin Allah, idan har Allah Ya nufa ni ne zan kasance Shugaban wannan kasar, ko ta hanyar Kotu, ko ta wace hanya, ba wanda ya isa ya hana ni.

“Bambancin da ke Tsakani na da Buhari shi ne, duk da ya taba zama gwamna a karkashin mulkin Soja, amma dai bai yi wa mutane aiki ba. Ya kuma yi Ministan Man Fetur, wanda mutane da yawa ma ba su san hakan ba. Alhalin ni, a lokacin da na yi Ministan harkokin waje, duk duniyan nan kowa ya sanni, sannan kuma, ayyukan da na yi a shekaru takwas na zama na a kujerar gwamna, sun isa shaida a gare ni.

Sule Lamido, ya kara da cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, Bafillatani ne kadai da sunan an haife shi Bafillatani, daganan, sai ya kalubalanci Shugaba Buhari da ya fassara masa wasu ‘yan kalamai da ya yi zuwa Fullanci a wajen taron.

“Buhari da Jam’iyyar sa ta APC, ba karyar da ba su shararawa al’ummar Nijeriya ba a lokacin zaben 2015, to yanzun mutane sun san gaskiyar lamurra, za kuma su ba su amsa a zaben 2019,” duk in ji Sule Lamido.

 


Advertisement
Click to comment

labarai