Connect with us

LABARAI

An Gwabza Tsakanin Gwarawa Da ’Yan Sanda A Neja

Published

on


Sakamakon arangama da wasu gwarawa manoma da jami’an tsaron ‘yan sanda ya jawo hasarar rayukan mutane a yankin Lapai, kamar yadda majiya mai tushe ta shaida lamarin ya faru da wani direba dan kabilar gwari da ya dauko tawagar amarya daga yankin Kuta inda ya doshi ruggar mugu da ke cikin karamar hukumar Lapai.

Majiyar ta ce jami’an ‘yan sandan sun tare direban da nufin karban na goro wanda yaki ba su goyon bayan da ya kai ga jami’an ‘yan sandan sun kai ga dokansa, wanda yasa jama’ar ke kan hanyar suka nuna rashin jin dadinsu. Martanin da jama’ar suka mayar ya hasala jami’an ‘yan sanda suka kai ga yin harbin da ya janyo rasa ran mutum daya nan ta ke, hakan yasa jama’ar ruggar mugu shigowa garin Lapai dan yin zanga-zangar lumana da kin amincewa da abinda jami’an ‘yan sanda ke yi na cin zarafin direbobi akan kin bada na goro, inda aka yi rashin sa’ar da jami’an ‘yan sandan suka sa ke yin harbin da halaka mutun daya nan ta ke da barin wasu mutane biyu magashiyan wanda dayan na asibitin kwararru na IBB da ke minna ya yin da dayan kuma na asibitin samunaka da ke garin Lapai.

Yanzu haka dai lamarin ya lafa inda ‘yan sanda ke rike da mutum daya a ofishinsu dake Lapai.

A ziyarar jaje da ta’aziyyar da mataimakin gwamnan Neja, Alhaji Ahmed Muhammed Ketso ya kai ya jawo hankalin jama’a akan daukar doka a hannu wanda ya ce wannan ba daidai ba ne. Mataimakin gwamnan wanda ya samu rakiyar mai martaba sarkin Lapai, Alhaji Umar Tafida Bahago da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Neja.

Ya bada tabbacin gwamnati ba za ta zura ido irin haka na cigaba da faruwa ba, yace ‘yan sanda abokan kowa ne bai kamata jama’a su ja gaba da ‘yan sanda ba, a duk lokacin da rashin fahimta ya shigo bai kamata bangarorin biyu suna rufe ido suna abubuwan da ba su da ce ba. Don haka gwamnati za ta tabbatar tayi bincike na adalci kuma duk wanda aka samu da laifi lallai za a hukunta shi kamar yadda doka ta tsara.

Tawagar ta mai girma mataimakin gwamnan ta baiwa Iyalan mamatan sadakar naira dubu dari, tare da alkawalin daukar nauyin wadanda aka raunata sakamakon wannan rashin fahimtar da ta taso.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ya ziyarci mutanen ruggan mugu, wakilin gwari-nupe, Alhaji Muhammadu Awaisu Giwa, ya ce, gwarawa mazauna kasar Nupe mutane ne masu son zaman lafiya, ya cigaba da cewar wannan lamari bai yi dadi ba da ya kai ga rasa rayuka. A cewarsa ya kamata jami’an tsaro su kawo karshen irin wannan cin kashin kajin da ake yiwa kabilar gwari a jihar nan.

“Irin wannan ya faru tsakanin sojoji da gwarawa wanda abin bai yi kyau ba, kuma yanzu somin tabinsa na son maimaita kansa a nan yankin Lapai, ya kamata jami’an tsaro su sani an kafa su ne dan baiwa jama’a da kasar nan tsaro, bai kamata jami’in tsaro ya rika barazana ga ‘yan kasa na kwarai ba, yin hakan babban kuskure ne.” inji shi

Wakilin ya ce da lamarin ya faru ya ziyarci ofishin ‘yan sanda na Lapai, inda aka nuna mashi wasu jarkunan man fetur da aka ce wai mutanen sun zo da nufin kona ofishin, yace akwai rahoton da ya nuna jami’in dan sanda guda ya rasa ransa akan wannan sabani ga motar faturol ta ‘yan sanda da aka kona, yace wannan koma baya ne, ya kamata manyan jami’an ‘yan sanda su rika lurar da kananan ma’aikatansu illa anfani da karfi wajen neman biyan bukata.

Wakilin ya jawo hankalin gwamnatin Neja da kungiyoyin kare hakkin jama’a akan su tabbatar sun yi bincike na gaskiya wajen walwale wannan sabani. “Bai kamata abinda ake yiwa gwarawa ya cigaba ba, ba a san bagware da fitina ba, ya kamata gwamnatocin siyasa da jami’an tsaro da su kara kaimi wajen kare rayuwar al’umma, domin irin wannan ba zai haifar da da mai ido ba a kasar nan ba.

“Gaskiya ba a mutunta rayuwar gwarawa, mu kuma rashin ran bagware daya tak babban rashi ne a wajen mu, zamu kara kaimi wajen wayar da kan mutanen mu akan illar daukar doka a hannu domin hakan ya kan haifar da da marar ido, ta bangaren jami’an tsaro kuwa da su ji tsoron Allah su sani sun yi alkawali na kare rayuka da dukiyar ‘yan kasa, saba ma hakan na iya zubar kimarsu a idon jama’a.

“Maganar bincike kuwa ina baiwa bangare gwamnati da jami’an tsaro shawarar da su yi aiki tsakaninsu da Allah, idan ma sun boye gaskiya akwai ranar gaskiyar za ta fito kuma ba su da wani shamaki. A madadin al’ummar gwarawa mazauna kasar Nupe mun yabawa maigirma gwamna wanda mataimakinsa ya wakilce shi, haka muna kara biyayya ga mai martaba sarkin Lapai akan hadin kai da goyon bayan da yake baiwa kabilar gwari mazauna yankin nan. Ta bangare jami’an tsaro kuwa yace suna kokari amma duk da hakan akwai masu son anfani da matsayinsu wajen bata su a idon mutane.” inji shi


Advertisement
Click to comment

labarai