Connect with us

LABARAI

Dakatar Da el-Rufai: Rikicin APC Na Kara Zafi A Kaduna

Published

on


Bangaren Jam’iyyar APC dake goyon bayan Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa, Alhaji Sulaiman Usman Hunkuyi, ya dakatar da gwamnan Jihar ta Kaduna, Nasir el-Rufai, daga cikin Jam’iyyar har na tsawon watanni shida.

Wannan dakatarwar da aka yi wa gwamna El-Rufai, ta zo ne a daidai kwanaki uku kacal da wani bangaren Jam’iyyar wanda ya kira kansa da, ‘Kaduna Restoration Group,’ shi ma ya baiwa gwamnan tuhuma ya kuma dakatar da wasu na tare da gwamnan uku daga cikin Jam’iyyar.

Wannan bangaren Jam’iyyar na APC, wanda ke karkashin jagorancin Sanata Hunkuyi, ya zargi gwamna El-Rufai ne da aikata wasu ayyukan da suke kishiyantar Jam’iyyar ta APC, da kuma aikata wasu ayyukan da suke cin zarafi ne ga bil adama.

Bangaren na Sanata Hunkuyi, ya gargadi gwamna El-Rufai, da cewa matukar bai amsa tuhumar da aka yi masa ba a cikin awanni 48, “to kuwa tabbas kwamitin amintattun Jam’iyyar zai zauna ya kuma yi hukuncin da ya dace a kansa.”

Sai dai kuma a wani rahoton da wannan bangaren ya fitar a ranar Lahadi, ya zargi gwamnan har ilayau, da laifin kin amsa kiran da kwamitin amintattun ya yi masa na ya zo ya kare kansa a kan tuhume-tuhumen da aka yi masa.

A kan haka sai wannan bangaren nan take ya yanke shawarar dakatar da shi daga Jam’iyyar har na tsawon watanni shida.

Rahoton kwamitin amintattun ya yi bayani kamar haka, “A bisa gazawarsa da karewar wa’adin awanni 48 da kwamitin amintattun wannan Jam’iyya ya baiwa gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad Elrufai, a kan ya zo ya bayar da wasu bayanai domin kare kansa daga tuhumomin da ake yi masa, wannan kwamiti wanda ke karkashin shugabancin, S.I.

“Danladi Wada, a wannan rana ta Asabar 17 ga watan Fabrairu 2018, ya taru sannan kuma ya duba shawarar da kwamitin ladabtarwar Jam’iyya ya bayar, kamar yadda doka ta 21 (B) ta tsarin mulkin Jam’iyyar APC, ta tanadar. A bisa gazawarsa na amsa kiran da da aka yi masa, wannan Jam’iyya ta dakatar da shi na tsawon watanni shida nan take daga duk wasu harkoki na Jam’iyyar APC.


Advertisement
Click to comment

labarai