Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Sun Ceto Makiyaya Da Shanu 200 A Jihar Borno

Published

on


Rundunar yan-sandan Nijeriya dake a jihar Borno ta bayyana cewa ta kubutar da makiyaya tare da shanu sama da 200 daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram a yankin karamar hukumar Nganzai dake jihar.

Kwamishinan rundunar yan-sanda a jihar Borno, Mista Damian Chukwu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri, bayan tattàunawar karshen wata da jami’an sa, a ranar litinin.

Bugu da kari kuma, Chukwu ya shaidar da cewa an ceto makiyayan ne ranar biyu ga wannan wata na Fabarairu, ta wani samamen hadin gwiwa a tsakanin yan-sandan da yan sa-kai na kato-da-gora (CJTF) a surkukin duhuwar Galte dake yankin karamar hukumar.

Haka kuma ya yi karin haske da cewa sun aiwatar da samamen bin-sakun biyo bayan wani rahoton da suka samu bisa ga yadda mayakan kungiyar sun yi garkuwa da wasu makiyayan tare da neman a basu kudin fansa, kafin su sako su.

“wanda babban jami’in yan-sanda na yanki (DPO) dake yankin ya jagoranci samamen tare da samun nasara bayan bata-kashi da musayar wuta da ya wakana a tsakanin su da mayakan kungiyar Boko Haram “.

“yan-sandan sun ceto makiyayan tare da wannan adadi na dabbobin su, a lokacin da mayakan kungiyar suka arce. Yayin da kuma yan-sandan sun sami bindiga mai sarrafa kan ta (GPMG) tare da albarusai wadanda mayakan suka gudu suka bari”. Inji shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai