Connect with us

TATTAUNAWA

Sai Iyaye Sun Canza Ne Za A Iya Kawo Karshen Fyade –Barista Aisha

Published

on


Za a iya cewar matsalar fyade ga kananan yara matsalar tan a gab da zama gagara-badau ga al’umma da kuma mahukumta, domin a duk rana sai ka ji matsalar sai karuwa ta ke yi tamkar wutar daji, wannan ne ke sa zargi ya yi yawa ga ma su rike da madafun iko cewar su ke da alhakin kawo karshen matsalar fyade, amma sai aka sami akasin haka. 

BARISTA AISHA AHMAD, lauya ce mai zaman kanta a Zariya, ita ta ce, duk matakan da gwamnati za ta dauka sai iyayen yara da kuma al’umma sun canza, san nan matsalar fyade za ta zama tarihi. Bayanin da ta bayyana wa wakilinmu BALARABE ABDULLAHI ke nan, a zantawar da suka a ofishinta da ke Zariya. Ga yadda tattaunawar ta kasance.

Ya ki ka dubi yadda matsalar fyade ke yawaita, tamkar wutar-daji a yau?

Duk bayanan da zan yi ma ka, ina fatan ba za ka ce a matsayi na mace, na so kai na ba, ni a nawa tunanin duk mai aikata fyade ga kananan yara, ya na yi ne domin son ransa, saboda haka son ran da na fadi, shi ne kan gaba ga dalilan da bata-gari ke furtawa bayan sun aikata fyaden, kuma

zalunci ne yi wa kananan yara fyade, ba zan gushe da fadin haka ba a tsawon rayuwa ta.

Kuma, in ba zalunci ba, tun da akwai mata wadanda ba sa kishin rayuwarsu, su jiran maza su ke yi a ko wane lokaci, me zai sa mai son yin fyaden ba zai je ga wadancan matan ba? A gaskiya, duk wani na-miji da ya ke aikata fyade, ba shi da dalilin da zai fadi da mutane nagari za su yadda da shi.

Wannan matsala ta fyade, babban laifi ne, ko kuma karamin laifi?

Ai in har ka furta fyade, a shari’ance ya kasu kasha biyu, wato akwai fyade da ake yin a kananan yara sai fyade da ake yi wa balagaggun mata. Kuma duk fyade biyun nan da na fada ma ka dukkaninsu manyan laifi ne, wannan laifi, dai-dai ya ke da kisan kai da fashi da makamai.

Wani abu da na ke son ka fahimta shi ne duk wanda aka yi wa ‘yarsa fyade, babu yadda za a yi ya ce ya yafe, kuma duk wadannan tanade-tanade, suna cikin addinin musulunci da kuma tsarin mulkin Nijeriya. Ka ga in mace bat a kai shekara goma sha shida ba, in har aka yi amfani da karfi ko kuma da yaddarta, na miji ya sadu da ita ya aikata laifi, kuma babban laifi, kamar yadda na bayyana ma ka a baya.

Amma a mace babba, akwai wasu abubuwa da ake dubawa, sai an tabbatar da furucinta, sai an duba, wato a wani yanayi aka yi ma ta fyaden? Inda aka yi ma ta fyaden akwai mutane? Shin za ta iya ihu a lokacin da za a yi ma ta fyaden ko bayan an yi ma ta fyaden? Shin ta yi dambe da wanda ya yi ma ta fyaden? Ta kare kanta? Kuma dai sai na miji ya sanya zakarinsa a farjinta, daga nan ne laifi zai iya tabbata, in an ce an yi wa babbar mace fyade. Kuma tabbatar da wadannan abubuwa, musamman na karshe, likita ne zai tabbatar, ta binciken da zai gudanar, sai an sami wannan sakamakon bincike daga likta, daga nan za a tabbatar da laifi ga wanda ya aikata fyaden. Amma in babbar mace ta ce an yi ma ta fyade, sai an tabbatar da abubuwan da aka bayyana. Kaza-lika, likita ne zai je kotu, ya bayyana yadda ya gano abubuwan day a bayyana wa kotu.

To, wasu abubuwa ake dubawa a tabbatar da fyade ga kananan yara?

To, yarinya karama dab a ta kai shekara goma sha shida ba, ba a duba abubuwan da ake tabbatar da fyade day a shafi kananan yara, kotu za ta yi ‘yan tambayoyi ga karamar yarinyar da aka yi ma ta fyade, kamar a ce ma ta, menene hukumcin wanda ya yi karya, sai ka ji yarinyar ta ce za a sa shi a wuta, da dai sauran tambayoyi da kotu za ta fahimci yarinyar da aka yi wa fyade tan a da hankali ko a’a?Da zarar an yi wa yarinya fyade, a gaggauta kai ta asibiti, rahoton likita, shi ne hujja mai karfi, da kotu za ta dogara da shi. ta yanke hukumci ga wanda ake zargin ya aikata laifi.

Idan laifi ya tabbata, ya batun da hukumci?

Ai hukumcin a bayyane yak e a tsarin mulkin Nijeriya, wato akwai daurin rai-da-rai da za a yi wa wanda ya aikata laifin, kuma in a musulunci ne akwai tanadin dokar da babu sassauci.

A na zarginku lauyoyi da Alkalai da sakin wadanda aka samu da aikata fyade, kin yadda da zargin da ake yi ma ku?

In ka tuna a baya, na bayyana ma ka bukatun bangaren da kotu za ta yarda su ta yanke hukumci, in kuma ba a tabbatar da laifin da ake zargi ba, dole a duba abin da dokar kasa ta tanada a kansa na zargin da ake yi ma san a aikata laifin fyade. Kuma ko da an sami mutum

turmi-da-tabarya ya na aikata laifin, sai kuma an duba abin da hukumci ya tanada, ka ga in an saki wanda ake zargi dai-dai ne, domin ba a same shi da aikta zargin da ake yi ma sa ban a aikata fyade.

Ya ki ka dubi iyayen yara a batun fyade a yau?

Ai a nan matsalolin suke, domin za ka an sami wanda ya lalata yarinya ta yi ma ta fyade, an fara nisa a cikin bincike, ana kuma ganin alamun nasara, sai a wayi gari iyayen yara su ce sun janye karar da suka yi, ko kuma a fara halartar kotu, sai ka ga iyayen yaran da aka yi ma su fyaden sun dai na zuwa kotu, to sai Alkali ya duba mai shari’a ta tanada ga wanda ake zargi, sai ta yanke hukumci. Sai ma su ce in an ce za a ci gaba da yin shari’ar, sai ka ji iyaye na cewar, su sun janye, wai ka da a bata sunan ‘yarsu a nan gaba.

Dagan an sai wanda ke tsare ya nemi lauya, domin ya karbe shi, ko kuma ya fitar da shi daga gidan yari da aka garkame shi, sai lauya ya je kotu ya kare shi, a karshe, sai ka ga an saki wanda ake zargi. A gaskiya, in har ana son kawo karshen fyade, to sai fa iyaye sun canza halin da na bayyana ma ka suna yi, na juya bayansu da taimaka wa kotu da lauyoyi, na ganin an hukumta wanda aka kama da zargin yin fyade. Ina tabbatar ma ka da cewar, babu Alkali ko kuma`lauya nagari da zai amince a bar mai yin fyade ya tafi sasa-kai ba.

To rashin hukumci ne ko kuma ko in kula daga iyaye ke sanya taki ga matsalar fyade a yau?

Duk biyun suna da muhimmanci, sai fa iyaye sun da goyon baya ga bangarorin jami’an tsaro da bangaren shari’a za su sami dammar yin hukumci ga wanda ake zargi da aikata fyaden. Kuma da iyaye na bayar da dammar binciken wanda ake zargi, aka tura wanda aka samu da aikata laifin fyade, zuwa gidan yari da zai shafe sauran shekarunsa, to ba za a sami ma su aikata fyade ba a nan gaba.

Yau an wayi gari, ana aikata laifin ba a yin hukumci, kuma mafi yawan laifin na iyaye ne kamar yadda na fadi a baya, ba za iya kawo karshen wannan matsala ba, domin sai iyaye da jami’an tsaro da kuma Alkalai sun sami goyon bayan yin aiki daga iyaye, za a sami mafitar wannan matsala ta fyade.

karshe, Barista Aisha Ahmad, wani sako kike da shi ga iyaye?

Ai sakon daya ne, kamar yadda na bayyana a baya-bayan nan, dole iyaye su canza halin da ke da shi, na su suke kai kara, amma daga baya sai su janye jikinsu, in sun canza, kamar yadda n ace, matsalar fyade za ta kau baki daya a cikin al’umma.


Advertisement
Click to comment

labarai