Connect with us

KASASHEN WAJE

Rouhani Ya Fara Ziyarar Aiki A Kasar India

Published

on


Shugaban Iran Hassan Rohani ya fara ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku a India domin habaka kasuwanci da kuma musayar fasaha a bangaren makamashi tsakanin kasashen biyu.

Ziyarar shugaban ta farko zuwa India tun bayan hawansa mulki za ta dauke shi tsawon kwanaki 3 ta yadda za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi huldar kasuwancin da ke tsakaninsu kafin komawarsa gida a ranar Alhamis din makon nan.

Akwai dai kyakkyawar alaka a tsakanin kasashen biyu, tun daga lokacin da Firaministan India Nerendra Modi ya ziyarci Iran a shekara ta 2016, inda shugabannin biyu suka kaddamar da gina wata tashar jiragen ruwa a Chabahar kudu maso gabashin Iran.

Haka kuma India na daga cikin jerin manyan kasashe uku da ke ci gaba da sayen man fetur din Iran ko a lokacin da takunkuman Amurka ke tsaka da aiki  a kan Iran.

A lokuta da dama dai kasashen biyu kawayen juna kan tsoma baki kan al’amuran cikin gidan junansu kamar yadda ya faru a bara Inda jagoran addinin Iran.


Advertisement
Click to comment

labarai