Connect with us

SIYASA

Ni Ba Dan Amshin Shatan Majalisa Bane –Shehu Sani

Published

on


Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewar shi baije Majalisa domin zama dan amshin Shata ga kowa ba, shi zababben ne wanda jama’a suka zaba ba nadadde ba, saboda haka aikin shi a majalisa shi ne kare muradun jama’ar da suka zabe shi, da kin amincewa da dukkanin wani abu daya wanda yaci karo da ci gaban kasa.

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne, lokacin da yake mayar da martani dangane da kiran da wasu kungiya mai suna Kaduna Concern Farum, suka yi, karkashin shugaban kungiyar mai suna Aliyu Sa’idu Rigachikun, inda suka bayyana aniyar yi wa Sanatan kiranye, bisa ga zargin kasa aikin da aka tura shi yi a Majalisa, maimakon haka sai ya dawo yana adawa da sukan Gwamnatin Buhari da na El-rufa’i, a yayin wani taron manema labarai da ya kira a cibiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen Jihar Kaduna.

Sanata Shehu Sani wanda ya bayyana hakan ta bakin Mai taimaka masa na musamman akan harkokin hulda da jama’a, Malam Sulaiman Muhammad, ya zargi Gwamnatin El- rufa’i, da daukar nauyin wadannan mutane masu ikirarin yi mishi kiranye, inda yace ba sabon abu bane ga Jama’ar Jihar Kaduna dama Nijeriya baki daya. A cewarsa, El-fufa’i, yasha dauko hayar mutane daga wasu wurare su tara ‘Yan jaridu suna surutu a kanshi, anyi haka yafi so shurin masaki, kuma aniyar El-rufa’i, da mukarraban shi ita ce batanci a gareshi, amma su jama’ar da ya ke wakilta a mazabar Kaduna ta tsakiya mai Kananan Hukumomi 7, sune Alkalai a tsakanin shi da El-rufa’i, kuma sune suke da hakkii na cewar za suyi kiranye amma ba a dauko wasu mutane daga waje ba.

Sanata Shehu Sani, yace, “ jama’ar Kaduna ta tsakiya mutane ne wayayyu wadanda suka san abin da suke yi, ba mutane bane wadanda za’a ari bakin su aci musu albasa, a tsawon zaman da nayi a Majalisar kimanin shekaru biyu da rabi, ‘Yan Kaduna ta tsakiya sun san ayyukan da nayi musu, kuma tabbas ina tare da jama’a ta, saboda haka a daina yiwa ‘Yan Kaduna ta tsakiya katsalandan a barsu suyi hukunci akan ci gaban su, ba’a dauko hayar wasu daga waje suyi magana da yawun su ba.”

Dangane da zargin cewa Sanatan na sukar Gwamnatin Buhari, sakamakon kalaman da ya yi na cewar Buhari ya huta a 2019 ya dora wani, Dan Majalisar Dattawan yace ko kadan ba sukan Gwamnatin Buhari yake yi ba, sai dai ya yi la’akari da halin da kasa take ciki ne, biyo bayan tsadar rayuwa da jama’a suke ciki, da yawaitar kashe – kashe tsakanin Manoma da Makiyaya, da yin garkuwa da Mutane da fashi da Makami, wannan shi ne dalilinsa, domin Buhari na kokari amma wasu mukarrabansa na cin dunduniyarsa, shi ya sanya ya bayyana ra’ayin shi da kiran Buhari ya huta ya dora wani Amintaccensa domin ci gaban Nijeriya da Jama’arta baki daya. A cewar Sanata Shehu Sani.


Advertisement
Click to comment

labarai