Connect with us

MANYAN LABARAI

Mummunan Hatsarin Mota Ya Ci Daliban Bauchi 25

Published

on


 A jiya ne mutum 29 wadanda suka hada da dalibai 25 da malaman su uku da direba sun rasa rayukan su a kan hanyar su ta zuwa nazarin ilimin tarihi a gidan dan Hausa da ke Kano.

Dalibai da Malaman da suka rasu sun kasance a karkashin kungiyar Hausa Fasaha dake makarantar Jeka ka dawo ta GDSS Misau da ke Jihar Bauchi.

Hatsarin ya auku a kusa da garin Gaya dake Jihar Kano da misalin karfe Goma na Safiyar jiya inda motar kirar ‘Toyota Hommer’ wacce aka cunkushe ta da daliban ta yi taho mu gama da mota kirar tirela mai tayu goma sha biyu, wacce ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, inda su kuma ke kan hanyar su daga Misau zuwa Azare zuwa Kano don gudanar da wannan nazarin tarihi.

LEADERSHIP A Yau ta gano cewa daliban sun kasance ‘yan ajin karamar sakandare daga daya zuwa uku wadanda suka kudiri yin wannan tafiya tare da malamansu sun gamu da hatsarin ne a dalilin aikin hanya da ake yi a wannan waje aka kuma hade ana tafiya  kan hannu guda. Lamarin dai ya yi muni sosai har sai da matafiya da mutanen yankin suka yi ta taimakawa kafin aka jawo gawarwakin dalibai 22 da malamai uku da direba yayin da kuma dalibai uku aka kai su asibiti

kafin daga baya suma rai ya yi halin sa.

Ya zuwa wannan lokaci lamurra sun tsaya cik a fannin aikin gwamnati a Jihar ta Bauchi kamar yadda babban mai ba gwamnan Jihar Bauchi shawara kan harkar ilmi Kwamared Sabo Mohammed ya shaida wa wakilin mu. Inda ya mika sakon gaisuwar ta’aziyya a madadin kwamishinan ilimi na Jihar Bauchi da daukacin masu ruwa da tsaki kan ilmi da kuma gaisuwar ta’aziyya ta gwamna Mohammed Abdullahi Abubkar na Jihar Bauchi game da wannan rashi na daliban inda ya bayyana cewa wannan babbar hasarace ga Jihar da ba za a taba mancewa da ita ba kan harkar da ta shafi ilmi.

Sabo Mohammed ya kara mika ta’aziyyar gwamnati da jama’ar Jihar Bauchi ga Mai martaba Sarkin Misau Alhaji Ahmed Sulaiman game da wannan babban rashi na yara masu kasancewa manyan gobe a Jihar Bauchi.

Ya ce gwmnati ta kadu sosai lokacin da ta samu wannan labari, kuma nan take jami’an ma’aikatar ilmi da sauran jami’an gwamnati suka dunguma zuwa garin na Misau domin yin jana’izar yaran wacce ta gudana a yammacin wannan talatar a garin na Misau.

Malam Ya’u Mohammed da Malam Mohammed Kaka Misau Malamai ne a wannan makaranta, sun bayyanawa LEADERSHIP A Yau alhininsu kan wannan rashi da suka ce ya haifar da gibi a fannin ilmi na makarantar ta jeka ka dawo da ke garin Misau, inda suka yi fatar Allah ya ba da hakuri ga iyayen yaran da kuma abokan karatun su da malaman wannan makaranta da sauran ‘yan uwa da dukkan jama’ar wannan kasa, inda suka ce wannan babban rashi ne da ba za su iya mance wa  da shi ba a tarihin karatun wannan makaranta.

Jagoran ayyukan musamman na hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC da ke Bauchi Kwamanda Paul E. Guar a lokacin da wakilin mu ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Bauchi, ya tabbatar da aukuwar wannan hatsari, inda ya ce daliban sun tashi daga garin Misau zuwa Kano sun gamu da ajalin su a kusa da garin Gaya sakamakon taho mu gama da babbar mota, inda ya bayyana cewa yin sakaci da dokar tuki ya temaka wajen haifar da hatsarin. Don haka ya roki jama’a su kasance masu lura da rayukan jama’ar da suke dauka da kuma nasu shi ne zai taimaka a samu raguwar hadurra a kasar nan.

Haka kuma Paul Guar ya bayyana takaici game da yadda aka cunkusa wadannan mutane har kusan 30 a motar da ke daukar mutane 18, lamarin da ya bayyana a matsayin abu maras kyau da kuma saba dokar tuki da lodi, saboda yin hakan na samar da karuwar yawan mutanen da za su iya galabaita ko rasa rayukan su a duk lokacin da wani tsautsayi ya abko kan matafiya, musamman ganin cewa wannan hatsari ya auku ne a wurin da ake gyaran hanya.  Daga karshe ya ce ofishin hukumar da ke Jihohin Kano da Jigawa sune za su bayar da cikakken bayani game da yadda aikin su ya gudana a wajen wannan hatsari.

 


Advertisement
Click to comment

labarai