Connect with us

MANYAN LABARAI

Jacob Zuma Ya Yi Murabus

Published

on


Shugaban kasar Afirka ta kudu, Mista Jacob Zuma ya yi murabus daga mukamin shi na shugabancin kasar, shi dai Jacob Zuma ya yi shekaru tara yana shugabancin kasar Afirka ta kudu.

Murabus din ya biyo bayan matsin lamba daga ‘yan jam’iyyar sa ta ANC, bisa zargin cin hanci da rashawa da sauran zarge-zarge, Mista Zuma ya na daga cikin jama’ar gwarzon dan kishin kasa na Afirka ta kudu wato Nelson Mandela.

Cyril Ramaphosa ne ya maye gurbin shi a matsayin shugaban jami’iyyar ANC mai mulki, Mista Ramaphosa shine mataimakin Zuma, don haka shine zai maye gurbin Zuma a shugabancin kasar Afrika ta kudu da ma jam’iyyar ANC.


Advertisement
Click to comment

labarai