Connect with us

LABARAI

Gwaman Bauchi Ya Rushe Dukkanin Shuwagabanin Gudanarwa Na Kwalejin Aikin Gona

Published

on


Gwamnan Bauchi Muhammad Abdullah Abubakar ya sanar da rushe dukkanin shuwagabanin gudanarwa na kwalejin ilimin nazarin albarkatun kasa ‘gona’ ta jihar Bauchi ba tare da bata wani lokaci ba.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin Bauchi dauke da sanya hanun Sakataren gwamnatin Bauchi, Alhaji Muhammad Nadada Umaru wadda wakilinmu ta yi tozali da kwafin takardar a Litinin din nan.

Gwamnan ta cikin sanarwarsu ya bayyana cewar wannan dakatarwar nan take zai fara aiki ba tare da jiran-jira ba, haka kuma gwamnan jihar ya amince da nadin kwamitin riko na kwalejin aikin gona domin ci gaba da tafiyar da harkokin kwalejin yadda ya dace.

Kwamitin da gwamna ya nada a matsayin na riko su ne Farfesa Muhammad D. Abubakar a matsayin shugaban kwalejin na riko, Abubakar Gabi kuma ya kasance shugaba mai kula da sha’anin kudi, Dakta Ali Hussaini kuma ya kasance a matsayin magatakarda kwalejin na wucin gadi.

Sanarwar gidan gwamnatin ta bayyana cewar wannan rushewa da kuma kafa hukumar gudanarwa na kikon nan take zai fara aiki ba tare da bata wani lokaci ba.

Idan dai baku mance ba; wannan jaridan mun sha kawo muku rahotonni kan hatsaniyar da ke cikin wannan kwalejin, inda kungiyar ASUP na kwalejin suka yi ta shelanta matsaloli da suke zargin shuwagabanin gudanarwa da aikatawa ciki kuwa har da batun bayar da takardar kammala kwalejin ta barauniyar hanya, wadda hakan ya yi nuni da cewar kwalejin na fuskantar matsalar shugabanci, haka kuma sun yi zarge-zarge da dama. Daga bisani dai ASUP ta rubuta takardar kokenta ga gwamnatin jahar, wannan dalilin ne wasu ke ganin gwamnatin ta bincika gami da yanke wannan hukuncin na rushe dukkanin shuwagabanin gudanarwa na kwalejin nan take.


Advertisement
Click to comment

labarai