Connect with us

MANYAN LABARAI

Fayose Ya Rubutawa Buhari Wasika Kan Canza Sunan Jami’ar Oye-Ekiti

Published

on


 Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya rubuta takardar tuni ga Shugaba Muhammadu Buhari, a kan canza sunan Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Oye,  Ekiti (FUOYE) zuwa, Jami’ar Adeyinka Adebayo, watau tsohon gwamnan mulkin Soja na tsohuwar shiyyar shiyyar yamma, marigayi Janar Robert Adeyinka Adebayo.

A ranar 20 ga watanMayun shekarar 2017, ne dai Adebayo, ya rasu a kauyensu na Iyin-Ekiti.

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a lokacin da yake mukaddashin Shugaban Kasa ne wajen jana’izan Adebayon,ya bayyana wannan shawarar da gwamnatin ta tarayya ta yanke, na canzawa Jami’ar suna zuwa Jami’ar gwamnatin Tarayya ta Adeyinka Adebayo, domin jinjinawa ga gudummawar da tsohon gwamnan yankin ya bayar.

Yanzun kimanin watanni tara kenan da bayar da waccan sanarwar, amma har yanzun ba a fara aiki da ita ba.

Jami’in hulda da manema labaran gwamna Fayose, Idowu Adelusi, ne ya bayyana hakan a cikin wata takarda mai kwanan watan 29 ga watan Janairu 2018, mai lamba, EK/GOB/28/93, inda aka nemi Shugaban kasan da ya tabbatar da alkawarin canjin sunan da ya yi.

“Kamar yadda mai girma Shugaban Kasa ya sani, Marigayi Adebayo ya rasu ne a shekarar da ta gabata.

“Mataimakin Shugaban Kasa ne ya wakilce ka a wajen jana’izan wacce aka yi a ranar 20 ga watan Mayu na shekarar ta 2017.

“A wajen ne Mukaddashin Shugaban Kasan ya bayyana wannan  shawara ta gwamnatin Tarayya na canza sunan Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Oye-Ekiti, zuwa Jami’ar Adeyinka Adebayo, domin yabawa da shugabancin da marigayin ya baiwa wannan yankin namu.

“Sai dai kuma, yau sama da watanni bakwai kenan bayan waccan sanarwar, ba wani abin da ya wakana.

“Ya Mai Girma, wannan takardar, ta tuni ce, a kan wancan muhimmiyar shawara da gwamnatinka ta zartar.”


Advertisement
Click to comment

labarai