Connect with us

NAZARI

Daga Na Gaba… Su Wa Ke Yi Wa Talakawan Nijeriya Tunani?

Published

on


Tare da Abdurrahman Aliyu 08036954354

Irin halin da wannan kasar ta shiga tun daga shekaru hudu da suka wuce, ya zuwa yanzu ya kamata ace talakan wannan kasa ya shiga taitayinsa, musamman ta fuskar zabe da tura wakilai a inda suka dace. Amma wani abin mamaki kullum wuri guda ake ba wani cigaba ko wata sabuwar hanya wadda zata nuna cewa lallai talakawan wannan kasar sun ji a jikinsu. Duk kokarin kiran sauyin da suke a baki ne kawai, amma a zahiri ba haka abun ya ke ba, domin a zukatansu da aikace babu sauyin , asali ma ba su san me ake kira da wannam sunana sauyi ba ko kuma canji.

Abin da na lura talakawan wannan kasa ke nufi da canji shi ne a fitar da wani wanda ke bisa mulki a kawo wani ko da kuwa wanda za a kawo din bai kai nagartar wancen ba in dai an fitar da shito su a wajensu bukata ta biya. Shi ma wannnan din da aka kawo kuma ba sai ya dauki lokaci ba wasu daga cikin talakawan za su fito su fara ikirarin sai sun sauya shi, wannan dabi’a kusan tana cikin abin da ya ke ciwa wannan kasa tamu tuwo a kwarya.

A yau wanan fili zai yi duba ne kan wasu abubuwa da kullum suke kawo wa wannam kasar tarnaki da koma baya, musamman ta la’akari da ,aben kananan hukumomi da aka gudanar a Kano ranar asabar din da ta wuce 10/2/2018. Wannan zabe da aka gudanar akwai abubuwan dubawa da yawa a cikinsa, da farko dai zabe ne wanda Jihar Kano ta shirya a karkashin hukumar zaben jihar, shi wanda ke shugabanci hukumar gwamnatin ce ta nada shi bisa wannan mukami, kuma tun da aka nada shi ake ta tayashi murnar ya samu babbar kujera, sannan wani abun mamaki shi wanda aka nada wannan hukuma wai Farfesa ne, wanda ana ganin cewa ko ba kome ya na da wani tunani dabam da na sauran mutane, musamman a bangaren ilimin boko, shi ya sa ake ganin zai iya jagorantar duk wani abu da aka bashi wanda za a iya yi wa al’umma adalci kuma a kwato masu hakinsu, sannan a matsayinsa na Farfesa kuma mai ilimi ana tunanin zai yi koyi da sauran Farfesa ya yi abin da zai bar wa kansa da iyalansa tarihi mai kyau ta yadda na dalibansa za su iya yin alfahari da shi kuma su yi koyi da shi a matsayin wanda ya yi wani abu mai kyau.

Tun tashin farko yadda aka sayar da takardar shedar yin takarar da kudi tsagaga alamu suka nuna cewa ba za a yi adalci ba ga zaben wanda hakan ne ya sa wasu jam’iyyun adawa suka kasashiga, zaben saboda a matsauinsu na wadanda basu da gwamnati a hannu kudaden da aka sanya ya yi masu yawa, amma hakan bai sa aka rage wadannan kudade ba. To duk ba ma wannan ne kbun korafi ba ko tayar da hankali,sai yanayin yadda aka gudanar da zaben, na farko dai an samu mutukar jinkiri na rashin kawo kayan aiki a rumfunan zabe da wuri, inda wasu rumfunan sai karfe biyu na rana aka kawo kahan aiki, sannan aka fara zaben duk da cewa ba a samu mutane sun fito da yawa ba wajen kada kuri’a.

Babban abin da ya fi kome takaici shi ne yadda aka rika nuna hotuna da bidiyon yadda ake gudanar da zaben, in da a rumfuna da yawa aka samu kananan yara sun bi layi zasu kada kuri’a kuma an basu sun dangwala sun jefa. Sai kuma bidiyon da aka samu wanda ya nuna yadda ake ta dangwale kuri’un ana jefawa, wasu ma ba a runfunan zaben ba ne a gidaje ne ake dangwalewar. Kusan dukan kagafen yada labarai na kasar nan sun hakalto wannan kwamacala wadda ake ce wai zabe ne.

In da tashin hankalin yake ta yadda shi shugaban hukumar zaben ya fito ya ayyana cewa jam’iyyar APC mai mulkiita ta cinye wannan zabe baki daya, kuma an yi zaben cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da samin korafin magudi ko wani abu da ya sabawa doka ba. Yanzu ace mutumin da ya kai girman Farfesa ya shirya irin wanan abun kuma bai ji kome ba a rayuwarsa, gani yake ya yi daidai? Shin yaushe ne to kasar nan zata gyaru in har mai ilimin kamar farfesa zai ba da goyan baya a aikata rashin dai-dai a kasar nan kuma ya nuna daidai ne, wannan ya nuna ko a cikin aji ba bu abin da ya ke koyawa dalibansa sai abin da yake ba daidai ba, wanda ya hada da rashin gaskiya da kuma hanyoyin batar da al’umma.

Babban karin tashin hankalin shi ne yadda shi Maigirma gwamana ya shirya bikin rantsar da wadannan mutane da aka ce zabarsu aka yi ba tare da yaji kome ba a rayuwarsa, wannan wace irin kasa ce wadda za a ce mutum mai shekaru kamar na Maigirma gwamanan Kano, kuma sannan mai rike da mukamin gwamna zai goyi bayan karya kiri-kiri domin kawai ya na son cimma wata manufa ta shi wadda iyakar ta nan duniya, shin mai girma gwamna bai tunanin cewa akwai mutuwa? Kuma za a tambayeshi kan abin da ya shuka, me yasa mai girma gwamna ba tuna cewa wadannan mutane da ya rantsar a bisa mukaman da ya nada su, ba zasu iya tsinana mashi kome ba a lahira, iyakar shi da su nan duniya.

Ya na da kyau ko ba kome idan shekaru suka taru ga mutum to ya rika tunanin lahira kawai ba wai abin da zai zama a duniya ba. Su kuma wadanda suka shirya wannan kwamacala su tuna cewa da yawa sun yi makamancin irin abin da suka yi a baya, amma yamzu suna ina?

Idan muka koma ta bangaren talakawa kuwa zamu ga cewa lallai lamarin talakan Nijeriya akwai sake cikinsa, na farko ya kasa gane cewa an hana shi ilimi, sannan ya kasa gane cewa shi bawa ne na wasu ya tashi ya nemi ‘yanci tun wuri bai kure masa ba. Domin duk mutanen da suka yi wannan aikin zaben talakawa ne, ya kamata su gane cewa wadannnan mutane da suka sanya su yin wannan aiki tsallakewa kawai za su yi su barsu domin ba zasu amfane su da kome ba, amma saboda tsabar Jahilci da rashin sanin ciwon kai, sai ga su a hoton bidiyo, wani sokon ma a cikin gidansa suna dangwale kuri’un mutane kan kudi kalilan, wadanda tabbas na san yazuwa wannan rubutun kudin sun kare.

Ya na da kyau tallakan Nijeriya ya sani cewa, damar kawo gyara ko sauyi a hannunsa ta ke, in ya gyaru to kome zai gyaru, in kuwa tallakawa za su bigaba da yin irin wannan hali da sukayi a Kano to lallai babu ranar da wannan kasa zata samu canji, za ai ta tafiya ne wuri buda ba gaba ba baya. Don haka, yana da kyau talakawa su shiga taitayinsu, su sani cewa wannan hali da suka sa kansu ciki to fa ba zai bille ba, kuma ba nufo hanyar gyara ba, talaka a bangar siyasa ai banza a banza ne kawai.

Babban kalubale kuma ga jam’iyyar APC ya ke, in dai da haske jam’iyyar APC su ke na ganin sun kawo sauyi mai amfani to ya zama wajibi su fadi matsayarsu kan wannan zabe na Kano, su takawa wannan zabe burki kuma su fito su barranta da shi, domin in har za su rika cewa, jam’iyyar PDP ta lallata kasar nan, sannan sun kawo magudin zabe da sauran abubuwa na cin hanci da rashawa, amma kuma su shirya zabe irin na kananan hukumomin Kano to lallai ba a dauko hanyar gyara ba kuma ba da gaske suke, sannan su bannar su ma ta fi ta bayan, domin su an zabe su ne saboda ana kyautata masu zaton zasu kawo gyara, amma kuma abun ya gagara. Don hakakalubale ne garesu su tashi tsaye su magance wannan matsala, kuma a hukunta duk mai hannu a cikinta, domin masu iya magana dai sun ce, “ Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta”


Advertisement
Click to comment

labarai