Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Abubuwa 13 Da Ba A Sani Ba Dangane Da Murtala Muhammad

Published

on


Murtala Muhammad ya na daya daga cikin shugabannin Nijeriya da ba zai yiwu a manta da su ba. Matashin shugaba dan shekaru 37, an yi mishi kisan gilla a ranar 13 ga watan Fabrairu, shekaru 43 kenan cur da su ka gabata; a wani shirin juyin mulkin da ba a yi nasara ba, karkashin shirin Laftanar Kanar Buka Suka Dimka.

Duk da an dauki shekaru da yin wannan danyen aiki na kashe Murtala, amma jimamin rashinshi bai gushe ba a tsakanin sojoji da farar hula.

An haifi janar Murtala Ramat Muhammed ranar 8 ga watan Nuwambar shekarar 1938 a garin Kano, ya yi karatu a kwalejin Barewa da ke Zaria.

A shekarar 1959 ya shiga aikin soji, inda ya yi karatu a makarantar sojoji ta Royal Military Academy ta Sandhurst da ke Burtaniya.

Janar Mutala ya samu mukamin Laftanal a shekarar 1961. Gabanin komawarsa Nijeriya a shekarar 1962, ya je rangadin aiki a kasar Kongo a matsayin wani wakilin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya.

A shekarar 1964 ne a ka ba shi mukamin Manjo na wucin gadi, bayan da a ka ba shi ragamar kula da sashin sadarwa a hedikwatar rundunar soji ta Kaduna.

Janar Murtala ya koma Lagos inda ya zauna tare da kawunsa Alhaji Inuwa Wada a lokacin da ya zama ministan tsaro, kuma ya kasance a can har lokacin da a ka yi juyin mulki na farko a shekarar 1966.

Shugaban kasa manjo janar Aguiyi-Ironsi ya kara masa girma zuwa Laftanal Kanal duk da kuwa shi ma wannan karin girma na wucin gadi ne, a watan Afrilun shekarar 1966.

Bayan juyin mulki na farko, sau uku janar Murtala ya na neman hada kan sojojin arewa da ke Legas domin a yi juyin mulki na biyu, sai dai wannan yunkuri bai yi nasara ba sakamakon harbe wasu sojoji da a ka yi a Abeokuta.

Janar Murtala Ramat Muhammed ya taka rawar gani a yakin basasar da a ka yi a shekarar 1967 lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu ke neman balle yankin Biyafara daga cikin tarayyar Nijeriya.

A wancan lokacin janar Murtala ne ya jagoranci rundunar sojin da su ka murkushe sojojin Biyafara tare da kawo karshen yakin basasar kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 1967.

Ya na matsayin Birgediya ne sojojin da su ka yi juyin mulki na uku a Nijeriya su ka nada shi a matsayin shugaban kasa , inda a watan Janairun shekarar 1976 a ka kara masa girma zuwa janar mai anini hudu, wato kololuwa kenan.

Har wa yau a wannan lokaci ne janar Murtala ya kirkiro da sabbin jihohi 7 wadanda su ne Neja, Bauchi, Gongola, Benuwai, Ogun, Imo da Bendel. Sannan kuma ya bayyana bukatar mayar da babban birnin Nijeriya zuwa Abuja da kuma alkawarin mika mulki ga farar hula a shekarar 1979.

Kisan Janar Murtala Muhammad al’amari ne wanda ya girgiza Nijeriya, domin kuwa al’umma sun tsinci kawunansu a karo na farko an halaka shugaban kasa me mulki. Janar Murtala Muhammad ya na dan shekaru 38 a duniya a lokacin da a ka aikata mishi wannan danyen aiki.

Da yawan ‘yan Nijeriya ba su san wanene Murtala Muhammad ba, kawai dai an san shi ne a jikin kudi Naira 20, sai kuma abubuwan da magabata su ka fadi wa ‘ya ‘ya da jikoki dangane da wanene shi. Saboda wannan dalilin ne LEADERSHIP A Yau ta tattaro muhimman abubuwa guda 13 wadanda ya kamata a sani dangane da Murtala. Su ne kamar haka:

 1. An haifi Murtala Muhammad a ranar talata, 8 ga watan Nuwamban 1938, a jerin gidajen Kurawa da ke cikin birnin Kanon Dabo. Sunan Mahaifinshi Riskua Muhammad, mahaifiyarsa kuma sunanta Uwani Ramatu. Su takwas ne a gidansu, mace guda da maza 7. Kuma Murtala Muhammad ne na biyu.
 2. A ranar 26 ga watan Janairun 1952, a ka dauki Murtala a matsayin dalibi na 941 a kwaleji, Kwalejin da a ka assasa ta a shekarar 1909. Ya na daya daga cikin dalibai 10 da su ka je makarantar daga Kano. Daya daga cikin abokan karatunsa shi ne marigayi Muhammad Shuwa, wanda ‘yan bindiga dadi su ka harbe shi har lahira a gidansa da ke garin Maiduguri a watan Nuwamban 2012.
 3. Murtala ya halarci wata makarantar horas da soji a kasar Ghana wacce a lokacin a ke kiranta da ‘Regular Officers Special Training School, ROSTS’, wacce a yanzu a ka sauyawa suna zuwa ‘Ghana Military Academy. A can ne Murtala ya fito a matsayin mataimakin Laftanar. Obasanjo da Gowon duk sun yi wannan makarantar.
 4. Murtala soja ne kaifi daya, amma fa a wurin iyalinshi mutum mai saukin kai. A shekarar 2006 matarshi Hafsat Ajoke Muhammad, wacce bayarabiya ce, ta bayyana cewa; “A gida da wurin aiki, mijina ba shi da bambanci. Kamar yadda bay a baki biyu a wurin aiki, haka ma a gida. Mutum ne mai dattako da sanin ya kamata.”
 5. Ko kun san, Kawun Murtala ne ya yi sanadiyyan haduwarshi da matarsa Hafsah? Bayan da kawun na shi ya hada su, su ka fara soyayya, haduwarsu ta farko a jihar Kaduna ne, a can ne kuma Murtala ya sanar da ita burin zuciyanshi har ta kai ga an daura musu aure a shekarar 1963 bayan ta kammala karatunta, kuma a wannan shekarar ne dai ya kai mukamin Kaftin a gidan soja. A shekarar 1965 Allah ya albarkace su da diya mace, wacce daga bisani ta yi karatu a kwalejin sarauniya ‘Kueens college’ da ke Yaba a jihar Legas.
 6. A lokacin da a ka yiwa Murtala kisan gilla, diyarsa Zalihatu ta na ‘yar shekara biyu da haihuwa, ita kuma diyarsa Jummai ta na ‘yar jinjira.
 7. Bayan an kashe Murtala, yayin da labarin ya iso ga matarsa Hafsah, a take ta yanke jiki ta zube a kasa cikin kuka da jimami, wanda hatta wadanda su ka kawo labarin sai da su ka firgita bisa tsoron halin da za ta iya fadawa.
 8. Ya zuwa yanzu dai matar Murtala, wato Hafsah Ajoke tsufa ya kamata, a na matukar ganin kimarta a kasar nan, saboda duk da kasantuwarta matar shugaban kasa a wancan lokacin, ba ta yi dagawa da wuce gona da iri ba. Allah ya albarkaci aurenta da Murtala da ‘ya ‘ya shida, su ne; Aishat, Fatimah, Zakari, Riskua Abba, Zalihatu, da kuma Jummai. Gabadayansu sun yi aure.
 9. Ko kun san a karshen 1964 ne Murtala ya kai matsayin Manjo (amma na wucin gadi) ‘T/Major’.
 10. Yakin basasan da a ka yi a Nijeriya wanda ya dauki watanni 30 a na gwabzawa (1967 zuwa 1970), Murtala na daga cikin wadanda su ka fuskanci wannan gumurzu daga farko har zuwa karshenshi.
 11. Da yammacin ranar 30 ga watan Yulin 1975, Murtala Muhammad ya gabatar da jawabi ga ‘yan kasa a matsayinsa na sabon shugaban kasa, kuma babban kwamandan askarawa.
 12. Murtala Muhammad ne ya samar da wani kwamiti wanda mai shari’ah Ayo Irikefe domin samar da karin jihohin Neja, Bauchi, Gongola, Benuwai, Ogun, Imo, da Bendel a watan Disambar 1975. Kwamitin kuma ya zo da rahoton da a ka yi amfani da shi wurin samar da sabbin jihohi a shekarar 1976.
 13. Murtala namijin gaske ne, dakakke kuma marar tsoro. Sojoji ‘yan uwansa sun shaide shi da cewa bai san wargi ba, kuma ba ya amsan wargi balle ya yi wasa da mai kawo wargi.

 

 

 

 

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai