Connect with us

SIYASA

Zaben Kananan Hukumomi A Kano: APC Ta Yi Wa Jam’iyyun Adawa Tumbur

Published

on


Shekaran jiya Asabar 10 ga watan Fabrairun 2018 ne ranar da hukumar Zabe mai zaman Kanta ta Jihar Kano, karkashin shugabancin Farfesa Garba Ibrahim Sheka ta gudanar da zaben Kananan hukumomin Jihar Kano 44. An gudanar da zaben cikin tsattsauran matakan tsaro kamar yadda hukumomin tsaro suka bayyana tun kafin zuwan ranar zaben, hakan kuma ya biyo bayan sa toka sa katsin da aka jima na ta yamadidi dashi tsakanin wasu jigajigan Jam’iyyar APC, haka kuma itama babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta garzaya kotu domin neman izinin kotu da ta dakatar da zaben, sakamakon korafin da suke na cewar an sa kudaden da basa bisa ka’ida a cewar Jam’iyyar ta PDP., amma dai cikin makon da ake sa ran gudanar da zaben sai kotu tayi watsi da wannan kara da Jam’iyyar ta kai gabanta.

Tun farar safiyar ranar Asabar goma ga watan Fabrairun shekara ta 2018 ne jama’a suka fara yin tururuwa zuwan cibiyoyin zaben da ke kusa dasu domin Kada Kuri’arsu, amma dai kamar yadda Jaridar Leadership A Yau  tayi kokarin ganin kwakwaf ta zaga runfunan zabe masu yawa amma dai har lokacin da wakilanmu suka dan bukaci tsahirtawa ba inda suka iske kayan zaben y aisa a cikin kwarya birni da kewaye, misali Mazabar Dan Maliki, Gurin Gawa, Shagari Kwatas, Sheka duk a karamar hukumar Kumbotso, sai kuma Gyadi Gyadi, Daurawa, Darmanawa, unguwa uku a k1aramar hukumar Tarauni, Filin sukuwa, Brigade, kwanar Jaba, PRP a karamar hukumar Nasarawa da kuma Bela, Rangaza da Zaura babba a karamar hukumar Ungogo duk wadanan wurare kayan zabe bai isa kan lokaci ba.

Amma bayan wasu lokuta kuma si kayan suka fara isa runfunan zaben aka ci gaba da gudanar da zaben, babban abinda yafi daukar hankali shi ne yadda aka samu karancin fitowar jama’a runfunan zabe, wannan kuma ana ganin yana da alaka da ficewar babbar Jam’iyyar adawa ta PDP, sai kuma suma masu biyayya ga darikar Kwankwasiyya sun kauracewa zaben kananan hukumomin. An ci gaba da kada kuri’a cikin kwanciyar hankali musamman ginin babu wasu jam’iyyun adawa da ake karawa dasu a lokacin zaben.

A mafi yawancin kananan hukumomin Dan takarar Jam’iyya mai Mulki ta APC ne kadai ke takarar kujerar shugabancin karamar hukuma, duk da an samu a wasu kananan hukumomi an samu wasu jam’iyyun sun tsayar da dan takara duk da cewar jam’iyyun ba fitattu bane, sai dai kuma an gudanar da zaben cikin kwanciyar hanklai ‘yan kalo lafiya mai wasa lafiya.

Tun da magaribar fari aka fara samun sakamakon zaben daga wasu kananan hukumomin inda Jam’iyyar APC ta ci gaba da yiwa sauran jam’iyyun dukan ‘ya’yan kadanya, musamman yadda Jam’iyyar ta lashe daukacin kujerun Kananan hukumomin Jihar Kano 44 da kuma Kansiloli baki daya, wannan ba wani sabon abu bane idan aka tuna alokacin Mulkin Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso wanda tun kafin zuwan ranar zaben ya bayyana cewa kazarsa tayi kwai guda 44 kuma ko daya ba zaiyi maragurbi ba, kuma hakan ce ta faru inda ya lashe daukacin kujerun alokacin mulkinsa.  A wannan karon a iya cewa lamarin ma kamar ya zarta wancan domin ita kazar Ganduje da ‘ya’yanta ma aka ganta, domin a wannan lokaci babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ma guduwa tayi ta bar ladanta.

Wani abin sha’awa kuma wanda tarihi ne ya maimaita kansa inda Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatarwa da al’umma cewar shi yana da kyakkyawar tarbiyar girmama dan Adam, musamman lokacin da ya isa mazabarsa A Ganduje cikin karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano. Gwamna Ganduje layi yabi kamar kowane talaka domin tantance shi ba tare da an hargitsa wurin zaben ba da sunan zuwan Gwamna. Gwamna Ganduje ya bayyana dalilin haka alokacin da yake zantawa manema labarai bayan kada kuri’ar tasa da misalin karfe 12:20 na rana, inda yace babu wani  fifiko alokacin kada kuri’a domin kowacce kuri’a kirga ta ake, saboda haka yace kuri’arsa ba fin ta kowa tayi ba a tsarin demokaradiyya.

Gwamna Ganduje ya  ci gaba da cewa bin layi alokacin zabe shi ne tsarin da yafi dacewa alokacin, yace mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne mai tsari don haka  ya bukaci jama’a da cewa kowa ya zama mai da’a da kuma bin ka’ida, saboda haka sai Gwamna Ganduje ya nuna gamsuwa da yadda hukumar zabe mai zaman Kanta ta shirya wannan zabe musamman yadda kayan zabe suka isa runfuna zabu  akan lokaci.

. Idan za a iya tunawa mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II haka ya yi a lokacin zaben Gwamna da shugaban kasa ashekara ta 2015 a madabarsa ta Gandun Albasa, bayan isowarsa wurin saikawai  Mai martaba sarki ya bukaci sanin wane na karshe domin bin layi, hakan ya karawa Jama’ar Kaunar mai martaba sarki

An gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali wanda har zuwa lokacin kammala zaben ba a samu bullar wani rahootn rikici ba ko makamancin haka. Kuma zaben ya gudana a daukacin kananan hukumomin Jihar Kano 44.


Advertisement
Click to comment

labarai