Connect with us

WASANNI

Yan Wasana Sun Gaji Sosai, In Ji Valverde

Published

on


Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona. Enersto Valverde ya bayyana cewa yan wasan kungiyar sun gaji da buga wasanni kuma shine dalilin dayasa basu samu nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Getafe ba a wasan da suka buga a ranar Lahadi.

Balberde ya bayyana hakane bayan kungiyarsa ta buga wasa canjaras da kungiyar kwallon kafa ta Getafe bayan da kungiyar tasa ta buga minti 45 din farko batare da takai hari ba a ragar Getafe.

Yace, yan wasan kungiyar sun fara nuna gajiya sosai sakamakon wasanni da suka fara yimusu yawa kuma yana fatan zasu samu dan hutu domin su murmure sosai.

Yaci gaba da cewa suna bukatar hutu yadda yakamata sakamakon acikin wannan makoon suka samu damar zuwa wasan karshe na cin kofin Copa Del Rey na kasar ta sipaniya.

Yaci gaba da cewa  yan wasan kungiyar Getafe sun rufe yadinsu na 18 sun hana yan wasansa shiga domin cin kwallo amma kuma duk da haka yan wasan sunyi kokari sosai.

Barcelona dai ta buga wasanni 12 cikin kwanaki 39 kuma zata dawo wasan laliga a ranar Asabar a wasan da zasu ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Eibar.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai