Connect with us

MANYAN LABARAI

’Yan Sanda 150, 000 Ke Aiki Gadin Manyan Mutane A Nijeriya

Published

on


Hukumar ‘Yan Sanda ta kasa (PSC), ta ce sama da ‘yan sanda 150, 000 ne ke gadin manyan mutane a kasar nan.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, a shekarar 2015, ya umarci cewar a janye ‘yan sandan da aka tura suna yin gadin manyan mutane police a kasar nan a kuma turasu don tunkarar kalubalen rashin tsaro da ake fuskanta a kasar

nan.

Shugaban hukumar ta ‘yan sanda ta kasa, Mista Mike Okiro ya sanar da hakan a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa a ranar lahadin data gabata a Abuja.

A cewarsa, “bazamu iya barin rabin yawan ‘yan sandan da muke dasu a kasar nan suna ci gaba da yin gadin manyan mutane ba a kasar nan. ”

Mista Mike yace, hukumar tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda tuni sun fara kaddamar da shirye-shiryen janye ‘yan sandan, amma karancin kudi ne ke kawo shirin cikas.

Shugaban yaci gaba da cewa, “baza mu iya kaddamar da umarnin janye ‘yan sandan ba saboda muna fama da karancin kudi”.

Ya jaddada cewar, abin takaicin shine,  wadanda suka rike mukaman Ministoci sama da shekaru goma zuwa shekaru sha biyar, har yanzu ‘yan sanda ne suke gadin su.

Mike ya yi nuni da cewa, rundunar ‘yan sandan bazata iya yakar karancin jami’an ‘yan sanda da take fama dashi ba alhali mafi yawancin jami’an ta,  suna ci gaba da gadin manyan mutane a kasar nan ba.

Shugaban yace, yawan jami’an nata sun isa su ga yawan alummar dake kasar nan, amma akwai bukatar kara daukar ‘yan sanda.

Sai dai Maki ya bayyana cewar karancin kudi shine babban cikasa da hukumar ke fuskanta wajen wajen kara daukar sababbin ‘yan sanda don ta kara inganta ayyukan ta.

A cewar sa, “ rundunar ‘yan sanda ba’a bata kason kudi da ya kamata a bata da kuma karancin jami’a.

Ya kara da cewa, “maganar kudi abu ne babba ga hukumar, in har ana son rundunar ‘yan sanda ta kasance a yadda ta kamata dukkan kasafin kudin kasar nan ba zai iya isar ta ba.”

Shugaban yace kudurin gidauniya ta “yan sanda dake gaban majalisar kasa in an tura ta zama doka, zata taimaka wajen magance matsalar ta rashin kudi.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai