Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Na Ke Safarar Kwaya Da Kayan Sojojin Aro’

Published

on


Wani dalibin Jami’a, Ahmed Hassan, wanda aka kama da laifin yin shigar burtu, ya bayyana yadda yake aron kakin Soja daga wani abokinsa Soja, yana yin safarar muggan kwayoyi.

Hasan, ya bayyana cewa, yana amfani da kayan aikin Sojan ne domin ya sami saukin wucewa shingayen jami’an tsaro da muguwar hajar na shi ta tabar Wiwi.

‘Yan sanda ne suka kama mai laifin a Lagas, sa’ilin da yake kokarin shiga da tabar ta wiwi cikin wata babbar makaranta.

Hassan, dan shekaru 27, ya bayyana abokin na shi da ya ara masa kakin Sojan da suna Rufa’i, wanda yake aiki da rundunar Soja da ke Ikorodu, a can Legas din.

Dubun na shi dai ta cika ne a sa’ilin da ya sanya kayan aikin Sojojin, sai wani dan sanda ya yi shakkun kasantuwarsa Soja, ko da ya fara yi ma shi tambayoyi, nan take ya fahimci cewa lallai

ba Soja ne shi ba.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Legas, Imohimi Edgal, ya bayyana Hassan a matsayin wanda yake amfani da kayan Sarki wajen aikata laifuka.

Ya kuma bayyana cewa da zaran sun kamala bincikensu za su gabatar da mai laifin a Kotu.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai