Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Aka Gudanar Da Taron Kungiyar Muryar Talaka A Kontagora

Published

on


Kungiyar Muryar Talaka Ta Kasa, ta samu nasarar gudanar da babban taronta na shekara-shekara a birnin Kontagora mai dimbin tarihi.Taron wanda aka fara ranar Jumma’a, 9 ga watan Fabarairu, shekarar 2018 Miladiyya, wanda shi ne karo na bakwai tun kafa kungiyar a shekarar 2003, Allah ya albarkace shi domin  ‘ya’yan wannan kungiya daga kowace kusurwa ta Najeriya, dama wasu kasashen Afirika Kamar Kamaru suka halarta. Sannan akwai shugabannin wasu kungiyoyi kamar kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara da Oyo, da wakilan kungiyar Zabi Sonka ta kasa, da Kungiyar Kontagora Frontiers Forum, Gwamutsawa da dimbin kungiyoyin sun samu halarta wannan taro karo na 7.

Rassan kungiyar daga jihohi daban-daban misali, Taraba karkashin shugaba Muhammad G. Mairariya Garba Chedi, Gombe karkashin shugaba Adamu Babale Makera, Bauchi karkashin Ahmed Arab Azare, Yobe karkashin Sale Bakuro Damaturu, JIgawa karkashin Audu A. Audu Gumel, Kano wanda  MUrtala Dankanawa Garo ya jagoranci tawagar, saboda ciyaman nasu wata hidimar ta tsaida shi gida, da Katsina wanda Kwamared Kabir Shehu Yandaki ya jagoranci tawaga mai karfin membobi 33, sai Kaduna wanda Usman Mukhtar ya wakilta, Nasarawa Shafale, Abuja, Badamasi Mohammed Kasuwar Yanya,Zamfara Hafizu Balarabe GUsau ya jagoranci tawaga mai dauke da sama da membobi sittin. Sauran jihohi sun hada da Sokoto karkashin jagorancin Kwamared Abubakar Tukur Bodinga, sai Kebbi karekashin jagorancin Hamza Galadima Birnin Kebbi. Akwai kuma mutane masoya kungiyar da sukai tattaki daga garuruwa daban-daban don kishin Talaka da Arewa suka zo wannan taro. Misali fitaccen marubucin nan, wanda ya taba lashe kyautar YALI ta Mandela Washington Fellowship wato Ibrahim Aboki ya zo daga Bauchi. Cikin manyan baki da suka zo domin sui jawabai ko gabatar da mukalu akwai Pastor Yohanna Buru daga Kaduna, Dokta Aliyu Muhammad Muri daga Katsina. Yayin da daga cikin gida muka samu bakuncin Dokta Isa Adamu daga Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai, da Dokta Muhammad Ibn Imam daga babbar kwalejin tarayya ta horon mallamai, dake Kontagora wato FCE Kontagora.

Akwai ‘yan siyasa da shugabannin Al’umma misali, limamin garin Kontagora, ya zo, akwai wakilin mai martaba Sarkin Sudan Sa’idu Na Maska wanda ,akwai gwarzon shekara na kungiya wato Alh. Abdurrahman Buhari MK, wanda hamshakin attajiri ne dake taimakawa Talakawa, saura sun hada da Ajiyan Kontagora Alhaji Mamman Ajiya, Engr. Rabi’u Idris SB mukaddashin darakta gidan rediyon jihar Neja,dan majalisa mai wakiltar mazabar Agwara, wato Barrister Bello Ahmad . Babban bako na Musamman shi ne ministan matasa da Wasanni, wato Barrister Solomon Dalung, wanda babban hadimin ofishinsa ya wakilta wato Alhaji Maiwada Danmallam.

A ranar Jumma’a, da dare misalin karfe tara da rabi an shirya ma membobin kungiya da sauran baki da suka zo daga ko’ina liyafar bangirma. Bayan jawabin maraba da barka da zuwa  daga bakin  shugaban kungiyar na kasa

Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, an nishadantar da mutane inda tawagar ‘yan wasa da suka hada da Washasha group daga Katsina, Ahmed Ekualizer daga jihar Zamfara, yan wasan tauri daga Kontagora duk sun nishadantar. Daga nan, aka tashi wurin karfe 11:30 na dare.

A rana ta biyu, wadda ita ce ranar babban taron, an fara da ziyarartar fadar mai martaba sarkin Sudan Alhaji Sa’idu Na maska, inda shugaban kungiya na kasa Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, da shugaban kungiya na jihar Neja Alhaji MUrtala Maigyada Kontagora, da uban kungiya Barrister Solomon Dalung wanda Alhaji Maiwada Dammalam ya wakilta da sauran membobin kungiya. Tun da farko saida Shugaba Zaidu ya shaida ma fadar cewa sun zo ne domin su samu albarka sannan kamar yadda suka saba duk jihar da suke taro, to dole suna fara wa da ziyarar uwayen kasa saboda muhimmancinsu yayi fatan Allah ya kara ma sarki lafiya wanda baya nan saboda jiyya da yake. A nashi jawabin, wakilin mai martaba Sarkin Suda, Mawakin Kontagora shima ya nuna goyan bayan sa ga kungiya, kuma ya ce sun dade suna jin sunan kungiyar, sai a wannan lokacin suka samu haduwa da shugabanninta.

An wuce dakin taro wato Adaka conference hall, dake a Otel din Safara, inda aka fara taro gadan-gadan da misalin karfe 11 na safe. Bayan jawabin maraba daga shugaban kungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Niger, wato Alhaji Murtala Maigyada Kontagora,sai jawabin shugaban kungiya na kasa Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, inda ya jinjinawa ‘yan kungiya bisa  goyan baya da suke ci gaba da ba kungiya da irin jajircewa ta gwagwarmaya da suke.”Ina tabbatar ma duniya cewa kan ‘ya’yan wannan kungiyar hade yake, kuma tunda ma muke taro bamu taba irin wannan da akai ba yau” in ji shugaban. Ya kuma nuna cewa kishin talaka, hakuri da rashin kwadayi ne yasa har aka zo inda ake yanzu.Shugaban ya tuno wasu membobi dasuka rasu  inda yai masu addu’a, tare da kara ba iyalansu hakurin jure rashi. Daga karshe yai fatan alheri ga dukkanin mahalata taron da sauran yan kungiya.

Malamai daban-daban sun gudanar da laccoci kan kalubalen dake Fuskantar Najeriya wajen kokarinta na zama hamshakiyar kasa. Misali, Dokta Aliyu Muhammad Muri daga Katsina, ya maida hankali akan kalubalen Ilimi da Arewacin Najeriya ke fuskanta inda ya fitar da shawarwari yadda za a rage cunkuso a makarantu, da yadda za a rage ma gwamnati lodin dake kanta da ya shafi ilimi, da yadda za a inganta jindadin malamai,yadda za a karfafa sanya ido ,da kara ma shugabannin makarantu kwarewa da hana fitar yaranmu makaranta kafin su kammala. Dokta Muri dole sai an gyara ilmi idan har Arewa zata ci gaba.

Laccar Dokta Muhammad Ibn Imam na Kwalejin Ilimi ta tarayya dake Kontagora ta tabo kalubalen gina kasa. Inda ya ruwaito Farfesa Ibrahim A. Gambori tsohon wakilin Najeriya a Majalisar dinkin duniya wanda a wata Lacca ya bayyana kalubale guda biyar (5) dake fuskantar gina Najeriya. Na farko tarihinmu na mulkin mallaka, na biyu kalubalen tattalin arziki da rashin daidaito na uku matsalar kundin tsarin mulki, na hudu matsalar ingatattun hukumomi da turakun dimokaradiyya sannan ta biyar matsalar shugabanci. Baya ga wadannan kalubale da ya kawo, ya sake bayyana wasu kalubalen kamar haka:cin hanci da rashawa, boko haram,rashin aikin yi,matsalar ilimin jami’a, matsalar muhalli, rashin kayan more rayuwa, cin zarafin mata,hadarurrukan abin hawa da sauran su.

Dokta Imam ya bada mafita kamar haka:

– Dole mu sanya kishin kasa. Kasarmu ta zama farko kafin wani abu.

– Dole gwamnati ta mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin ciyar da kasa abin da ya shafi samar da gidaje, ruwan sha, mukamashi, hanyoyi da sauran su.

– Dole a kyautata rayuwar matasa

– Su ma matasa dole su mike su nemi na kansu maimakoin mita da korafi kawai.

– Dole a cigaba da yakar rashawa da cin hanci.

Daga karshe dai, taron kungiyar Muryar Talaka ya zo karshe, kuma kowa na sambarka, da fatan duk abin da aka tattauna a taron za ai aiki da shi. Allah ya ba mu ikon aiki da shi, yasa suma shugabanninmu su amfana daga taron. Kowa ya kama hanyar komawa garunsu inda za a ci gaba da gwagwarmaya bisa karin fahimta da aka samo daga wannan taro karo na bakwai.


Advertisement
Click to comment

labarai