Connect with us

KASUWANCI

Wuta Mai Amfani Da Hasken Rana: Dalilin Da Ya Sa Aka Gaza Kammala Aikin

Published

on


Majiya mai tushe ta hanyar wani kundi da aka samu a asirce a cikin satin da ya gabata ya yi bayani dalla-dalla akan  dalilin da ya sa aka samu tsaiko akan samar da wutar lantarki da gudanar da aikin samar da sababbin wutar lantarki guda sha hudu ta hanyar hasken rana da zai samar da megawatts 1,125 ga hanyar layin wuta ta kasa.

Sai dai, bayanan da suke kunshe a cikin kundin suna cin  karo da juna idan aka yi la’akari da ikirarin Ministan ma’aikatar  wuta da gidaje Mista Babatunde Fashola ya bayyana cewar  (IPPs) ta gabatar da  bukata ga gwamnatin tarayya akan cewar sharuddan ba saboda jinkirin da aka

samu wajen gudanar da aikin.

Aikin samar da wuta ta hanyar hasken rana guda sha hudu da masu samar da wuta masu zaman kansu (IPPs) suka sanyawa hannu na sayen na’urorin a bisa yarjejeniya ta   (PPAs) tare da kamfanin samar da wutar lantarki mai zaman kansa na  (NBET) a watan Yulin   shekarar 2016 don gudanar da aikin samar da wuta, musamman a jihohin Arewacin kasar nan akan jimmalar kudi dalar Amurka biliyan 2.5.

Majiyar mu ta labarto cewar, ci gaba da gudanar da aikin ya tsaya cak akan dalilai da suka shafi samar da  (PPAs) da kuma tsafar kudin wuta da aka amince dashi a wancan lokacin.

A cewar majiyar, a cikin kundin da aka samu daga ma’aikatar kudi gwamnatin tarayya ta hanyar Ministan Kudi uwargida Kemi Adeosun, bayan biyo bayan sanya hannu da aka yi na samar da wuta ta hanyar hasken rana guda sha hudu ta yarjeje da aka kulla a watan Yuni na shekarar 2016, taja kunne akan kashi 11.5 da aka amince akan gudanar da aikin.

Bugu da kari, kundinIt ya kuma yi ikirarin cewar,hanyar da aka bi ta yin aikin dalla-dalla ba,inda saboda haka, zata dakatar da amincewar da aka yi akan yarjejeniyar ta (PCOAs).

Kundin ya kara jaddada cewar, kimanin tsadar kudin da za’a samar da wutar mai aiki da hasken rana, a fadin duniya naci gaba da da yin sauka akan hujjar Nijeriya na fuskantar matsalar in har taci gaba ta amince da yarjejeniyar ta  (PCOAs) akan kashi 11.5 samar da wuta ta (kilowatt) akan awa akan aikin.

Har ila yau, kundin wanda ya hada da bayanai akan abinda zai iya gudana akan hanyar, ya bayyana cewar, matsalar ta samo asali ne bayan da tsohon Manajin Darakta na (NBET) Mista Rumundaka Wonodi, wanda aka ruwaito ya fara gudanar da yarjejeniyar ta (PPAs), amma bai amince da farashin masu sun zuba jari ba, wanda kuma aka yi gaggawar cire shi daga mukamin a watan Mayu na shekarar 2016.

A cewar Wonodi takatarwar, ta bayar da kafa ga wasu jami’ai na (NBET) da kuma Ma’ikatar ta hanyar yanke gudanar da yarjejeniyar da masu son zuba jarin akan farashin samar da wutar kilowat 11.5 da aka amince masu.

An kuma bankado cewar yarjejeniyar akan farashin, wasu manyan jami’an ma’aikatar ne suka yi gaban kansu su kayi su da kansu, inda daga bisani suka mikawa(NBET) ragamar aikin ba tare da bincikar abinda ke shigowa ba.

Kamar yadda wata majiya mai tushe ta danganta harkar, ta bayyana cewar wannanwani shu’umanci ne babba.

A dukkan sati sako yana shigowa, inda sakon ke cewa karin kudin wutar an amince dashi abinda kawai ake bukata, a sanya hannu akan akan yarjejeniyar ta (PPA).

“A cikin sati biyu, munada yarjejiniya guda sha hudu da aka sanyawa hannu.” Bugu da kari, majiyar tamu ta labarto cewar daga cikin sanarwar ta samar da lasisi da hukumar sanya ido akan samar da wuta (NERC) cewar wasu daga cikin masu zuba jari akan samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana da suka samu lasisi, sun samu lasisin akan yarjejeniyar ta  (PPAs), sun samu lasisin ne daga  hukumar ta (NERC) a cikin ‘yan watanni da suka bayan da aka sanya hannu akan yarjejeniyar ta(PPAs).

Daya daga cikin ayyukan da aka tsara za’a gudanar a jihar Nasarawa, an samu lasisin ne watan Nuwambar shekarar 2016, a cikin watanni hudu bayan an samu (PPA) din.

Sai dai kuma, Minista Adeosun a martanin data gabatar akan bukatar ma’aikatar wuta da ayyuka da kuma hukumar (NBET) akan amincewa da aikin na (PCOAs) akan farashin takki amincewa kuma daga cikin wasikun da aka rubuta a hukumance aka kuma yi musayar su, sun nuna cewar, harkar ta samar da wutar mai aiki da hasken rana ta yi gagaruwar faduwa kasa warwas a cikin ‘yan shekarun da suka shige kuma farashin aikin na samar da wutar kilowatt, dole ya kasance yadda ya dace.

Kemi ta kuma buga misalai akan irin gasar da aka shiga wajen samar da wutar kilowatt na kasar Afrika ta Kudu da Zambia da Egypt da Ethiopia aka yi a cikin lokacin da  Nijeriya ta samu nata, wanda kuma farashin yake a tsakanin biyar zuwa bakwai.

Ministan ta kara da cewa, ganin cewar a cikin wasikar akwai hadari da gwamnati ta samar a cikin takardar garanti ta  (PRGs) da kuma (PCOAs,), karin kudin wutar a kasar nan ya kamata a kalla a bisa yadda na sauran wadannan  kasashen yake, inda kuma tsadar gudar da aikin, ya kamata ya zama bai daya kamar yadda yake a fadin duniya.

Adeosun ta kuma sanar da cewar gwamnatin tarayya bazata amince da gudanar da yarjejeniyar aikin na  (PCOAs) ba da kuma wani akin, har sai idan ta gansu cewar anyi adalci akan farashin kuma sai idan aikin ana bukatar sa a kasar nan.

Da take jaddada matsayin gwamnatin tarayya Adeosun a daya daga cikin martanin ta ga hukumar (NBET), bayan da aka nada sabon Manajin Darakta na hukumar ta (NBET) Dakta  Marilyn Amobi, ta yi tambaya cewar an yi yarjejeniya akan farashin akan (PPAs) kafin ta amince da yarjejeniyar ta(PCOAs).

A saboda haka, majiyar mu ta labarto cewar kamfanoni biyu masu son zuba jari  Afrinergia Power da kuma kamfanin Cosmos, sun sabunta farashin su zuwa kashi 7.5 na kilowatt sun kuma samu amincewar Minista Adeosun a watan Disambar shekarar 2017.

A cikin wasikar data aikewa da hukumar (NBET) akan wannan maganar, Adeosun tace, “Ina son in bayar da shawara akan samar da ci gaba cewar gwamnatin tarayya zata kawai gudanar da aikin (PCOAs) na samar da wuta mai aiki da hasken rana na IPPA wanda ya cika ka’idoji guda uku na tabbatar anyi adalci da samar da farashin da ya dace mai madogara wanda zai yiwa gwamnatin tarayya daidaia akan kadarorinta.

Ta sanar da cewar cazar farashin gudanar da aiki, ba zai wuce yawan dalar Amurka 0.075 na kilowatt ba kuma tsadar gudanar da aikin, kada ya wuce dalar Amurka biliyan 1.32.

Sai dai kuma, majiyar bata samu iya iske Amobi don ya yi bayani ba akan wannan ci gaban da aka samu, duk da haka majiyar ta sanar da cewar, daukin da Minista Adeosun da Amobi, suka samar ya kare Nijeriya daga sanya hannu akan gudanar da wannan yarjejeniyar, wadda zata kai tsawon shekaru ashirin na tsawon yarjejeniyar ta (PPA).

“Akan yanayin aikin wanda aka amince da kashi 11.5 wanda Bankin Duniya ya sanar a hankali, ma’aikatar kudi baza kuma ta bayar da (PRGs) akan gudanar da ba.

A cewar majiyar, “Idan aka lura minista Adeosun taki  halartar taron sanya hannu na (PCOAs) da aka gudanar a watan  Afirilun shekarar 2107 domin kuwa, ministan ta jaddada matsayin ta na cewar, ba za ta yi mubayi’a ba akan na (PCOA) ba wanda tace bai cika sharudda ba.”

Majiyar ta yi nuni da cewar, “ Nijeriya ta tuhumanci ma’aikatar wuta da tsohon Manajin Darakta na rikon kwarya na hukumar  NBET akan yadda aka cimma matsaya akan kashi 11.5.”

A cewar majiyar, an kuma yi ikirarin cewar wasu masu zuba jari akan samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana sun sayar da lasisin su na (PPAs) ga wasu masu zuba jari don a tabbatar da fargabar ministan kudi Adeosun.

“Alal misali, daya daga cikin masu aikin na jeka nayi ka da suka samu (PPA), tuni sun sayar da lasisin su da kuma PPA ga wasu rukuni dake Dubai, inda suka yi gaba da miliyoyin daloli ba tare da sanya kayan samar da wuta mai aiki da haske rana daya ba.

“Hukumar NBET, tana iyakar kokarinta wajen daidaita wannan matsayin position ta hanyar hada karfi da karfe da ma’aikatar kudi. Majiyar a karshe tace,  kwanan baya Amobi ya kafa tawaga da Dakta  Eugene Edeoga ke jagoranta don samar da rajin farashin akan wutar lantarki mai aiki da hasken rana akan kashi hudu kafin shekarar ta kare”.


Advertisement
Click to comment

labarai