Connect with us

RAHOTANNI

Sarakunan Arewa Da Kungiyoyin Fulani Sun Dau Hanyar Samar Da Zaman Lafiya

Published

on


  • Neja Ta Ware Matsuguni Ga Makiyayan Da Aka Koro

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya himmantu wajen dakile fitintinu tsakanin makiyaya da manoma a fadin kasa, hakan ya biyo bayan neman samun zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin kasa, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi Na biyu ne ya bayyana hakan a babban taron masu ruwa da tsaki na kungiyoyin makiyaya da sarakunan gargajiya da ya gudana a minna asabar din makon da ya gabata.

Mai martaban ya cigaba da cewar mataimakin shugaban kasa ya umurci mai alfarma sarkin musulmi,  Alhaji Sa’ad Abubakar da Lamidon Adamawa, Alhaji Mustapha Barkindo da sauran sarakunan arewa da su lalubo hanyar da za a samu zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a kasar nan da sauran sassan Afrika da kowa ya mayar da takobinsa kube dan a samu zaman lafiya a cikin al’umma.

Taron wanda aka yi karkashin kungiyar Miyatti Allah Cattle Breeders Association Of Nigeria ( MACBAN) a dakin taro na Idris Legbo Kutigi da ke minna. Mai martaba, Alhaji Muhammadu Sanusi ya jawo hankali makiyaya da su zama masu hakuri, koda an tsokane su su daina saurin daukar martani cikin fushi domin fushi ba abinda yake haddasawa illa nadama.

Mai martaba, yace mataimakin shugaban kasa ke jagorantar kwamitin da maigirma shugaban kasa ya kafa dan lalubo hanyar da za a bi dan samun dai-daito tsakanin makiyaya da manoma a yankunan da ake samun tashin hankali tsakanin bangarorin biyu. Yace yawan tashin hankali da sabanin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya dadadden abu ne da ya kamata a nemo bakin walwale shi, domin muddin babu zaman lafiya tattalin arzikin kasar nan zai rika tangadi ban cin hasarar dukiya da rayuka da hakan zai ta haddasawa.

Taron dai wanda ya samu halartar manyan kungiyoyin Fulani da suka hada da Miyatti Allah Cattle Breeders Association Of Nigeria, bisa jagorancin shugabanta na kasa, Ardon Zuru, Alhaji Muhammadu Kiruwa, sai Miyatti Allah Kautal Hore Fulani Socio-Cultural Association, bisa jagorancin shugabanta na kasa, Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, da Gan-ALLAH Fulani Cultural Association, bisa jagoranci Alhaji Sale Baye.

Da yake bayani ga manema labarai, shugaban Miyatti Allah Cattle Breeders ta kasa, Ardo Muhammadu Kiruwa, cewa yayi a tarihi na kafuwar kungiyar makiyaya a kasar wannan shi ne karo na biyu na haduwa da sarakunan gargaji na Arewa kan matsalolin da makiyaya ke fusknata. Zuwansu da sakon gwamnatin tarayya na cewar duk abinda za a yi a tsaya, koda an tsokani makiyaya kar su rama domin a baiwa gwamnati hadin kai don a samu zaman lafiya.

Ardon yace daman fulani mutane ne masu son zaman lafiya domin arzikinsu a waje yake kowa na gani, don haka sun fi kowa tsoron fitina, domin in ya taso akan su yake karewa. Kafin ma gwamnati tayi wani abu mu da kan mu zamu kafa kwamiti mai karfi da za ta shiga ta wayar da kan makiyaya, su guji daukar fansa duk abinda aka yi masu su sanar da shugabanni, mu kuma sai mu isar inda ya kamata.

Shugaban ya jawo hankalin gwamnatin tarayya akan sauran sarakuna da ba fulani ba suma a kira su, dan su kafa kwamiti mai karfi musamman a bangaren Adamawa, Taraba da Benue da su daina kaiwa makiyaya fulani hari da kashe dabbobin mu da Iyalan mu, ba mu da wani sana’a da za mu yi da yafi kiwo. Wasu gwamnatocin sun fito dan hana mu sana’ar mu na kiwo musamman jihar Taraba da Benue kuma ba mu ga yadda za a tauye mana hakkin mu ba da ‘yanci na zaman mu ‘yan kasa a hana mu sana’a, don haka wadannan al’ummomin jihar Taraba da Benue suna nan zaune a ko ina a Arewa, idan an ce za a hana makiyaya yin sana’ar kiwo, tau ya za a yi da mutanen Benue da Taraba da ke zaune a sauran sassan jahohin Arewa, kodai fulani ne aka raina, wannan ya sabawa tsarin mulkin kasar nan na baiwa kowa ‘yancin watayawa da kuma tsarin zaman lafiya.

Alhaji Bello Abdullahi Bodejo na kungiyar Miyatti Allah Kautal Hore ya yabawa maigirma mataimakin shugaban kasa na bada aikin nan a inda ya dace, yace sai dai abin kashi biyu ne. Bayan hare-haren da ake kai mana a fili ana kashe mu da dukiyar mu akwai kuma na mummuke da ake mana, na kar karya arzikin fulani tare da talautar da su.

Ya kamata masu martaba sarakunan Arewa su sani, hadin kai da zaman lafiya yana tafiya ne tare da adalci. Yau kabilun Bashama da Biron suna kai mana hare-hare, sannan a hannu daya kuma shugabannin mu suna hada kai da jami’an tsaro ana tarwatsa mana dukiya, mun yi kokari akan maganar yaki da rashawa, akwai batagrin shugabannin da ke hada kai da jami’an tsaro ana talautar da makiyaya wanda ya zama wajibi wanda duk aka samu da irin wannan ma a dauki matakin da ya da ce.

Duk makiyayin da aka samu da laifi akai shi gaban alkali ayi mai hukunci kamar yadda ake wa kowa a kasar nan amma ba a rika tsorata su ana karban dukiyarsu da sunan toshiyar baki ko kashe magana ba. Hadin kan makiyaya da kungiyoyin su ya ta’allaka ne akan manufofinsu na alheri mu kan a bangaren mu muna tare da kowa amma duk wanda ya yarda da zalunci ba zamu kasance tare da shi ba.

Kowanne shugaba ya nemi sana’a kar ya dogara akan rashawa, domin dogaro da rashawa shi ke kawo barnar da ke faruwa yanzu, abin yayi yawa a buge ka can sannan kuma a nushe ka nan, maganar hakuri kan muna da hakuri matuka domin kan hakurin mu ne yasa ake cutar da mu ko yaushe.

Kamar yadda na ji gwamnatocin Arewa na gogoriyon bada masaukai ga makiyaya, ya kamata a tabbatar an yi tsarin da ya kamata, duk inda aka ware din nan ya zama an samar da tsaro kuma ya zama akwai iyaka da manoma dan kar kuma ayi gyaran ganganr azbinawa.

Alhaji Sale Baye na Gan-Allah, kuwa cewa yayi idan ana son kawo karshen wannan tashe-tashen hankulan sai an dawo da burtulla, kuma guraren kiwo da aka ware a tabbatar akwai mashayan ruwan dabbobi.

Maganar killace dabbobi wannan abu ne da zai yiwu ba, domin mu makiyaya tun asali an san mu da yawo kuma mu ne tushen komai na rayuwar, manoma suna anfana da mu, mu ma muna anfana da su. Amma masu kiraye-kirayen a killa ce makiyaya su sani mu ba ‘yan kasuwa ba ne wannan sana’ar ta kiwo abu ne da muka gada kaka da kakanni.

Don haka tunanin wasu na canja kiwo zuwa zamani ba abu ne mai yiwu wa ba, domin akwai wanda dabbobin na sa ya gaje su ne kaka da kakanni, idan bafillatani na da shanu da za ka yi masu kima na kudi akan miliyan biyu, koda milayan biyar za ka ba shi bai iya rabuwa da su. Mu kiwo a wajen gado ne, babban tashin hankali a wajen makiyayi bai wuce ka ce za ka raba shi da kiwon nan ba.

Shugabanni da sarakunan gargajiya mu fadawa kan mu gaskiya, wannan fadace-fadacen da ake yi da sunan makiyaya da manoma ba wani abu ya kawo shi ba illa siyasa, hassada da bakin cikin na tsirarun wadanda ba su son zaman lafiya a kasa. Wannan fadan kabilanci ne, fadar addini ne, maganar gaskiya ‘yan siyasa su fadawa junan gaskiya su daina siyasa jinin jama’a, makiyayi da manomi ‘yan juna ne kuma dukkansu suna anfana da juna.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, babban darakta a hukumar kula da ilimin ‘yayan makiyaya ta jihar Neja, Ardo Abdullahi Babayo, yace maigirma gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello ya himmantu wajen hada kai da makiyaya da jami’an tsaro wajen lalubo hanyar samun zaman lafiya. Yace dan samo hanyar zaman lafiya da kaucewa fadace-fadace tsakanin makiyaya da manoma da gwamnatin tarayya ta ke yi a jihar nan akwai hekta 44,000 na kasa da makiyaya 23 a jihar nan.

Yace makiyaya biyu da suka kunshi hekta 14,000 suna cikin karamar hukumar Rijau, yayin da sauran hekta 30,000 na a Kamfanin Bobi a cikin karamar hukumar Mariga ne. Yanzu haka gwamnatin jihar Neja a kashin kanta ta ware hekta 36,000 dan karban makiyayan da aka koro bisa sharadin za su yi biyayya ga ka’idodin da aka gindaya masu.

Taron dai ya samu halartar Lamidon Adamawa, Alhaji Mustapha Barkindo, da Sarkin Minna, Alhaji Umar Faruk Bahago mai masaukin baki bisa jagoranci Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu. Sauran sun hada da shugabannin kungiyar Miyatti Allah Cattle Breeders, Ardo Muhammadu Kiruwa, Da Alhaji Sale Baye shugaban Gan-ALLAH ta kasa da Lamido Bello Abdullahi Bodejo shugaban Miyatti Allah Kautal Hore ta kasa da sauran shugabanni na jahohi da shiyyoyi na dukkanin kungiyoyin, da Dakta Sale Momale, sai Dakta Aliyu Tide.

Taron dai wanda aka bukaci dukkanin kungiyoyin makiyayan da su aje bambamce-bambamcen da ke tsakanin su dan yin aiki tare, ana sa ran cikin shekarar nan za a yi a sassa hudu na kasar kafin nan da karshen shekarar nan da mu ke ciki.


Advertisement
Click to comment

labarai