Connect with us

RAHOTANNI

NURTW Ta Kebbi Ta Ayyana Goyon Baya Ga Buhari Da Bagudu

Published

on


Kungiyar NURTW ta kasa reshin jihar kebbi ta kaddamar da bukin Neman da nuna goyun bayan su ga shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma Gwamna Atiku Bagudu domin koma tsayawa takara a shekara ta 2019.

Wannan taron bukin an gudanar da shine a filin taro na Haliru Audu da ke a Birnin-kebbi a jiya.

Da yake gabatar da jawabinsa na makasudin suna gudanar da taron shugaban NURTW na jihar kebbi , Alhaji Usman Abubakar Bagudu ya bayyana cewa makasudin gudanar da taron na Kungiyar ta NURTW reshin jihar kebbi domin nuna goyun bayan su da kuma neman shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamna Abubakar Atiku Bagudu su sake tsayawa takara ta shekara ta 2019 a kasar nan.

Ya ce Kungiyar ta yanke shawarar yin hakan ne saboda irin ci gaban da aka samu a kasar nan da kuma jihar ta kebbi.

Har ilayau ya ce saboda haka sun rebuta takarda biyu, daya ga Gwamnan jihar kebbi daya kuma ga shugaban kasa domin bayyana bukatar su.

Daga nan shugaban na Kungiyar ta NURTW ta jihar kebbi ya mika sakon takardun ga uban Kungiyar na jihar watau tsohon Dan majalisar tarayya kuma yayan Gwamna Bagudu , Alhaji Bello Bagudu domin ya isar da sakon nasu.

Shi ma uban Kungiyar na NURTW ta jihar kebbi Alhaji Bello Bagudu ya tabbatarwa mambobin Kungiyar cewa wannan sako da aka bashi domin isar da shi ga shugaban kasa da kuma Gwamnan jihar kebbi tamkar su suka kai sakon.

Daga nan ya godewa jama’ar da su halarci wannan taron da kuma gwamnatin jihar kebbi kan goyun bayan da kuma taimakon da take yiwa Kungiyar direbobi a jihar ta kebbi.

Bugu da kari shima shugaban Kungiyar na kasa Alhaji Nazir Usman wanda ma’ajin Kungiyar ta kasa Alhaji Yahuza ‘Yankaba ya wakilta a wurin taron, inda ya bayyana goyun bayan su ga mulkin shugaba Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu kan irin ci gaban da suka samar a kasar nan.

Alhaji Nazir Usman ya ci gaba da cewa wannan gwamnati ta sadaukar da kanta wurin ganin cewa ta yaki cin hanci da rashawa, samar da tsaro da kuma farfado da tattalin arzikin kasar nan kai har da samar da aiki ga matasan kasa da kuma sauransu.

Kazalika ya cewa saboda hakan ne “suka ga ya dace suba mambobin jihar kebbi goyun bayan domin kaddamar da wannan taron na neman shugaba Muhammadu Buhari da kuma Gwamna Bagudu su koma tsayawa takara a zaben shekara ta 2019”.

Daga karshe ya nemi shugaban kasa da kuma Gwamnan kebbi da su amince da takardun da kungiyar ta NURTW reshin jihar ta kebbi ta rubuta zuwa ga resu kan su koma tsayawa takara a 2019, kana ya godewa jama’ar da suka halarci wannan taron. Har ilayau ya yi kira ga mambobin kungiyar na NURTW na kasar nan da a zaben shekara ta 2019 kowa ya zabi shugaban kasar Muhammadu Buhari da kuma Gwamnan Abubakar Atiku Bagudu a jihar kebbi.

A nashi jawabin, Gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana Jindadinsa da kuma godiyar su ga kungiyar NURTW ta kasa da kuma reshin jihar kebbi kan irin karramawa da mambobin kungiyar su kayi musu kan cewa su kowa tsayawa takara a shekara ta 2019, wannan ba karamar karramawa ce  ka yi.


Advertisement
Click to comment

labarai