Connect with us

NAZARI

Muryar Talaka… Batun Sauya Fasalin Kasa: Ina Aka Kwana?

Published

on


Tare da Bishir Dauda 08165270879

Idan masu bin wannan shafin za su iya tunawa a baya, na yi rubutu akan kiraye-kirayen da ‘yan kudancin kasar nan k eta yi na  dole sai an canza fasalin kasar nan, ko kuma a waste kowa yasan in da dare yai masa. Da farko da gwamnati na kallon masu irin wannan ra’ayi a matsayin ‘yan tada zaune tsaye, mutanen dake amfani da kabilanci, addini ko shiyya don biyan bukatar siyasa ko ta kashin kai. Na kawo misalai na daga masu wannan raji inda na lissafa mutane irin su marigayi Abraham Adesanya, tsohon shugaban kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, da irin su Ransome Kuti, Wole Soyinka, sai na baya-baya kamar Yinka Odumakin.

A hankali yanzu wannan kira na kara samun tagomashi. Kama daga kungiyoyin banza masu tada fitina irin MEND, NIGER DELTA ABENGERS, IPOB, OPC zuwa malaman coci-coci kamar su Mathew Hassan Kukah, dama ‘yan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda keso yai amfani da batun sauya fasalin kasa domin ya samu kuru’u daga Inyamurai da yarbawa.

Yanzu sauran sassan kudancin  Nijeriya kamar kudu maso yamma da kudu maso gabas da kudu maso kudu da jihohin Middle Belt musamman Binuwai da Kiristocin Arewa  sun hade ma Arewa ta yamma da ta gabas da Musulmi baki inda suke nuna goyon baya ga kiraye-kirayen su Afenifere.

A da muna ganin masu irin wannan ra’ayi, a matsayin  masu yima kasa zagon kasa. Domin ai abin da suke so shi ne a kawo karshen hadin kan kasar nan; a raba kasar zuwa shiyyoyi shidda (6) masu karfi fiye da gwamnatin tsakiya. Wannan shi suke kira da turanci merger of states. Yayinda suke so a baiwa kowace shiyya mai kumshe da kabila iri daya damar mallake duk harajin dake shigowa a jihar ta ciki hard a BAT, da mallake ikon mallakar albarkatun kasa bakidaya ciki hard a fetur. Gefe guda za a mayar da gwamnatin tsakiya  ‘yar Rabbana ka wadata mu inda za a dinga ‘yan mata wani abu daga cikin kason da kowace shiyya ke samu. Wannan tsari  na rage ikon gwamnatin tarayya shi ne ake kira da turanci Debolution of power. To amma yanzu fa kida ya sauya domin gwamnatin APC ta dauko hanyar biya bukatun masu irin wannan kiraye-kiraye, domin a kwanaki na gaya maku kwamitin da jam’iyyar ta kafa karkashin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I wanda za gaya fadin kasar nan, inda ya saurari ra’ayin ‘Yan Nijeriya game da batutuwa da dama da suka shafi sauya fasalin kasa, kuma wannan kwamiti ma har ya kamala aikinsa ya gabatar da rahotansa ga uwar Jam’iyyar.

Kwamitin dai ya amince da batun rage ma gwamnatin tarayya karfi; da cire kananan hukumomi daga tsarin Nijeriya, da hade jihohi, da kirkiro ‘yan sandan jihohi da sauran su.

Rahotan kwamitin abin takaici ne, abin Allah wadarai ne, domin rahoton bai wakiltar ra’ayin mafi rinjayen ‘yan Nijeriya. Domin babu wani dan Nijeriya na kirki mai tunani da hangen nesa da zai goyi bayan a soke kananan hukumomi. Batun a soke kananan hukumomi, ya fi kama da ra’ayin shugaban kwamitin wato gwamnan jihar Kaduna Nasiru wanda tun hawan sa bias kujera bai boye manufarsa ta kyamar kananan hukumomi ta hanyar korar ma’aikata da kuma mallaman firamare daga bakin aikinsu da sunan gyara. Don haka babu mamaki don kwamitin ya bada shawarar soke kananan hukumomi daga kundin tsarin mulki ba. Ta yaya ‘yan Nijeriya da tunaninsu da hankalinsu za su taba goyon bayan ci baya? Mu tuna an kirkiro kananan hukumomi ne domin akai gwamnati kusa da  jama’a, a samar da ci gaba ga talakawa  da tsaro da aikin wayar da kai  amma kawai sai a wayi gari a ce wasu ‘yan jari hujja sun kawo karshen su?

In dai domin cin hanci za a bada shawarar soke kananan hukum omi, to ba a cin hanci a tarayya da jihohi? Biliyan Nawa Maina ya gano an sace ma ‘yan fansho a matakin tarayya? Nawa ake sacewa a NNPC, CBN,FIRS,NIA da sauran su kowace rana a Nijeriya?

Sannan nawa ake sama da fadi das u a jihohi da sunan ayyukan raya kasa? Shi kansa gwamna El-Rufa’I, kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara ya taba kalubalantarsa day a fadi yadda yake kashe kudaden karta kwana (SECURITY BOTE) a jiharsa amma yai kwana.Saboda sokewa ko rusawa bas hi ne mafita ba, kamar yadda kwamitin ya nuna. Idan akwai niyyar a gyara al’amurran kananan hukumomi ba tare da an kori kowa daga aikinsa ba, koma an rusa ba, za a iya, domin a kasar an sha gudanar da bincike iri-iri kan yadda za a gyara kananan hukumomi. Sakamakon binciken na nan amma ba ai komi akan shi ba, sai yanzu wani ko wasu dake cikin mayen giyar mulki za su bada shawarar soke kananan hukumomi. Wannan fa rashin mutunci mane.

Kwamitin ya amince da kirkiro ‘yan sandan jihohi. E, lalle kasar Amerika da muke koyi da ita, tana da ‘yan sandan jihohi da kuma na FBI. To amma fa ba dole bane abin da yai aiki a Amerika ya yi a Nijeriya.Abubuwa da yawa da muka kwafo daga kundin tsarin mulkin Amerika yanzu basu aiki a Nijeriya. Kazalika, masana da kwararru da dama sun nuna illar ‘yan sandan jihohi a kasar da har yanzu babu yancin bil’adama. Kasar da za a iya tura sojoji suje su tada gari guda kamar yadda muka gani zamanin Obasanjo a Zaki-Biyam da Odi, kuma kasar da hatta ‘yan sandan tarayyar kan goyi bayan kabila ko addininsu lokacin rikicin addini kamar yadda muka  gani a rikicin Zangon-kataf, Kafanchan da Plateau dama Shagamu inda aka nemi jami’an tsaron aka rasa lokacin rikicin 1999.

Kasar da gwamna  kan iya ba kwamishinan ‘yan sanda ummarni a daure abokin hamayyar siyasa ko wani wanda ra’ayi ya saba, a irin wannan kasa ka sake kai ‘yan sandan jihohi to talaka baida sauran sukuni. Muguntar da ‘yan doka sukai a janhoriya ta daya zai zama tamkar wasa. Domin yanzu kasar mugunta ta karu, rashin tausai da zalunci sun karu, sannan babu tarbiyya kamar da, don haka sai dai in dama wani mulkin zalunci ake son sake shinfidawa a kasar banga dalilin da zai sa wani  ya goyi bayan kafa ‘yansanda jihohi.

Saboda haka, aikin da El-Rufa’I yai mu mutanen Arewa, ba mu karbe shi ba, kuma muna kira da dukkanin wakilanmu dake majalisar dokoki da kada su sake su karbi wannan shawarar kwamitin domin bai wakilci ra’ayinmu ba.

Duk yan kishin Arewa dole mu fito mu yaki wannan rahoto mu tabbatar bai rayu ba, inko ba to za mu koma bayi a kasarmu ta haihuwa, kana ‘ya’ya da jikoki za sui Allah wadarai da abin kunyar da muka bar mas.


labarai