Connect with us

RAHOTANNI

Matasa Sun Fara Zuba Sinadarin ‘Methylated Spirit’ A Lemun Koka-kola Don Su Bugu

Published

on


A lokacin da Olamide, wani dalibi mai karantar ilimin kimiyya, ya bayyana da sakamakon bincikensa a farkon wannan shekarar, ya sha suka kala-kala, a kan cewa wai yana son kara nu na wata hanya ce kawai ga matasan kasarnan na shan abin da ke sa maye.

Amma a na shi kariyan da kuma na wadanda suke goyon bayansa, ya yi kokarin ya nu na yadda matsalar take ne kawai, ya kuma nu na hanyar da wadanda alhakin abin ke kansu ya kamata su bi wajen kare rayukan mutane.

Yanzun yadda hotunan wannan muguwar dabi’ar ta jirkita lemun kwalba na Koka Kola da shi wannan sinadarin na ‘methylated ‘ suka soma bayyana, ya sanya mutane sun fara fahimtar Olamide a kan gaskiyar maganan sa.

Yanzun a bayyane take, matasanmu suna jirkita wadannan ababen biyu, da nufin samar da wani abin sha mai dandano a gare su wanda zai iya sanya su cikin maye.

Duk da kasantuwar ya zuwa yanzun ba su baiwa wannan abin wani suna ba, amma dai lamarin yana nan yana ta habaka a tsakanin matasan tamkar wutar jeji.

A ‘yan watannin nan dai, yawaitan shaye-shayen ababen da ke sa mayen, yana ta kara jawo hankulan al’umma. Matasa daga dukkanin sassan kasarnan, sai kara tsunduma a cikin harkar ta shaye-shaye suke yi, da nufin wai su yaki halin kunci da damuwar da suke ciki.

Wannan masifar ta shaye-shaye dai a yanzun ta zama ruwan dare a tsakanin matasan, kama daga birnin Lagas kawo cikin lungunan da ke cikin birnin Kano, duk matasa ne maza da mata ‘yan maye, inda ma har ta kai ga kwalbar maganin tarin nan ta Codeine, farashin ta ya zama daya da farashin kwanon abinci mai dadin da mutum zai ci ya koshi.

Wannan sabuwar hanyar bugar da kan da matasan suka kirkirowa kawukansu, ta fi kowacce damuwa da kuma ban tsoro, domin kuwa ba ta yadda mutum zai iya yin wani bayani a kanta.

Shi dai wannan sinadari na, ‘Methylated,’ tsantsan giya ne, wanda kuma an tanade shi ne kadai domin hada wasu magunguna da shi, amma sam bai da ce da a sha shi ba.

Shi ma maganin tari na Codeine, matasa maza da mata masu yawa suna kwankwadarsa a bisa wata manufa ta daban da manufar da aka yi shi, musamman a wannan yankin na Arewacin kasarnan.

Wannan masifa ce babba, wacce za a iya cewa, annoba ce da ta fi kowacce hadari wacce kuma ke ta kara ruruwa a tsakanin matasan kasarnan.

Akwai matukar bukatar cibiyoyi da makarantu su saka wasu darussa a cikin darussan da suke koyawa dalibansu, wadanda za su nu na masu hadarin yin tu’ammali da ababen sa mayen.

Su ma malamai da limamai na addinanmu, ya wajaba su karfafa yin gargadi a cikin hudubobinsu da kuma nu na wa al’umma mummunan makomar duk mai yin tu’ammuli da kayan maye, wanda karshen makomarsa ita ce wutar jahannama.

Mu fa sani a yanzun haka muna kara kusantar wata babbar annoba ce, wacce ba wata-wata karshenta halaka ne, matukar muka yi kunnen uwar shegu da ita, shikenan mun rasa matasanmu da muke alfahari da su, wanda hakan kuma yana nu na karshenmu ne bakidaya.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai