Connect with us

LABARAI

Kwamitin Gwamnatin Jihar Katsina Kan Fetur Ya Fara Aiki

Published

on


Kwamitin aiki da cikawa akan samarwa da rarraba albarkatun man fetur na jihar Katsina ya gudanar da wani taro da manyan dillalan man fetur a shiyyar Daura.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin na jiha, Alhaji Muhammad Lawal Aliyu ya bayyana cewa rahotannin da suke zoma kwamitin sun nuna cewa dillalan man fetur din suna saida shi fiye da farashin da gwamnati ta amince da shi.

Ya yi nuni da cewa wasu gidajen mai suna boye man fetur din domin san kan su da kansu.

Ya bayyana cewa wani rahoto ya nuna cewa masu hawa motoci da sauran al’ummar shiyyar Daura suna fama da matsalar rayuwa da wahalhalu a sanadiyyarkarancin man fetur din.

Shugaban kwamitin ya shedawa taron cewa sun je yankin ne domin a tattauna hanyoyin da za a bi domin kawo karshen matsalar.

Alhaji Lawal Aliyu yayi kira ga ya bayyana cewa kamfanin samar da man fetur na kasa ya sha alwashin samar da wani kaso na musamman na albarkatun man fetur ga jihar Katsina.

Don haka ya roki dillalan man fetur din wadanda suke sha’awa da su gabatar da sunayensu ga kwamitin.

Shi ma da yake jawabi, wani memba na kwamitin Comrade Sa’idu Magaji Karkarku ya sanar da dillalan man fetur din cewa wasu mutane suna cewa su membobin kwamitin suna amsar kudade a gidajen mai.

Ya gargade su ga me da kara farashin man fetur din wanda kamar yadda yace ba za a yarda da hakan ba.

A jawabansu na daban-daban wasu dillalan man fetur din sun yi korafin cewa sun sawo man ne da kansu.

Wani Alhaji Danlami Tela Ada Daura ya bayyana cewa ba a sa rai su saida man fetur din kasa da farashin da suka sawo shi.

Shima da ya ke jawabi Alhaji Ashiru Mai Kwai yayi kira ga gwamnatin da ya saurari matsalolin su.

Dangane da dukkan matsalolin da dillalan man fetur din suka gabata shugaban kwamitin Alhaji Lawal Aliyu tare da sauran membobin sun yanke shawarar daukar matakai na tabbatar da ganin cewa man fetur ya wadata a Daura da kewayenta.


Advertisement
Click to comment

labarai