Connect with us

LABARAI

Katsina Da Chana Za Su Yi Hadin Gwiwa

Published

on


Gwamnatin jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin kasar China da ta duba yiwuwar rage wahalhalun da yan ksuwa ke fuskanta wajen samun Bisa domin tafiya kasar China.

Gwamna Aminu Bello Masari yayi kiran a lokacin da ya amshui bakuncin jakadan kasar China a Nijeriya Dr. Shon Phinghian da ya kai ziyara a gidan gwamnati dake nan Katsina.

Kamar yadda gwamnan yace, yan kasuwa na fuskantar wahalhalu da dama wajen samun Bisa domin domin zuwa kasar Chuina don gudanar da harkoki na kasuwanci.

Gwamnan ya bayyana cewa kasar China na taka muhimmiyar rawa wajen kawo cigaba ga kasashen da suka ci gaba, musamman ta hanyar kere-kere da kasuwanci.

Yayi kira ga jakadan kasar China da ya kara daukaka dangantaka tsakanin kasarsa da jihohin dake kasar nan ta bangaren sufuri musamman ta fuskar sufurin jirigin kasa.

Gwamnan yace hakan zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin al’umma da kuma taimakawa gwamnatin jihar Katsina ta hanyar bunkasa tattalin arziki.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa za a bunkasa samar da kudaden da ake wajen jawo hankalin masu zuba hannun jari.

Ya yi nuni da cewa, cikin shekaru talatin kasar China ta zama abin kwatance saboda kyakkyawan shugabanci.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa naira miliyan goma da jakadan kasar China ya bada za a yi amfani dasu wajen bunkasa sha’anin kiwon lafiya a jihar nan.

Tun da farko, jakadan kasar China a Nijeriya yace ya zo jihar nan ne domin samun kyakkyawan hadin kai da gwamnatin jihar Katsina ta fuskar noman rani, samar da ruwa, bunkasa ababen mo re rayuwa da makamantansu.

Haka kuma, yace yana bukatar kula da wata yarjejeniya da ta shafi kayayyakin gona domin fitar dasu.

Jakadan ya bayyana bada tallafin naira miliyan goma ga jihar domin bunkasa bangaren kiwon lafiya


Advertisement
Click to comment

labarai