Connect with us

RAHOTANNI

Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Buhari Ya Ajiye Kujerar Ministan Albarkatun Man Fetur

Published

on


Jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya, ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya ajiye hade da barin kujerar babban Ministan albarkatun danyen mai ta Nijeriya la’akari da rikitar-rikita da kuma tsananin wahalar mai da ke faman jama’an kasar a kowani yankin kasar. Jam’iyyar ta shaida hakan ne a cikin wata sanarwar da suka raba wa manema labaru a jiya Lahadi dauke da sanya hanun babban sakataren watsa labaru na jam’iyyar Kola Ologbondiyan a birnin tarayya Abuja, ya ce kwata-kwata Buhari ya fadi warwas ta fuskacin shawo kan matsalolin da suke jibge a bangaren sha’anin mai da kuma gazawa wajen shawo kan rikicin da ke tattare da wannan janibin ta sha’anin mai a Nijeriya.

Jam’iyyar adawar ta shaida cewar abun daya tilau kuma da ya dace shine shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ajiye wannan mukamin nasa na babban ministan albarkatun mai ya mika ga wani nagartaccen mutum wadda zai iya fuskantar matsalolin da suke jibge domin samar wa ‘yan Nijeriya saukin rayuwa da kuma inganta tattalin arzikin a fadin kasar. “Yanzu haka da muke magana, tattalin arzikin Nijeriya ya yi kasa a cikin wattani biyu da suka gabata biyo bayan hatsaniyar da sha’anin man fetur ke ciki, sana’o’i da daman gaske sun samu nakasu, farashin kayyaki dukkaninsu sun yi tashin gwaron zabi fiye da yadda kake tsammani, don haka dole ne a hanzarta fuskantar sha’anin tattalin arziki”.

“Muna kira ga shugaban Nijeriya Buhari da ya gaggauta cire kansa da kuma ajiye mukamin nan daga ma’aikata mai dumbin muhimmanci wato sashin albarkatun dan fetur, hade da samar da mutumin da ke zai iya yi wa jama’a aiki da suka dace a dan sauran watannin da suka rage masa”Jam’iyyar ta yi bayanin cewar kin ajiye wannan mukamin da Buhari zai yi hakan zai iya kawo koma baya wa sha’anin tattalin arziki a fadin Nijeriya domin a cewar PDP akwai tulin matsalolin da suka dace Buhari ya maida hankulansu a kai, sun yi amannan cewar hakan ne ma ya janyo Buharin ya gaza kasau wajen kokarin tafiyar da sha’anin ma’aikatar albarkatun man fetur yadda suka dace a fadin Nijeriya, don haka ne suka shawarcesa da tsaida mukaminsa na Ministan mai gami da lalubo wani jajirtaccen da zai yi aiki tukuru wa kasar nan. PDP ta bayyana cewar hakan ne kawai zai iya kaiwa ga a samun shawo kan matsaloli da kuma rikicin da suke shakare jibge a sha’anin mai da kuma samar da hanyoyin shawo kan matsalolin karancin mai da ke addabar ‘yan Nijeriya a halin yanzu.


Advertisement
Click to comment

labarai