Connect with us

SIYASA

Hada Aikin Jarida Da Siyasa Na Bukatar Goge Wa (I) – Habila

Published

on

ILIYA HABILA Shi ne mai tallafa wa Kakakin Majalisar tarayyar Nijeriya na musamman akan yada labarai da hulda da ’yan jarida. A wannan hirar ta musamman wacce yayi da LEADERSHIP A YAU ya yi dogon jawabi kan yadda aikin jarida ke da matukar bukatar ta-ka-tsantsan a lokacin da mutum ke hada aikin jarida da kuma hidimar siyasa. Habila ya yi amfani da wannan damar ya bayyana yadda dan jarida zai kauce wa shiga hidimar da bata shafi aikin sa ba; tattare kuma da bai shiga ya dagula aikin kare mai gidansa ko kuma wanda yake aiki a karkashin nasa ba. KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi, Ga hirar kamar haka

Da wa mu ke tare a halin yanzu?

Sunana Iliya Habila, an haifeni a ranar 31 ga watan sha biyu, alif 1967 yau ina da shekaru 50 a duniya, an haifeni ne a garin Lafiyan-Sara ko ka ce Kwara da ke karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi. Na shiga firamare a alif 1976 a L.E.A a Lafiyan-Sara, mun zana jarabawa mu 20 a St John Bianney’s Seminary (S.J.B.S) da ke Barikin Ladi, Jihar Filato a shekara ta 1981. A cikin mu ashirin din nan ni kadai na samu tafiya makarantan gaba da firamare a Barikin Ladi a ranar 14/9/1981 na kai har aji uku daga bisani kuma na nemi canji zuwa Teachers College Kangere, mun fara aka tun a zangon farko a zo aka maida kowa karamar hukumarsa, a bisa haka ne na dawo karatuna Teachers College Bogoro (Yanzu an canza wa makarantar suna zuwa G.S.S Bogoro) na kuma daura ne daga fom 3, na kammala makarantar a 1987. Daga bisani kuma na zo na dan yi aikin koyarwa a karamar hukumata na dan wani lokaci, daga bisani na samu izinin shiga jami’ar Maiduguri a 1988, na fara jami’ar da karatun share fage, da Allah ya sa na ci sai na zama cikakken dalibi a fanni koyon aikin jarida wato ‘Mass Communication’ daga 1989-1994 inda na samu shaidar digiri a wannan sashin da sakamako mai kyau. Bayan nan kuma na je na yi wa kasa hidima a jahar Kebbi na koyar ne a kwalejin birnin Kebbi, (Kebbi State Polytechnic) a haka kuma ina dan aiki a wasu jaridu a lokacin. Bayan da na kammala bautar kasa, na dawo gida a 1995 na zo na fara aikin jarida a gidan telebishin na jihar Bauchi wato BATB amma ba a matsayin cikakken ma’aikaci ba; ina amsar albashin naira 250. Ina cikin haka na zo na samu aiki a gidan telebishin a jihar Kaduna DITB daga 1995 zuwa 1997. A wannan shekarar ta 3/2/1997 ne kuma na samu aiki da kamfanin dillacin labarai ta Nijeriya wato NAN. Karin farko NAN ta tura ni aikin a Yola inda na yi shekaru biyar 5 cur, daga bisani NAN suka yi min canjin wajen aiki zuwa jahar Taraba inda na shafe shekaru 6 ina aiki a wannan jahar, daga nan kuma aka dawo da ni jihata ta asali wato Bauchi inda na shafe shekaru 4 ina fafatawa a aikin jarida. Sannan kuma an kaini aiki jihar Gombe nan ma na yi shekara 4. Yanzu kuma haka na samu aiki a ofishin Kakakin Majalisar Tarayya, Honarabul Yakubu Dogara inda a halin yanzu na ke aiki a matsayin mai tallafa masa na musamman kan harkokin watsa labarai da hulda da ‘yan jarida. Na bar wajen aikina wato NAN zuwa wani lokaci a matsayin wanda ya dan bar aiki zuwa na wani lokaci (secondment), bawai na bar NAN ko na yi ritaya bane, a yanzu haka ma ina matsayin Mataimakin Babban Edita (Assistant Editor-In-Chief) a nan kamfanin Dillancin Labarai, wto NAN. Ka ji takaitaccen tarihina.

Ko ka taba rike wani mukami a aikin jarida?

A lokacin da na je jihar Adamawa aiki, na rike mukamin sakataren kungiyar wakilan kafafen sadarwa (Correspondents Chapel) daga 1997-1999, daga wannan shekarar kuma aka yi zaben jihar gabaki daya na nemi kujeran sakatare kuma na ci, shekara daya da wasu watannin aka yi min canjin wajen aiki zuwa Taraba a wannan garin ban nemi wani matsayi ba, sai da na zo Bauchi na nemi zama shugaban kungiyar wakilan kafafen sadarwa na jihar Bauchi kuma cikin yardar Allah na ci daga shekara ta 2008 zuwa 2011. Ni na kasance shugaban Chapel na Bauchi. Bayan nan kuma na rike wasu mukamai na kwamitoci daban-daban a aikin jarida.

Ko ta yaya Iliya Habila ya tsinci kansa a wannan sana’ar ta jaridanci?

Gaskiya ni tun ina karami ina sha’awar sauraron rediyo sannan kuma ni mai sha’awar karance-karance da rubuce-rubuce ne, ko takarda na gani a kasa zan dauka na karanta. Sannan yanayin makarantun da na je sun sake sanya ni na samu kwarin guiwar kasancewa na dan jarida. domin ni tun da na so kasancewa a bangaren kimiyya ne, aka zo aka kai ni kwaleji sashin koyarwa ba da son raina ba; sai na ce kila malanta zan yi, da na zo tafiya jami’a sai kuma na nemi aikin jarida tun da daman can ina sha’awa. Tun da na fara karatuna a wannan sashin sai ya kasance duk wani bangare na koyon sana’a ko gwajin aiki duk ina yi ne a fannin aikin jarida, TB, rediyo jarida dukka dai. Wannan dalilin ya sa na zunduma cikin aikin na jarida. Sannan na fahimci aikin jarida idan kana son ka bauta wa Allah ka kuma bauta wa jama’a ka taimakesu ne to lallai ka rungumi aikin jarida, na sake nazari domin aiki ne gabaki daya da ya kasance

aikin taimako, aiki ne wanda zaka kawo wa al’ummarka ci gaba, ba aiki ne wanda za ka tara kudi nan take ba, a bisa haka na kasance a wannan sana’ar har zuwa yau.

Sau-tari aikin jarida aiki ne mai hatsarin gaske, ko ka taba tsintar kanka a cikin wani hatsari a yayin da kake kan aikin nan na jarida, walau ko ka yi wani rahoto a kan wani ko wasu da ya dawo hayaniya?

Bar na fada maka ka, rubutu akan wani ya tada hankali sam wannan bai ma daga cikin koyarwar aikin jarida. Bayanai kashi biyu ne wasu suna yin rubutun su a kan gaskiya ne sai kuma ya tayar da hankalin jama’a, wasu kuma za su fadi karya ne na son zuciya ko son wani abu. Hakan ne zai sa ka ji ana cewa dole ka zo karyata kanka da kanka. A rayuwata ta aikin jarida ban taba yin wani aiki ko rubutun da ya tada hankalin jama’a ba, ba wai don na kasa a aikin jarida ba, illa dai kawai sai don koyarwar kamfanina na Kamfanin Dillancin Labarai ta Nijeriya NAN. Mu kamfaninmu ta NAN ba su yarda ka ce ka ji wannan labarin daga wata majiya ba, ba tare da bayyana sunan wanda ka ji wannan labarin daga garesa ba, mu muna da wani koyarwa a jikinmu wanda dole ne ka tabbatar da ina ne majiyar da labarinka ya fito, sabili da a karshe idan labari ya fito ofishinka ba su bukatar zaunawa suna neman wani hujjar cewar sun baka horo, ko su jama’a su ce wannan dan-jaridar yana sharara karya a cikin rubutunsa. Ni a gaskiya a maimakon ce maka na taba yin rahoton da mutane suka ji ba dadi sai na ce maka sai dai rahotonin da jama’a suka ji dadinsu. Domin a wannan aikin inda ba baka taba tsammanin zan je ba, to na je shi. Idan ka taba jin KOMA a karamar hukumar Jada a jahar Adamawa, a shekara ta 1997 lokacin da na fara aiki da NAN na je na yi kwanaki biyar a wajen. Shi garin KOMA a lokacin ko na ce har yanzu ma akwai wasu mutane ‘yan adam suna rayuwarsu tsirara suke yi komai, tafiya tsirara, suna rayuwa ne a kan duwatsu. Ni na je wannan kauyen na yi rayuwa da su na fito na bayar da labari kar har ma abun da ake ce masa  Nazari/Sharhi mai tsawo feji guda dukka a kansu na yi. Wannan labarin ya zamo min abun alfahari domin ba kowani dan jarida ne zai je can ba, domin wasu ‘yan jaridan sun fi damuwa da su je aiki inda za su samu duniya ba inda zasu kawo wa jama’a abubuwan da zasu ji labarin da basu sani ba ko suke neman ji basu da yanda zasu yi zuwa gare shi. Idan kana son ka yi aikin da jama’a za su ji dadin aiyukanka irin wadannan wuraren ne zaka je ka nemo labarai, shi irin wannan labaran muna kiransu (Labaran da zasu taimaka wa mutane ko suke nemansu) wannan rahoton har yanzu ina jin dadinsa kuma ina tune da shi. Sai kuma wani zuwana kasar Ethiopia, a lokacin da na je Ethiopia nine kadai aka bani dama aka ce na je na kawo labarai wa News Agency of Nigerian, na je can kasar na kawo hotuna, labarai na kuma aiko da sautin murya da kuma bidiyo mai motsi, irin wadannan damar ba a ma fara baiwa mutum dama ko a turasa irin wannan aikin matukar ba’a gama amincewa da kwarewarsa akan aikin jarida ba. Irin wadannan aiyukan da na yi suna da dama kuma na ji dadin yinsu a aikin jarida.

Ta fuskacin nemo labarai baka taba fuskanta barazana, firgici ko wani abu na tashin hankali ya sameka a lokacin da kake farauto labarai ba?

Hum! Irin wadannan ai sau dayawa an samesu a aikinmu irin wannan kullum ne matukar kana aikin jarida. Lokacin da na ke aiki a DITB Kaduna, ita Kaduna a lokacin kullum a cikin rikici take, muna aiki wasu lokutan rikici zai tashi cikin dare, muna da na’urar daukan hoto (camera) duk inda ka shiga kowa ya san me kake son yi ko ka ke nema, ya gano me ka zo yi. Wani ba wai kawai zai bika bane, zai ma zo ne ya rungumeka da bala’i, a irin wannan lokacin na samu firgici a aikin jarida. Bayan wannan, da yake ni na fara aikin jarida a zamanin soja ne, akwai barazanar da muka yi ta fuskanta sosai akan rubuce-rubuce ta kaina ko ta abokan aikina a lokacin, na sha zuwa ina maganar yanda zan yi belin ‘yan uwanmu a hanun jami’an tsaro na soja ko na dan sanda, dukka wannan mun fuskanta. Barazanar da na fuskanta a kwana-kwanan nan shi ne lokacin da aka zo zabe na 2015 mun fita aikin nemo labarai a jihar Gombe aka zo aka farfasa mana mota aka yi mana raunika, ni kaina na ji raunuka a jikina. Dalilin wannan tsautsayi kawai don wai ana kamfen, suna kan yin kamfen, sai ga motarmu ta zo wucewa da suka tabbatar dukka ‘yan jarida ne a ciki kawai suka nufumu da ruwan duwatsu suka yi ta jifanmu kawai, a galla mu biyar a cikin motar nan kowa sai da ya ji raunuka sauran kuma Allah ya kiyayesu. Gaskiya irin wadannan barazanar da kuma firgici a wannan aikin koda kai wane ne dole ka fuskance shi. Wasu lokutan ma fa ba wai sai ka yi ma wasu wani laifi ko wani abu ba. daga wani ya ganka sai ya ji haushinka meye dalilin kawai don kai dan jarida ne, wani kuma kila ko don shi yana bangaren gwamnati, wala-alla ka yi labarin da bai yi wa gwamnati dadi ba, wani lokacin kuma suke zargin meye sa kake nemo labarai akan gwamnati, ko kuma suke ganin kana adawa da gwamnatin ko da su, wala-alla suka Khalid yana bangaren gwamnati yana ci yana sha tare da su, a nan kuma talakawa za su ce ka je ka hada kai da gwamnati ko zaku tauye musu hakkinsu a fagen labari. To gani dukka biyu dai sai a hankali, shi dan jarida yana tsaka-tsakiya ne, domin idan ka biye wa talakawa gwamnati sai ta sa maka karan tsana ta ce ko kana yi mata zagon kasa ne, idan kuma ka yawaita kawo labarai gwamnati, su kuma talakawa su ce kana maula ko ka koma jikin gwamnati. To ka a irin wadannan ma dukka barazana ne a fagen aikin jarida, barazana ba wai sai an zo gidanka ana cewa za a kashe ka ko wani abun na daban ba. aikin dai sadaukarwa ne.

Ka yi mana bayanin cewar kuna samun horo sosai a ma’aikatarku ta NAN, Shin kana nufin idan mutum ya bi doka da tsarin aikin jarida ba zai yawaita fadawa hadura a aikin na jarida ba?

Eh ba za a ce ba za samu matsala dukka-dukka ba; shi aikin jarida, aiki ne da ko ka yi gaskiya za ka iya fadawa cikin matsala, idan baka yi gaskiyar ma za ka iya samun matsala a yayin aikin naka, amma fa idan har dan-jarida ya kasance mai bin horon da aka yi masa, kuma yana aiki da shi ta hanyar aikinsa a aikace to tabbas shiga matsala, hatsari, firgici zai ragu sosai. Idan ka fadi gaskiya ko an bika ka san gaskiyarka ka fadi, matsalar ita ce wasu sun shigo aikin jarida ne ba tare da sanin ka’idojin aikin ba; musamman idan ka samo labari akan mutum meye kamata ka yi? Ka nemesa ka ji bangarensa, amma wasu sai su boye gaskiyar da cewar sun neme bangarensa ba a samu ba. kiwa ne ke jawo irin wadannan halayen a aikin, mutum na son yana kwance a kan katifarsa yana ba da labari da nemosa ba tare da ya fita nemo wa ba. wannan bai dace ba. abun da na ke son na fadi maka a nan, idan aka samu horo sosai wa ‘yan jarida da kuma amfani da kwarewar to wannan matsalar da kake magana a kai gaskiya zata ragu. Domin idan ka samu kwarewa ka san hanyoyin da zaka bunkasa aikinka ta yanda wanda ka yi labari akansa duk da ba zai ji dadi ba. kada ka damuwa wai wanda ka yi masa aikin sai ya nuna godiyarsa, duk abun da zaka yi a aikin jarida wasu zasu ji dadi wasu kuma ba za su dadinsa ba, idan ka yi gaskiya shi ne zai taimakeka wajen kowani fanni su ke jin dadin labaranka.

Za mu ci gaba gobe…

Advertisement
Click to comment

labarai