Connect with us

RAHOTANNI

An Gudanar Da Taro A Kan Dimokradiyya Da Kare Hakkin Dan Adam A Nijeriya

Published

on


Wata kungiya mai zaman kanta mai suna “Initiatibe for Conciliation and Right Protection” ta shirya taro na musamman domin yin nazari a kan yadda ake gudanar da harkokin dimokradiyya da kuma yadda ake gabatar da kare hakkokin ‘yan Nijeriya a fadin tarayyar kasar na, taron dai ya gudana ne a babban dakin taro na Jami’ar Legas.

Manyan baki da suka hada da malaman Jami’a da shuwagabannin kungiyoyi yan jarida da shuwagabannin dalibai na jami’o’in kasar nan suka sami halartar babban taro domin yi nazari kan yadda kasar nan ke tafiyar da tsarin dimokradiyya da kare hakkin ‘yan kasa.

Wadanda suka yi jawabi sun wajen taron sun hada da tsohon dan takarar gwamnan jihar Lagos a shekarar 2015 wato Mista Babatunde Olalere Gbadamosi (BOG) da  Dakta Achuke Chude Wanda ya na daga cikin masu jagorantar wata kungiya mai zaman kanta “Joint Action Front” ta Nijeriya (JAF) sai kuma Mista Segun Awosanya na kungiyar “Unibersal Institutional Reform Adbocate”, da kuma Prince Adelaja Adeoye.

Sauran wadanda suka samun halarta sun hada da Farfesa Isa Hasan na jami’ar Ahmadu Bello wanda Barrister Geofery NetoChuku ya wakilta, sai kuma Dakta Dan Ekere wanda shima ya turo wakili.

Cikin wadanda suka albarkaci taron akwai shugaban Hausawa mazauna Lagos. Taron ya bada karfi ne a kan yanda rayukan alumma suke ta salwanta a kasan da ake ikirarin ana tafiyar da mulkin “Dimokradiyya”.

Har wa yau dukkanin masu jawabin sun nuna rashin yardansu a kan zaluntar da gamnatin kasar nan ta ke yiwa wasu fitattatun ‘yan Nijeriya ta hanyar kin bin umarnin kotu musamman shugaban kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Nijeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky da Kwanal sambo

Dasuki da sauran ‘yan Nijeriya dake fuskantar musgunawa iriir a fadin tarayyar kasar nan.

Sannan kuma sun yi tsokaci mai tsawo a kan mulkin kama karya da wasu tsiraru suke yi a kan miliyoyin alumman Nijeriya. A nasa jawabin Mista Shegun Awosanya, ya bada karfi ne a kan zalunci da ke gudana a wurare daban-daban da kuma hanyoyin da yakamata abi domin samun zaman lafiya da gujewa fadawa tarkon mayaudaran ‘yan siyasa.

Ya kawo nazarce nazarce daban daban a kan yadda kasa ya kamata ace ta kasance da kuma yadda ake tafiyar da alamura. Shiko Shugaban Hausawa mazauna Legas wanda suka nuna farin cikin su da wannan taro da aka shirya da kuma kira da a gaggauta sakin duk wani

wadanda aka zalunta da kuma biyansu hakkinsu.

Ya kira da alumma da su hadakai domin samun ci gaba da Zaman lafiya. Bayan anyi tambayoyi ne an bayar da amsoshi, sai Kwamred Ahmad Isa Shuaib ya rufe taron da jawabai a kan abin da ya haukan alumma domin ganin an dai na zalunci da kuma tsayuwa kan gaskiya. Ya yi tsokaci a kan kashe alumma a jihohin Binuwai da Zamfara da Taraba da sauran sassan kasannan daban daban, ko dai da sunan Fulani ko Boko Haram ko kuma masu tada kayar baya.

Sa’annan ya yi kakkausar suka a kan yanda jami’an tsaro na Nijeriya ke kisan mutanen da ya kamata ace suna tsarewa. Initiatibe for Conciliation and Right Protection ne ta dauki nauyin taro din.

 


Advertisement
Click to comment

labarai