Connect with us

MANYAN LABARAI

Ganduje Da Kwankwaso: Wa Ya Fi Cin Gajiyar Wani?

Published

on


A dokance dai za a iya cewa, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ne ya fi cin gajiyar tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, amma a siyasance kuma za a iya ganin cewa, shi Kwankwason ne ya fi cin moriyar Ganduje. Tabbas wannan ikirari ne mai wuyar karbuwa ko fahimta ga mabiyan siyasa da dama ko da a jihar ta Kano, to amma wasu hujjoji da kuma waiwayen tarihin abubuwan ya su ka wakana a tsakani ka iya tabbatar da wannan ikirari. Idan dai za a iya tunawa, a kwanan nan a na ta samun sa-toka-sa-katsi tsakanin tsohon gwamnan da mai-ci, inda wasu ke ganin akwai butulci a cikin lamarin irin na an ci moriyar ganga an yada kwaurenta.
A daya bangaren kuma wasu ke ganin so a ke a cigaba da bankarawa a na yin mulkin kama-karya, alhali kowa da lokacinsa. Idan a ka duba kundin tsarin mulkin kasa da dokar zabe a Nijeriya za a tabbatar da cewa, dan takarar gwamnan ko na shugaban kasa ne kadai su ke da ikon tsayar da mataimakansu. Hatta jam’iyya ba ta da ikon zabar wa dan takarar gwamna ko na shugaban kasa wanda zai iya yi mu su mataimaka, domin damar kacokan ’yan takarar dokokin kasa su ka baiwa. To, ka ga kenan a bisa fahimtr ikon doka, Kwankwaso ne ya dauko Ganduje tun a 1999 ya nada shi a matsayin mataimakinsa su ka yi mulki na tsawon shekara hudu zuwa 2003.
A wannan shekara ta 2003 ne su ka sake tsaya wa takara, inda Kwankwaso ya sake daukar Ganduje a matsayin mataimakin gwamnansa su ka yi takara tare, amma sai su ka fadi zaben. Bayan shekara takwas ne kuma dai a 2011, Kwankwaso ya sake tsallake kowa ya zabi Ganduje a matsayin mataimakinsa, inda su ka tsaya takara tare har su ka sake lashe zaben kujerar gwamnan jihar, sannan su ka sake shimfida mulki na shekara hudu a tare. Wannan tarihi ya nuna cewa, Kwankwaso ne ya yi wa Ganduje alfarma ta fuskar ikon da ya ke da shi a dokance, domin bisa doron doka Kwankwason ya na da damar da zai iya daukar wani mutum daban a matsayin mataimakinsa, ba sai Ganduje ba, tunda jam’iyyarsa ta tsayar da shi takara ta hanyar ba shi tikitin tsaya wa neman kujerar gwamna a lokuta daban-daban har guda uku (wato 1999, 2003 da 2011). Idan a ka tsaya iya nan, ko shakka babu za a ce Kwankwaso ne ya taimaki Ganduje a siyasance.
To, amma ba a nan gizo ke sakar ba; idan a ka yi duba izuwa ga alakarsu takararsu ta fuskar siyasa a tarihince, hakika za a iya cewa, Ganduje ne shi Kwankwaso ya taka ya ci moriyar dukkan zabukan da ya lashe. Gabanin zaben 1999, a cikin ’yan takarar da ke neman kujerar gwamna, an fi jin duriyar siyasar Ganduje da ta Marigayi Magaji Abdullahi a jihar Kano fiye da ta Kwankwaso. Da yawan ’yan jihar da ba su damu da siyasa ba ma ba su san ko da sunan Kwankwaso ba, duk da cewa ya taba rike mataimakin shugaban majalisar wakilai na kasa a lokacin mulkin soja na Ibrahim Badamasi Babangida, domin majalisa ce wacce ba ta yi aikinta ba, saboda rashin mika mulki ga hannun farar hula.

To, a 1999 sai ya zamana shi Magaji Abdullahi a tsohuwar jam’iyyar APP ya ke takara, shi kuma Ganduje a PDP ya ke neman tasa takarar tare da su Kwankwason da irin su Marigayi Ahmad Rufai da sauransu. Dalilai da dama sun saka a na kallon Ganduje a matsayin wanda ya fi duk masu neman takarar PDP karfi, musamman kasancewarsa shi ne wanda ya fito daga gidan Santsi, wato gidan tsohon gwamnan jihar, Marigayi Abubakar Rimi, sannan kuma a na ganin cewa, Ganduje ya fi sauran ’yan takarar masu gidan rana kasancewarsa bai dade daga sauka daga kujerar kwamishina na tsawon shekaru da ya shafe ya na yi a jihar ba a lokacin mulkin soja na Marigayi Sani Abacha. Wannan ya sanya a cikin PDP Ganduje mutanen gari ke kallo, yayin da APP kuma Magaji a ke kallo.
To, amma da a ka zo zaben fitar da gwani, sai gidan Tabo (wato gidan gidan tsohon gwamnan jihar Marigayi Sabo Bakin Zuwo a karkashin jagorancin tsohon minista Musa Gwadabe da su ka tsayar da Kwankwaso) su ka hade da gidan NPN na tsohon minista Aminu Bashir Wali mai goyon bayan Rufai. Wannan lamari ya sa an yi kiki-kaka, inda duk da lashe takarar fitar da gwani da Ganduje ya yi, sai gidajen siyasar biyu (Tabo da NPN) su ka ki yarda; su na ganin cewa, bai kamata a ce daya ta rinjayi biyu ba. Bayan doguwar tattaunawa a karkashin kasa a je a ka sake sabon zaben fitar da gwani, don a zauna lafiya.
A wannan zaben fitar da gwanin sai Tabo da NPN su ka hade kuri’unsu guri guda su ka zabi Kwankwaso shi kadai bisa alkawarin zai bai wa Rufai takarar kujerar mataimakin gwamna. Hakan kuwa a ka yi. Bayan sanar da sakamakon zaben, sai Kwankwaso ya ayyana Rufai a matsayin mataimakinsa. To, amma da su ka fito yakin neman zabe cikin gari a washegari, sai a ka rufe su da jifa. Ba shiri su ka koma Gidan Akida na Abubakar Rimi da ke kan titin Maiduguri. Bayanai sun tabbatar da cewa, a nan ne a ka roki Rimi ya shawo kan Ganduje ya amshi takarar mataimakin gwamna, don a samu a kai gaci, domin wannan barakar ta na nuna cewa, akwai yiwuwar APP za ta iya lashe babban zaben jihar, saboda ta riga ta tsayar da Magaji Abdullahi a matsayin dan takarar gwamna ba tare da sa’insa sosai ba. An ce, Rimi ne ya rarrashi Ganduje ya yarda ya karbi takarar mataimakin gwamna a karkashin Kwankwaso, don a kai gaci.
Daga nan ne dan takarar PDP ya ke iya fitowa yakin neman zabe, saboda albarkacin an ga Ganduje (wanda Rimi ke goyawa baya) a cikin tawagar. An yi ittifakin cewa, wannan mara wa Kwankwaso baya da Ganduje ya yi a 1999 ce ta sanya a ka karya Magaji Abdullahi a ranar zaben gwamna, wanda hakan ne ya kai ga Kwankwaso lashe zaben. Bugu da kari, a 2003 wasu tartiban bayanai sun nuna cewa, sakamakon raba gari da a ka yi tsakanin su manyan siyasar jihar irinsu Rimi, Wali da Gwadabe, sai Rimin ya kira Ganduje ya ce ma sa ya rabu da Kwankwaso ya fito takarar gwamna da kansa. Ya yi ma sa alkawarin zai sa a ANPP ta tsayar da shi takarar gwamna, domin Kwankwaso ba zai ci zabe ba.
To, amma sai Ganduje ya bai wa Rimi hakuri; ya ce ba zai iya barin Kwankwaso a irin wannan tsaka mai yiwuwa ba, domin a lokacin gwamnatin Kwankwaso ta yi bakin jini a kan batun kaddamar da Shari’ah a Kano da mafi yawa ke ganin gwamnatin na yiwa batun zagon kasa. Haka Ganduje ya runtse idanu ya mara wa Kwankwaso baya a ka wannan tsaka mai wuyar su ka fadi a zabe tare, ita kuma ANPP a karkashin takarar Ibrahim Shekarau ta lashe zaben, kamar yadda Rimi ya tabbatar wa da Ganduje tun da fari. A na ganin wannan ne dalilin da ya sa Kwankwaso ya nada Ganduje mataimakinsa na musamman lokacin da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya nada shi minista. Kazalika a 2011 lokacin da PDP ke kokarin kwace mulki daga ANPP a jihar Kano, daya daga cikin muhimman abubuwan da su ka taimaki PDP shi ne kashe wutar rikicin neman kujerar mataimakin gwamna, domin a lokacin a na ta faman rikici a cikin ANPP kan wanda zai gaji Shekarau. Babbar dabarar da Kwankwaso ya yi ita ce, kiran Ganduje da ya yi ya ba shi takarar mataimakinsa. Tabbas wannan hikima ta kawo karshen duk wata wutar fitina da a ke tsammanin za ta iya ruruwa a PDP kan fitar da wanda zai mara wa Kwankwaso baya, domin ya dauko wanda ya yi ma sa a can baya. Don haka duk na hannun damansa sai su ka hakura, duk da cewa, da yawansu sun fi Ganduje kusa da Kwankwason, domin ’yan cikin gida sun san cewa bukatar siyasa ce kadai ta ke zaunar da Kwankwaso da Ganduje a inuwa daya, amma ba don tsantsar kaunar juna ba.
Zaben Ganduje da Kwankwaso ya yi ya yi rana, domin an lashe zaben kuwa. Shekarun hudun da su ka biyo bayan zaben 2011, Kwankwaso bai samu rigingimu a gwamnatinsa kan wanda zai gaje shi ba. Wato ya taki sa’a mataimakinsa mai biyayya ne. don haka ya mike kafa yadda ya ke so ba tare da fargabar komai ba. To, amma masu iya magana su na cewa, tsiyar Nasara sai za shi gida, domin a lokacin da batun babban zaben jihar ya taso, Kwankwaso bai ankara ba sai ya wayigari yawancin na jikinsa Ganduje su ke yi.
Tartiban bayanai sun nuna cewa, Kwankwaso ya so ya tsayar da wani daban ba Ganduje ba, amma fargabar irin tawayen da za a iya yi ma sa a cikin sabuwar jam’iyyar da su ke koma, APC, ya sa ya hakura ya mara wa Gandujen baya, saboda kada irin abinda ya sam Shekarau a 2011 ya faru a kan shi Kwankwason, inda sakamakon dagewa da Shekarau ya yi a kan tsayar da Salihu Sagir Takai, a ke ganin ya zama sanadiyyar faduwar ANPP a shekarar. Don haka wasu ke ganin cewa, ba da son ran Kwankwaso ya tsayar da Gandujen ba, domin babban misali a nan shi ne, me ya sa Kwankwaso bai tsayar da Ganduje takarar gwamna a 2007 ba lokacin da EFCC ta hana shi tsaya wa takarar gwamnan jihar? A ganin wasu, hakan ya nuna cewa, tun fil’azal Kwankwaso ba ya so Ganduje ya zama gwamna kamar shi, kamar yadda wasu ke hasashe. To, amma duk da cewa, Ganduje ba dan takararsa ba ne, amma lashe zabe da APC ta yi kacokam a jihar ta Kano ya bai wa Kwankwason wata martaba ta musamman a siyasance, domin da ba a tsayar da Ganduje ba, ba za a iya tabbatar da abinda zai faru ba a 2015. Bisa wadannan bayanai da su ka gabata, za a iya gaskata cewa, idan za a yi duba ta fuskar doka, za a ce Ganduje ne ya ci gajiyar Kwankwaso, domin da bai ba wa Gandujen takarar mataimaki ba, da bai sami damar da ya samu ba. Amma idan idan a ka dubi batun ta fuskar siyasa, to za a ce ne, Kwankwaso ne ya ci gajiyar Ganduje, domin dukkan zabukan da Kwankwaso ya lashe a matsayin gwamna, idan da bai dauki Gandujen a matsayin mataimakinsa ba, da bai kai labari ba. Wallahu a’alamu!


Advertisement
Click to comment

labarai