Connect with us

LABARAI

Buhari Da Ganduje Ne Yan Takararmu A 2019 -Hon. Idi Gwangwan Rano

Published

on


Shugaban jam’iyyar APC na Rano Honorabale Alhaji Idi Abubakar Gwangwan Rano ya bayyana cewa mu mutanan shiyar Rano da ma sauran masu kishin jam’iyyar mu ta APC a kano da kasa baki daya Muhammad Buhari shi ne dantakarar su a 2019 in Allah ya kaimu lafiya haka kuma Gwamnoni APC su ne yan takarar kowa ne dan APC kamar yadda mu a nan shiyar Rano dama sauran yan APC, to gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje shi ne yan takararmu a 2019.

Alhaji Idi Abubakar Gwangwan ya bayyana haka ne jam kadan da kammala ba da sakamakon zaben kananan hukumomin kano 44 da kansaloli 484 da Jam’iyyar APC talashe su baki daya a zaben da aka gudanar a ranar Asabar dinnan da ta gabata ta 10/2018.

Idi Gwangwan ya ce ba wani abu ne ya sa ya bayyana hakan ba sai dai saboda ya san duk mutanansu na wannan shiya ta karamar hukumar Rano ya san sun ci gajiyar aiyoka da gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta yi musu kuma ya san duk mutanan wannan yanke karkashin jagoran cin tsohon sifika wato kakakin majalisar Dokoki na Jihar Kano a baya Ganduje da Buhari su ke yi sakamakon samar da tsaro da shugaban kasa yayi da kuma aiyokan da Gwamna Dakta Ganduje keyi daga hawanshi zuwa yau.

Shima Honorabale Nura Danlami Rano wani matashi ne da ya ce tsaran da aka samu a zamanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma yadda Gwamna Ganduje ke tafi da siyasa ya sa ya yadda ya ansa kiran dattawa, da matasa, matan rano akan ya nemi takarar majalisar dokoki ta Rano a 2019 idan Allah ya kaimu.

A na sa bagaren, shugaban karamar Hukumar Rano Honorabale Abdullahi Alasan Sansan, ya ce abin da ya fi ba shi sha’awa a lokacin wannan zabe na kananan hukumomi 44 na kano a zamanin Gwamna Ganduje shi ne yadda zaben ya gudana lafiya ya ce to haka ma su ke san gani a 2019 don haka ya yabawa mutanan karamar hukumar Rano akan yadda suka gudanar da zabe lafiya kuma suka zabe jam’iyyar APC karkashin jagoran cin Muhammadu Buhari da Gwamnan kano Ganduje.

Shi kuwa shugaban karamar hukumar Bunkure na ruko kuma mai barin gado Honorabale a Ado Abdu Hotoro ya bayyana yadda aka yi zabe lami lafiya a matsayin abin godiya ga mai duka da kuma yabawa jagororin mulki kowane mataki daga tarayya har zuwa Jiha da sauran masu ruwa da tsaki a Bunkure da ma kano baki daya.

Akarshe dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar kibiya a majalisar dokoki ta Jihar kano Honorabale Mai Fada Bello ya ce ansami tsaro, ansamo Karin wutar lantarki a ko ina cikin kasar nan nan kuma shiyar su ta Kibiya, Rano da Bunkure Gwamna Ganduje yayi musu aiyokan hanyoyi da sauran abubuwan ci gaba to ai dole su zabe Buhari da Ganduje domin dai yaba kyauta tokoyci. Sai dai kuma wakilinmu ya rawaito mana cewa shugaban karamar hukumar Kibiya na ruko mai barin Gado Sagiru Umar Kofa ya yi layar zana ana tsaka da gabatar da zaben kananan hukumomin Jihar Kano.


Advertisement
Click to comment

labarai