Connect with us

RAHOTANNI

Azzalumai Ne Ba Su Son Zama Na A Nijeriya (II) –Maina

Published

on


Ci gaba daga Jiya

Malam Abdulrasheed Abdullahi Maina ya aka yi ka dawo Nijeriya ne?

Lokacin da na tafi, sai ’yan majalisa suka ce wa shugaban kasa ka zabi Maina ko ka zabi ’yan majalisa. Na tashi na tafi wajen sahugaban kasa na ce masa a zabi ’yan majalisa, Saboda su mutane ne da yawa ni kuma ni kadai ne. Don haka abin da ya faru ya zo ya faru na bar kasa zuwa Dubai. Da na tafi sai ’yan majalisa suka aikewa da shugaban ma’aikata takaarda cewa sai a koreni daga aiki. Ka san kuma na hana a bashi wadancan kudade da suke sacewa na fansho. Domin na rubuta takarda zuwa ga ma’aikatar kudi cewa a dakatar da tura masa biliyan biyar da miliyan dari biyu. A rinka tura masa miliyandari takwas da ashirin da biyar. Ka ga na hana tura masa sama da biliyan hudu kenan. Saboda haka shima cike yake da ni. Domin ya rasa yadda zai yi da ni. Saboda shugaban kasa ya cire hijabi tsakanina da shi. Saboda haka ne ya sa ya sami wadannan kudaden. Da akwai wannan hijabin da manyan nan za su rinka yanke kudaden.

Don haka sai na kai kara kotu a shekarar 2013. Na maka gwamnatin tarayya kotu da majalisar dattawa da ta wakilai. Nasarar da na samu ne ya sanya aka yi amfani da ita yanzu aka dawo da ni aiki. Na yi nasara a kansu ne saboda ina da gaskiya. Kotu ta ce a mai da ni aikina. Ba yanzu bane aka ce a mai da ni aiki. Tun a shekarar 2013 kotu ta ce a mai da ni aiki.Abin da ya sa tun a  wancan lpkacin ban dawo ba. Saboda ina jin tsoron yadda rayuwata za ta kasance ne a wannan lpkacin idan na dawo. Amma da wannan gwamnati ta karbi mulki. Sai shugaba Buhari ya kai ziyarar aiki kasar Dubai. A nan ne aka kirani otal din da ya sauka na je. A nan ne aka ce zan zauna da wasu daga cikin ministoci. Wallahi ban taba ganin ministan shari’a ba sai a wannan lokaci. Gara ma NSA Munguno shi na sanshi tun kafin wannan lokaci. Na zauna da su muka yi mitin. Suka ce wane irin taimako zan musu a wannan Gwamnati kamar yadda na yi wa waccan gwamnatin? Na ce musu Buhari uba ne a wurina. Domin lokacin da na ke yaro Ubana ya yi hulda da shi. Na ce duk irin taimakon da ake so in yi zan yi don a taimaki al’umma. Suka ce ai yakamata ka dawo gida ne ka yi, Na ce musu ko ina nan zan yi muku abin da kuke sao na yi. Mun tattauna abubuwa sosai na tsaro. Wanda ba zai yiwu in sanar da kai ba. A nan ne fa da za su tafi na ce bari na basu tukwici.

Na shiga kwamfuta na fitar musu da wata takarda na ce musu tunda yanzu ana neman kudine da za a yi wa al’umma aiki to ga wannan su tafi da shi. Ko da suka karbi takardar ba su yarda za a sami naira miliyan dari a ciki ba. Da suka zo gida sai gashi sun sami tiriliyan daya da biliyan dari uku. Su masu zagina din sun fadawa ’yan Nijeriya cewa Maina ya tara kudi?

Saboda haka na yi mamaki. Ni da nake bin bashin biliyan sittin, shine za a ce na saci biliyan biyu. Idan haka ne sai in ce su cire biliyan biyu dinsu su bani sauran biliyan hamsin da takwas da nake da su a wurinsu. Ballantana ba wasu biliyan biyu da aka sata. Shi kansa shugaban ma’aikatan ai kotu ta wankeshi a kan wannan zargi.

Kada na bar tambayar da ka yi min. Saboda haka daga Dubai ne na umarci lauya na da ya rubuta takardar koke zuwa ga ministan shari’a cewa a mayar da ni aikina ko kuma in sake komawa kotu. Da aka rubuta shi kansa ministan ya yi mamaki da ya ga takardar kotu na cewa a mayar da ni aiki. Ya yi mamaki tun a wancan lokaci da ba a mayar da ni aiki ba.

Sai ya dauki takarda ya rubutawa Hukumar daukar ma’aikata cewa ga wani kaza kotu ta ce a mayar da shi aiki. Su kuma hukumar suka zauna suna yi mitin su goma sha biyar. Daga nan suka tura wa shugabar ma’aikata takarda cewa ta tura zuwa inda na ke aiki, wato ma’aikatar harkokin cikin gida, domin su yi dubo ga ita wannan takarda a yi gyaran abin da ya kamata. Aka tura wannan takarda mutum ashirin da biyar suka duba ta, Ban sansu ba. Suka tambaya shin wane laifi ne ma na yi da har aka koreni aiki? Suka ce ai ko ba a zo da takardar kotu ba za su mayar da ni aiki, Domin ba laifin da na yi. Saboda haka sai suka rubuta cewa sun amince a mayar da ni bakin aiki. Suka nemi da a bani Darakta, domin sa’o’ina a wajen aiki yanzu manyan sakataroro ne ba ma daraktoci ba. Ko lokacin da na bar aiki shekaru biyar da suka wuce ai ki mataimakin darakta ne. Saboda haka wannan na wani abu bane don an bani darakta.

Suka tuwa wannan takarda zuwa ofishin shugabana ma’aikata, ita kuma ta tura takarda zuwa hukumar daukar ma’aikata. Ta ce ma’aikatar harkokin cikin gida sun amince da mayar da Maina aiki, saboda haka kuma ku yi na ku aikin. Amma abin da ya bani mamaki shine ni dai ma’aikacin Gwamnati ne da ya fara aiki tun daga mataki na 8, saboda haka ba mukamin siyasa aka bani ba, wanda shugaban kasa ke nadawa duk lokacin da ya ga dama. Saboda haka na san cewa shugaban kasa bai da ikon korata aiki. Idan kuma za a yi to shikenan a bani takarda, idan an bani sai in koma kotu. Kuma wannan din ma wasu ne suka yi wa shugaban kasa din karya.

Daga nan aka kammala komai aka sanar da ni. Aka tura kwafen takardar zuwa ofishin shugabar ma’akata. Shugabar ma’aikata ta dauki wannan takarda ta sanyawa hannu sannan ta tura ta zuwa ma’aikatar da na ke aiki. Ma’aikata ta suka kira ni, suka bani takarda na koma ofis. Daga nan na sami labarin cewa wai ministan shari’a ya mayar da ni aiki. Ministan ba zai iya mayar da ni aiki ba. Kotu ce ta mayar da ni aikina.

 

Wane mataki kake bi don ganin an wake ka daga wadannan zarge-zargen da ake yi maka?

Matakai kam ina nan ina bi kala-kala. Yanzu haka kamar yadda ka sani na maka Ibrahim Magu kotu a matsayin sa na Magu. Sannan na maka ita EFCC din a gaban kotu saboda sun yi min kazafi.

Idan za ka iya tunawa akwai lokacin da aka ce an sami kudi sama da biliyan daya a asusun ajiya da dan Maina mai shekaru 7. Ni da bani da da mai shekaru uku, hudu, biyar, shida, bakwai, takwas, tara, goma, sha daya ko sha biyu. Aka je aka dauki hoton almajiri aka ce ga dan Maina. Daga nan na fito a jarida na ce idan shi Magu din da gaske ya ke to ya buga wannan abin a jarida mutane su gani. Amma har yau shiru.

Abin da ke faruwa shine tsoro ake ji na dawowa ta Nijeriya, ana tsoron in je gaban Buhari in bude kwamfuta na ne. Domin za ta ci mutane da yawa. Yau da zan bar kasar nan ba za ka kara jin an yi maganar Maina ba. Saboda haka so suker su koreni daga kasar ta kowace hanya. Ni ban dawo don in tona wa wani asiri ba. Ni na dawo ne in taimaki kasar nan. Kuma dawowa ta ban da wannan tiriliyan daya da biliyan dari uku din da minista ya fada cewa na samo wa Nijeiya, akwai wasu kudadrn da na samo. Amma ai ban fada ba.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai