Connect with us

WASANNI

Akwai Matsala A Kungiyar Mu, In Ji Mourinho

Published

on


Mai horar da yan wasan kyngiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya ce, ko da kungiyarsa za ta shafe tsawon sa’oi 10 tana fafatawa da Newcastle, ba za ta zura kwallo guda ba a wasan da suka fafata a ranar Lahadi.

Mourinho ya bayyana haka ne bayan Manchester United ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a karawar da sukayi da kungiyar Newcastle a jiya a gasar firimiya ta Ingila.

Mourinho ya ce, ‘yan wasan Newcastle sun zage dantse sosai wajen ganin sun samu maki, yayin da yace, abin da suka yi yana da kyau muddin suna muradin lashe wasan.

Sai dai ya kara da cewa, ‘yan wasan na Newcastle sun yi wasan ne tamkar dabbobi don ganin sun samu nasara a gida kuma a karon farko tun cikin watan Oktoba a gasar ta firimiya a Ingila.

Yanzu haka sau biyar kenan Manchester United ke shan kashi a gasar  ta bana, in da kuma Newcastle ta fitar da kanta daga matakin ‘yan dagaji sakamakon kwallon da Matt Ritchie ya ci ma ta a wasan.

Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta samu nasara a kan Southampton da ci 2-0 a fafatawar da suka yi a gasar  a ranar Lahadi, yayin da Huddersfield ta lallasa Bournemouth da ci 4-0.

Mourinho yace yan wasansa suna bukatar sake dagewa domin shawo kan matsalar da suke fuskanta a yan kwanakin nan inda yace abubuwa basa tafiya yadda yakamata a kungiyar.


Advertisement
Click to comment

labarai