Connect with us

RAHOTANNI

Akwai Alherai Mai Yawa Ga Wanda Ya Shirya Mauludi –Sadaukin Zazzau

Published

on


An shawarci al’ummar musulmi a duk inda suke das u rika shirya taron mauludi, domin amfana da dinbin ladan da ake samu ga duk wanda ya shirya taron mauludin.

Wannan shawar tare da fadakarwa ta fito ne daga Sadaukin Zazzau, Alhaji Yusuf Shehu Idris, a zantawarsa da Leadership A Yau jim kadan bayan taron mauludi day a saba shiryawa duk shekara a gidansa da ke birnin Zariya.

Sadaukin Zazzau Alhaji Yusuf Shehu Idris ya ci gaba da cewar, malamai da dama sun sha gabatar da wa’azi a lokutan tarurrukan mauludi, na ladan da mai kowa mai komi ya tanada ga duk wanda ya tara al’umma, aka yi karatu domin Annabi Muhammadu [S.A.W.] hatta al’ummar musulmi da suke halartar taron mauludi, a dewar Sadaukin Zazzau, baya ga ladan da suke samu, na halartar taron musulunci, wanda ya halarci taron ya kan sami karin ilimin addini na fannoni da dama musamman tarihin rayuwar Annabi Muhammadu  [S.A.W.] na yadda ya rayu da kuma ire-iren gudunmuwar day a bayar domin ci gaban addinin musulunci.

A dai zantawar da aka yi da Sadaukin Zazzau, Alhaji Yusuf Shehu Idris, a taron mauludin wannan shekara da ya shirya, an yi addu’o’I  godiya ga Allah [S.W.T.] na cikar mai martaba Sarkin Zazzau shekara 43 a karagar masarautar Zazzau da kuma yi wa kasa addu’o’in ci gaba da samun zaman lafiya mai dorewa, fiye da yadda aka samu a yau.

Shi ma fitaccen shehin malamin nan da ke Zariya, Shekh Sani Halifa dogon wa’azi ya yi na wajibi ne al’ummar musulmi su kara tashi tsaye wajen neman ilimin addinin musulunci, ya ce rashin karatu mai inganci ne ke sa fadin bayanin da musulunci bai fadi ba.

Wannan, kamar yadda Shekh Sani Halifa ya ce wadannan kalamai na kawo matsaloli a cikin addinin musulunci da kuma kawo rashin fahimta a tsakanin al’ummar musulmi,baya ga durkusar da addinin musulunci da ire-iren wadannan kalamai ke haifar wa.

A sakonsa wajen taron ,mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya yi kira ga al’ummar musulmi das u ci gaba da gudanar da rayuwarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada,haka ne kawai zai sa a ci gaba da samun ci gaba  da kuma hadin kan musulmi a duk inda suka tsinci

kansu.

Mai martaba Sarkin Zazzau da makaman Zazzau Alhaji Umaru Mijinyawa ya wakilce shi, ya kuma yaba wa malamai da suke gabatar da fadakarwa a tarurrukan mauludi a masarautar Zazzau, na yadda suke bakin kokarinsu, na ganin fadakarwar da suke yi ya zama silar ilmantar da musulmi da kuma haduwar kan musulmi, ya ce ya na fatan malaman za su dore da yin haka a nan gaba.

Wannan taron mauludi da Sadaukin Zazzau Alhaji Yusuf Shehu Idris ya shirya ya sami halartar fitattun malamai da suka hada da Shekh Sabitu, Sardauna da Shekh Mansur Kaduna da Shekh Abdulhakami Muntaka Kumasie da kuma wasu daga cikin Hakiman masarautar Zazzau.


Advertisement
Click to comment

labarai