Connect with us

KASUWANCI

A 2017 Bankuna Sun Bayar Da Bashin Tiriliyan 63 Ga Kamfanoni Masu Zaman Kansu

Published

on


Alkalumma daga hukumar kididdiga ta kasa sun nu na cewa, Bankunan kasannan sun baiwa wasu kamfanoni masu zaman kansu basukan da suka kai jimillan Naira Tiriliyon 63.27, a shekarar da ta gabata 2017.

Wannan lissafin yana daga cikin bayanan da hukumar ta kididdiga ta fitar a ranar Juma’a ne a Abuja wacce kuma wakilinmu ya yi tsinkaye gare ta.

Wannan adadin ya nu na an sami karin Naira Tiriliyon 2.2 kenan a kan basukan Naira Tiriliyon 61.5 wanda kamfanonin suka ci a shekarar 2016.

Dalla-dalla, lissafin ya nu na, kamfanonin sun ci bashin Naira Tiriliyon 16 a zangon farko na shekarar da ta gabata. A zango na biyu da na uku, kamfunan sun ci bashin Naira Tiriliyon 15.7, da kuma Naira Tiriliyon 15.82 ne bi-da-bi.

Rahoton kuma ya nu na cewa, kamfanonin da ke sashen Man Fetur da Iskar Gas, sune suka fi kowane sashe cin bashin daga Bankunan, domin kuwa sun jibgi bashin Naira Tiriliyon 14.2 ne su kadai kawai.

Kamfanonin da ke biye da na wannan sashen su ne, kamfanonin kere-kere, wadanda su ma suka ci bashin Naira Tiriliyon 8.79, daga Bankunan.

Amma a daya bangaren kuma, Kamfanonin tonon albarkatun kasa, sune suka ci bashi mafi kankanta daga Bankunan, domin kuwa kwata-kwata bashin Naira Bilyan 56.6 ne kacal suka karba da sunan bashi daga Bankunan.

Sauran sun hada da Kamfanonin da suka shafi harkokin noma, wadanda suka ci bashin, Naira Tiriliyon 2.07, sashen hasken lantarki, sun karbi bashin Naira Tiriliyon 1.85, sashen gine-gine, sun karbi Naira Tiriliyon 2.56, sai kasuwanci, sun amshi rancen, Naira tiriliyon 3.89, kamfanoni masu alaka da gwamnati sun karbi rancen Naira tiriliyon 3 ne daidai.

Kamfanonin da ke harkar filaye da gidaje sun amshi basukan Naira Tiriliyon 3.13, Inshora, sun ci bashin Naira Tiriliyon 3.89, Ilimi,sun amshi rancen Naira Bilyan 310, Sadarwa, akwai bashin Naira Tiriliyon 3.2 a kansu. Zirga-zirga da ajiya, sun karbi rancen Naira Tiriliyon 1.55, a sa’ilin da sauran sassan suka amshi bashin Naira Tiriliyon 1.47, daga Bankunan.

Wani tsohon Shugaban cibiyar kasuwanci na birnin Tarayya Abuja, Mista Tony Ejinkeonye, ya yi kira ga Babban Bankin kasa da ya rage yawan kudaden da yake taskacewa na ko-ta-kwana, domin a sami karin kudaden da Bankunan za su yi amfani da su wajen bayar da basukan da kamfanoni da kuma sauran mabukata ke bukata.

Yana mai cewa, yin wannan kiran ya zama tilas,domin kuwa a yanzun haka, Bankunan sun kai matuka na iya abin da za su iya badawa rancen, wanda iyakacinsa shine kashi tamanin cikin dari na ajiyarsu.


Advertisement
Click to comment

labarai