Connect with us

LABARAI

Shirin ‘Gani Da Ido’ Na Gwamna Abubakar Ya Daga Darajar Ilimi A Bauchi

Published

on


Shugaban hukumar Kula da Makarantu na musamman a jihar Bauchi, wato ‘Special Schools’ Yakubu Ibrahim Hamza ya shaida cewar, abu kwaya daya da mutum zai bari don na baya su rika tunawa da shi shi ne ya tabbatar da cewar, kowane yaro ya halarci makaranta don samun ilimi mai nagarta walau a karshen karatunsa zai yi aikin gwamnati ko a’a.

A bisa wannan daliline, shugaban hukumar makarantun na musamman ya jinjinawa Gwamna Muhammad Abubakar saboda yadda ya bijiro da wani sabon shiri a bangaren ilmi wanda aka yi wa lakabi da “Eye On Education” da nufin inganta harkokin ilimi a jiharsa ta Bauchi.

Shirin wanda ya kunshi kwararru a fannin ilimi wadanda aka dora masu nauyin kai ziyarar gani da ido a makarantu domin lura da yadda al’amura ke gudana, tare da ba da shawarwari wa wadanda suke tafiyar da harkokin koyo da koyarwa da kuma tattara matsalolin makarantu da zummar kawo mafita.

Shugaban ya yi tuni da cewar, samar da shirin kai ziyarar gani da ido da gwamnatin Muhammad Abubukar ta kaddamar a shekara ta 2015, har ya sa ingancin ilimi a jihar Bauchi ya kai ga cirawa sama, inda alkaluma suka nuna cewar jarrabawar SSCE da aka samu kashi 0.03% cikin dari a shekara ta 2015, a shekara ta 2017 an samu kashi 27% cikin dari.

Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza wanda ya yi jawabin haka a satin da ya gabata sa’ilin da ya karbi bakoncin mambobin wata kungiyar matasa mai fadakar da mutane kan tsarin dimokaradiyya (DEI) a ofishinsa a Bauchi, ya ce wannan yunkuri ya taimaka wajen kara kwazon dalibai da kashi cas’in (90) cikin dari da suka rubuta jarrabawarsu ta karshe, inda suka samu kiredit biyar-biyar zuwa sama da haka, ciki har da turanci da lissafi.

Ya kuma bayyana cewar, ta sakamakon shirin ya sa gine-ginen makarantu ciki har da gidajen ma’aikata da ajujuwa da dakunman kwanan dalibai an gyarasu, wanda hakan ya kawo kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa a makarantu “Ziyarar gani da ido na wata- wata da ake kai wa a makarantun sakandare guda biyar na musamman da suke karkashin hukumar, a yanzu haka an fadada zuwa makarantu hamsin (50) da suke fadin jahar nan, kuma sannu a hankali lamarin zai kai ga makarantu fiye da dari hudu da suke jahar nan da zummar daga matsayin ilimi baki daya”, inji Hamza.

Hamza ya kuma yabawa daliban makarantar sakandare na musamman ta Jibril Aminu da ke jihar Bauchi bisa rawar gani da suka taka a gasar ilimi ta kasa wadda aka yi a Abuja, inda suka zo mataki na uku bayan makarantar yara masu hazaka da ke Abuja da kuma wata makarantar kudi da wakila tana shiyyar kudu maso gabas ko kuma kudu maso kudu wadda a yanzu ba zai iya tuna yankin da take ba.

Shugaban ya kuma jaddada aniyar hukumar ta ganin cewar, matsayin ilimi ya kyautata a jihar, ya kuma bayyana cewar, kafin zuwan gwamnati mai ci a jahar Bauchi galibin makarantu sun durkushe, kuma gine-ginen makarantun sun lalace wasu daga cikinsu basa aiki amma yanzu ana samun natija ta fuskacin kyautata su.

 


Advertisement
Click to comment

labarai