Connect with us

KASUWANCI

Sarrafa Tumatur: Kamfanin BONPET Zai Yi Hadin Gwiwa Da Kamfanonin Yankin Asiya

Published

on


A makon da ya gabata ne Shugaban Kamfanin BONPET Guruf ya rattabawa wata takarda koke hannu, wacce suka aikewa shugaban kasa da ita.

Kamfanin na BONPET ya shahara wurin samar da tumatur na zamani, wanda kuma yake da hadin gwiwa da wasu kamfanoni mabambanta daga yankunan duniya.

bayan fitar da takardar koken da kamfanin ya yi, LEADERSHIP A Yau ta samu jin ta bakin Shugaban kamfanin, Mista Eric. wanda ya bayyana dalilin koken nasu da kuma hadin gwiwar da suke kullawa da wasu kasashen yankin Asiya.

Dangane da hadin gwiwar kamfanin da wasu kamfanonin kasashen waje, Shugaban BONPET ya bayyana cewa; “Muna matukar farin ciki da yi wa al’umma albishir cewa abokan huldanmu daga kasashen waje, wato yankin Asiya masu sarrafa tumatur sun tabbatar mana da cewa sun yanke shawarar yin hadin gwiwa da kamfaninmu na RISCO FOOD LIMITED domin a gina wani kamfanin sarrafa tumaturi da ya fi kowanne girma a duniya, a Jihar Katsina.

“Kamfanin zai rika sarrafa tan dubu dari bakwai da hamsin 750,000 na tumatur a cikin shekara guda.” in ji shi

Shugaban ya kara da cewa; “Muna sa ran kimanin mutanen da kamfanin zai samar wa aikin yi za su kai Dubu goma zuwa Dubu goma sha Biyar, da kuma Manoma Dubu hamsin wadanda za su karu sosai da wannan shiri.

“A tsarin da ake da shi za a fara ne a wannan shekarar ta 2018 kuma za a kammala shi a cikin shekara biyu kacal idan dai babban bankin Nijeriya CBN ya dakatar da Bayar da canjin kudaden kasashen waje ga masu shigo da tumaturin gwangwani zuwa kasar nan. Ya kuma karfafe mu ta hanyar bamu isassun canjin kudaden kasashen waje wadanda za mu sayo injuna da wasu bangarorin injuna da kuma sauran kayan hadin samar da su a nan Nijeriya.

“Kuma hukumar kula da ingancin magunguna ta Nijeriya watau ‘NAFDAC’, ya kamata ta dakatar da yi wa tumaturin gwangwani mara inganci da ake shigowa dasu daga kasashen waje rajista daga yanzu. Ta kuma hana sayar da tumaturin gwangwani maras inganci a kasuwannin Nijeriya.

“Ita ma Hukumar hana Fasa kauri ta kasar nan ya kamata ta hana shigo da tumaturin gwangwani a cikin Nijeriya kamar yadda suke yi akan shinkafa” In ji shugaban kamfanin na BONPET.

 


Advertisement
Click to comment

labarai