Connect with us

KASUWANCI

PTAD Ta Fara Tantance ‘Yan Fanshon NITEL Da MTEL A Arewa Maso Gabas

Published

on


Masu karban Fensho sun yaba da shirin tantancewan da hukumar da aka dorawa alhakin bin kadi da kuma biyan ‘yan fenshon hakkokin su ta PTAD, ke yi. Tuni dai hukumar ta PTAD, ta fara gudanar da tantance ‘yan fensho 900, wadanda duk cikkan su tsaffin ma’aikatan hukumar sadarwa ce ta kasa NITEL da kuma MTEL a Jihar Gombe, domin biyan su hakkokin su na kudaden fenshon da suke bin gwamnati.

Wannan bayanin yana daga cikin sanarwar da hukumomin ne suka bayar ga manema labarai a Kwalejin Ilimi ta Gombe, wajen da ake gudanar da akin tantancewan.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, ta sami izinin tara dukkanin bayanan ‘yan fenshon ne da kuma jimillan hakkokin su daga hukumar sayar da kadarorin gwamnati ta kasa (BPE).

Ta kuma sanar da cewa, shi wannan shiri na tantance ‘yan fenshon zai taka marhaloli da dama na tantancewa, kafin a kai ga biyan sahihan ‘yan fenshon hakkokin na su.

Tantancewan da aka fara a ranar 15 ga watan Janairu, zai gudana ne a cibiyoyi guda bakwai na kasarnan bi-da-bi, da suka kunshi, Enugu, Fatakwal, Kano, Gombe, Abuja, Lagos 1 da kuma Lagos 2, a kuma kowace cibiya  za a kwashe kwanaki takwas ne ana gudanar da tantancewar, ana kuma sa ran dukkanin ‘yan fenshon da su zo da dukkanin takardun da aka bayar da sanarwar za a tantance su da su wajen tantancewar.

Hakanan su ma magadan ‘yan fenshon wajibi ne da su zo da takardun da aka zayyana a cikin sanarwar.

Hukumar kuma ta bayyana cewa, ta karbi lambobin wayan marasa lafiya da suke kwance daga cikin ‘yan fenshon, za kuma ta bi su duk inda suke kwancen domin tantance su.

Wasu daga cikin ‘yan fenshon da suka yi magana da manema labarai a wajajen da ake tantance su din sun yaba da wannan hobbasan da gwamnati ta yi na biyan su hakkokin su, kamar yadda ake biyan sauran ma’aikatan gwamnati a cikin kasarnan.

Mangus Umaru Babasanda, daga Jihar Borno, wanda ya yi aiki a hukumar ta NITEL, a matsayin Shugaban masu gadi, wanda kuma yake lura da sashen Arewa maso gabas, cewa ya yi, “Mun jima muna sauraron wannan hakkin namu, da yawanmu ma har ,um fitar da rai a kan samun na shi.

“A ranar litinin ne aka fara tantancewar, amma ni sai yau ne na samu aka tantance ni, mu ‘yan fensho,muna yabawa gwamnatin Tarayya da kuma hukumar PTAD, a kan tsarin da ake bi na tantancewar, domin yana gudana cikin lumana, hatta ma abinci ana ba mu a wannan wajen.

“Fatana dai ita ce, a biya mu hakkokinmu da zaran an kammala tantance mu.”

Ita ma da take maganaa a wajen, Sakatariyan hukumar ta Fensho a Jihar ta Gombe, Zainab Haruna, ta yabawa hukumar ta PTAD, a kan kyakyawan tsarin da ta yi na tantancewar.

Ta kuma yi fatan cewa, ‘yan fenshon za su sami hakkokin na su ta yadda hankulansu za su kwanta da zaran an kammala tantancewar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai