Connect with us

SIYASA

‘Nijeriya Na Bukatar A Ceto Ta Daga Halin Da Ta Ke Ciki’

Published

on


A ranar uku ga watan Fabrairun 2018 ne Sabuwar jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa N.R.M ta gabatar da taron kaddamarwa tare da bayyana kudurorin jam’iyyar.

Taron wanda aka gabatar a dandalin ‘Eagle Skuare’ ya samu halartar dimbin magoya bayan wannan Jam’iyya ta ceton Al’umar Kasa, wadanda suka zo daga sassa daban-daban na Nijeriya; Kudanci da Arewacin Kasa.

Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, Sanata Said Muhammad Dansadau ya gabatar da jawabi mai muhimmanci a wurin taron, wanda kuma LEADERSHIP A Yau ta samu halarta, ta nakalto wa masu karatunmu. Ga gundarin jawabin na shi:

“Ina yi wa manyan bakinmu, ’yayan jam’iyya da magoya baya maraba da zuwa. wadanda suka niko gari daga sassa daban-daban na tarayyar Nijeriya domin halartar wannan taro.Wannan taro ne na kaddamar da jam’iyyar Ceton al’ummar Kasa, wacce hukumar zabe ta kasa INEC ta mika wa takardar rajista a ranar 10 ga watan janairun 2018.

“Yi wa Jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa rajista ya bude wani sabon faife a tarihin Nijeriya, wanda ya zo wa da ‘yan kasa da karfafawa dangane da sa ran cewa sauki zai samu daga shekarun wahala da aka keto. samuwar Jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa wani nufi ne na Allah, don a tsamo kasar nan daga halin da take ciki na rashin tabbas da kunci da ake ciki.

“A yau, hadin kan al’ummar kasar nan na cikin wani yanayi. Samuwar mabambantan ra’ayoyi da tada kayar baya daga dukkan bangarorin kasar nan, na nuna cewa ana so ne a yi amfani da kabilanci wurin tarwatsa kasar. Kuma duk wannan tana faruwa ne sakamakon rashin daukar matakan da suka dace ne ke neman jefa kasar cikin rudani, rashin tabbas din da ya haifar da rashin hadin kai, tare da yin barazana ga zaman lafiya da tsaron kasar nan tamu mai albarka. Rashin tsaro, da aikata munanan laifuka a fadin kasa. Duk wani wanda Nijeriya ke ransa, kuma dan kasa na gari ya san cewa abubuwa ba su tafiya daidai a kasar nan. Ba a taba samun lokacin da aka samu rarrabuwa a Nijeriya kamar a yanzu ba. Wannan kuma duk ya biyo bayan shekarun da ake dauka cikin gurbataccen tsarin gudanarwa na gwamnati da rashin akidar kawo sauyi. An cutar da kasarmu ta hanyar kawar da ita daga kan alkiblar da ta dace, an shigo da son rai, ninanci, da rashin inganci. Sakamakon rashin annoba, sai shugabanninmu suka kirkiro mana da annobar da gangan, suka jefa mu cikin mawuyacin halin rayuwa, wadanda suka hada da yawaitar kashe-kashe, ta’addanci, da wasu matsalolin tattalin arziki. Wannan ne ya sa ake bukatar daukar mataki cikin gaggawa, lamarin da ya fi karfin mu sanya son rai a ciki matukar muna son ceto kasar nan daga halin da aka jefa ta a ciki.

“Akwai bukatar a yi aiki don bunkasa Nijeriya. Aiki ne da dole a yi shi. Abin da ake bukata don yin wannan aiki shi ne kawo sabbin fikirori, daukar matakai, da kuma karfin halin sauya tsari da yanayin gudanarwar gwamnatin Nijeriya.Wannan shi ne abin da Jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa ta kawo wa ‘yan kasa. sabbin ra’ayoyi da shaukin raya kasa, yin gaskiya a yayin gudanarwa tare da yin amfani da siyasa wurin yi wa Allah da al’umma hidima.

“Jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa, NRM ba wai kawai jam’iyyar siyasa ba ce. Tafiya ce wacce ta kumshi dukkanin ‘yan kasa, wadanda har cikin zuciyarsu basu jin dadin irin abubuwan da ke faruwa a kasar nan. Wadanda kuma suka yi imanin cewa ta hanyar dagewa da sadaukarwa za a kai ga nasara, a samar da kasar da ta doru a turbar gaskiya da adalci. Haka kuma mutane wadanda suke da tunanin cewa kasar nan ta dade cikin mawuyacin hali, tare da yin hakuri da shugabannin da ba su san mene ne mafita ba. Wadannan ‘yan kasa na gari ne suka yi dandazo domin ceto kasar daga hannun baragurbin shugabanni. A jam’iyyar ceton al’ummar Kasa, mun yi imanin cewa jagoranci ba yana nufin sai an dora ka akan mukami bane.

“Wannan kaddamarwar ta yau ce matakin farko na ganin an kawo sauye-sauye ga Nijeriya, ta yadda za a fara yin abubuwa yadda suka dace. lokaci ya yi, kuma yanzun ne wannan lokacin.

“Bari na fadi ba tare da wani taraddadi ba, cewa Jam’iyyar Ceton Al’ummar Kasa za ta yi takara a dukkanin matakan ofisoshin siyasa da ake da su a Nijeriya a kakar zabe mai zuwa, wadanda Kundin tsarin mulki ya ayyana, ciki har da kujerar shugabancin kasa. A tashin farko, za mu farad a yin takara a zaben Jihar Ekiti da za a gudanar a watan Yuli da kuma na Jihar Osun wanda za a gudanar a watan Satumbar 2018. Za mu yi wannan takarar ne da zimmar samun nasara. mun yi imanin cewa daga nazarin da muka yi da bibiyan lamurra, mutane sun gamsu da ra’ayoyin wannan jam’iyya, wanda hakan ke nuna jama’a za su yi abin da ya dace domin cin moriyar kudurorinmu da ci gaban kasa bakidaya.

“Za mu tsaya tsayin daka akan kudurorinmu, Za mu tunkari zaben 2019. wanda zai zo da ‘yar manuniya ga ‘yan Nijeriya. za mu yiwa ‘yan kasa hidima da gaskiya da adalci. Sai mun wanzar da dukkan manufofinmu a aikace. Sakamakon sadaukarwa da jajircewa, ‘yan Nijeriya za su samu hadin kai da zimmar kai wa ga nasara ba za mu yarda a maimaita irin kura-kuren da gwamnatocin baya suka tafka ba.

“Mun cimma matsaya a wannan jam’iyya ta ceton al’ummar kasa na cewa za mu gudanar da abubuwan mu su sha bamban da yanayin yadda aka saba gudanarwa a Nijeriya. Dole ne mu ceto wannan kasar, mu sauya mata fasali, mu dawo mata da martabarta a idon duniya. A shirye muke mu fahimtar da ‘yan kasar nan cewa matukar suka jajirce wurin neman halaliyarsu, gwamnati za ta tallafa musu wurin cimma nasarorinsu na rayuwa. Mun yi imanin cewa sakonmu na son kawo ci gaba da raya kasa ya riski al’umma, wanda ke dauke a tambarin jam’iyyarmu.”

Kwamitin Sasanta ’Ya’yan Jam’iyyar APC:

 


Advertisement
Click to comment

labarai