Connect with us

WASANNI

Mun Shirya Yi Wa PSG Dukan Tsiya, In Ji Zidane

Published

on


Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa shi da yan wasansa sun shirya  yiwa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German dukan tsiya a wasan da kungiyoyin zasu fafata a gasar zakarun turai a ranar Laraba.

Ya bayyana hakane a ranar Lahadi bayan kungiyarsa ta doke kungiyar Real Soceidad daci 5-1 a wasan laliga wasan da dan wasan kungiyar, Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye 3 a raga wanda hakan yasa yanzu yanada kwallaye 11 a gasar laliga da ake bugawa.

Ya ce, yaji dadin nasarar da suka samu a wasansu na laliga wannan nasara zata kara musu karfin gwuiwar tunkarar PSG din domin su samu nasara duk da cewa yasan suna cikin wani hali na rashin zura kwallaye a raga.

Yaci gaba da cewa yasan yan wasan da zasu buga masa wasan Paris Saint German saboda haka yagama shiryawa domin bawa duniya mamaki duk da ana cewa PSG din a yanzu ba kanwar lasa bace saboda suna da manyan yan wasa.

A karshe ya ce yasan yan wasansa sun gama shiryawa tsaf domin fuskantar kalubalen dake gabansu duk da cewa yasan akwai bukatar mayar da hankali domin gyara duk wata matsala da zasu fuskanta kafin wasan na PSG.

 


Advertisement
Click to comment

labarai