Connect with us

MANYAN LABARAI

Janar John Shagaya Ya Rasu

Published

on


Jami’i Ne Mai Kwazo —IBB

Dan Kasa Ne Na Gari —Dattawan Arewa

A jiya ne Allah ya yiwa tsohon Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu, Janar John Shagaya rasuwa.

Shagaya ya rasu ne sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyarsa ta zuwa garinsa na haihuwa, Langtang ta Arewa dake Jihar Filato.

An haifi John Shagaya a ranar 2 ga watan Satumbar 1942, ya kuma rasu yana da shekaru 75 da haihuwa.

Kafin rasuwarsa, tsohon Ministan harkokin cikin gidan ya kasance daya daga cikin na gaba-gaba a jam’iyyar APC.

An nada John Shagaya ya zamanto shugaban hukumar gudanarwa ta NIPSS ‘National Institute for Policy and Strategy Studies dake Kuru ta Jihar Filato.

Marigayin ya zamanto Sanata ne karkashin inuwar jam’iyyar PDP a shekarar 2007, inda ya wakilci Filato ta kudu a majalisar dattawa.

A mulkin soji kuwa, Shagaya ya taba rike Ministan Harkokin Cikin Gida a zamanin mulkin Babangida.

Tsohon shugaban Kasa a zamanin mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana jimaminsa dangane da rasuwar Janar Shagaya.

Janar IBB ya bayyana Janar Shagaya a matsayin daya daga cikin hazikai kuma masanan jami’an Sojoji a lokacinsa. Kuma wani jajirtaccen namiji wanda ya sadaukar da komi nasa wurin gina kasa.

Ya ce, “Janar Shagaya jami’i ne wanda ba ya nuna bambanci a tsakanin al’umma, ba ya ruduwa da bambancin addini, ko kabilanci a yayin da yake gudanar da aikinshi. rasuwarsa babbar rashi ne ga nijeriya gabadaya.” in ji IBB

A nata sakon ta’aziyyar, Kungiyar Dattawan Arewa, ta bayyana cewa wannan rasuwar Janar shagaya a matsayin wani lamari mai kidimarwa. ta kuma yiwa mamacin shaida a matsayin dan kasa na gari mai kaunar ci gaban Nijeriya.

Sakon na Kungiyar dattawan arewa ya bayyana cewa; “Marigayi Sanata Dakta Shagaya jami’i ne mai dattako da natuswa a lokacin da ya yi aikin soja. Kafin yayi ritaya sai da ya kai mukamin Janar na soja, kuma tsohon ministan harkokin cikin gida. Bayan yayi ritaya ne ya koma harkar karatu inda ya samu shaidar zama dakta a fannin tsaro da tsimi. Wanda kuma daga bisani ya shiga harkar siyasa a shekarar 2007.

“Kungiyar Dattawan Arewa na yi wa iyalan Shagaya ta’aziyyar wannan rashi, gwamnati, al’ummar jihar Filato da sauran ‘yan Nijeriya bisa wannan rashi da aka yi.”

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai