Connect with us

KASUWANCI

Ingila Za Ta Saka Naira A Jerin Kudaden Da Za A Iya Kasuwanci Da su A Waje

Published

on


Hukumar hulda da kudaden kasashen waje ta kasar Ingila, ta amince da a saka takardar kudinmu ta Naira a cikin jerin kudaden da za a iya yin cinikayya da su a tsakanin kasashe.

Da hakan, takardan kudin namu na Naira za ta kasance ta uku a cikin kudadenmu na yammacin Afrika da hukumar kudin ta Ingila ta amince da su wajen yin huldan cinikayya da kasar ta Ingila, in ji rahoton.

Kasar ta Ingila da takwarorin ta na kasashen Turai, sun cimma wata yarjejeniya a watan Disamba, wacce ta yarje da su ci gaba da tattaunawa kan harkokin kasuwanci a tsakaninsu.

Hakan kuma alami ne, wanda ke nu na girman kiman da kasar ta Ingila ke ganin Nijeriya da shi. Hakan zai kuma kara girman kafofin kasuwanci da kuma hanyoyin zuba jari a tsakanin kasashen biyu.

“Wannan yana nufin, kamar yadda mutum zai iya yin cinikayya da kudin na kasar Ingila, to hakan kuma zai iya yin cinikayyansa da Naira a kasuwannin waje na kasar ta Ingila. Hakanan kamfanonin Nijeriya da suke cin bashi a takardar kudinmu ta Naira, za su sami tagomashin kariya daga kasar ta Ingila.

“Wannan zai kuma bayar da daman rage hadarin da ke tattare da yin kasuwanci da kudaden na kasashen waje, ta yanda a yanzun duk ana iya yin hakan da Bankunanmu na nan cikin gida.”

A wata sabuwa kuma, Babban Bankin Nijeriyan (CBN), a jiya, ya sake zuba jarin da ya kai na dala milyan 325,64, a kasuwannin cikayyan kudade ta SMIS.

Kamar yadda rahoton hakan daga babban Bankin ya nu na, za a yi amfani da kudaden ne a fannukan Noma, Jiragen sama, albarkatun Man Fetur da kuma kayan gyaran manyan mashinan masana’antu.

Idan dai ba a manta ba, a watan Janairu na wannan shekarar ta 2018, Babban Bankin na Nijeriya, ya zuba jarin da ya kai na dala milyan 304,4, a wannan kasuwar ta musayar kudaden waje a tsakanin Bankuna.

Babban Bankin ya yi hakan ne, domin dakile sarkakiyar da ta afku a wannan sashe a farkon zangon shekarar 2017, a sabili da aikace-aikacen masu safarar kudaden da makamantansu. Wanda a wancan lokacin, har ta kai ga faduwar kudin namu na Naira kasa warwas, wanda ya kai ga ana sayan dalar Amurka guda da Naira 525, a yanzun hakan dai, kudin namu ya karfafa, inda dalar ta daidaita a kan Naira 360, a kan dalar guda a kasuwannin na duniya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai