Connect with us

BIDIYO

Hukumar Tace Finafinai Ta Na Tara Wa Ganduje Makiya Ne – Salisu Officer

Published

on


An zargi hukumar tace finafinai ta jihar Kano a karkashin jagorancin Malam Isma’il Na’abba Afakallah da janyo wa gwamnatin jihar Kano bakin jini a wajen mafin yawan masu sana’ar shirin finafinan Hausa, inda hakan ke tara wa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, makiya a siyasance.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin sakataren hadaddiyar kungiyar masu shirin fim na Kannywood (MOPPAN) reshen jihar Kano, Malam Salisu Muhammad Officer cikin wani jawabi da ya yi a shafinsa na Facebook da ke yanar gizo a karshen makon nan, inda ya ankarar da gwamnan jihar irin hatsarin da Afakallah ke neman jefa gwamnatin jihar ta jam’iyyar APC.

“Maimakon hukumar tace finafinai su kalli ta yadda za su sulhunta wasu yara da ke wannan masana’anta wadanda ke zagin gwamna a wake da iyalansu da jawo kowa a tafiyar Gandujiya, yanzu ya kasance hukumar ce ta ke jawo wa gwamnati sababbin bakin jini,” in ji Salisu Officer, wanda ya yi karin haske kan badakalar Rahama Sadau.

Ya ce, “maganar Rahama Sadau ba laifin shugabancin kungiya ba ne; magana ce ta daga kin gaskiya sai bata. Rahama ta rubuta wa kungiya wasikar neman afuwa kwanan nan, kuma ba wanda ya ce za a yi ma ta afuwa ko ba za a yi ma ta ba. Mun zauna mun neme ta, don mu samu wasu bayanai daga bangarenta.

“Amma ba ta nan ta yi tafiya ta watanni, sai mu ka jingine lamarin, amma mun sami tartibiyar magana a kan cewar hukumar tace finafinai a gwamnatance ta yi ma ta afuwa kuma za ta cigaba da duba finafinanta duk da wannan takarda da mu ka sanar mu su su ka ba mu amsa.”

Officer ya nuni da cewa, wannan abu da hukumar ta aikata na yin gaban kanta ya haifar da rarrabuwar kai da rashin da’a a tsakanin ’yan Kannywoood, ya na mai cewa, “wannan mataki yaba wa wasu dama su ke zagin shugabanci a kafafen sadarwa kamar yadda ku ke gani. To, wannan ba komai ba ne a tsarin kungiya, sannan ya kamata jama’a su sani cewa, komai ya na da iyaka.

“Maimakon hukumar tace finafinai su kalli ta yadda za su sulhunta wasu yara da ke wannan masana’anta wadanda ke zagin gwamna a wake da iyalansu da jawo kowa tafiyar Gandujiya, yanzu ya kasance hukumar ce ta ke jawo wa gwamnati sababbin bakin jini, (duk ga cewa) a kungiyance mu na iya kokarinmu mu ga ’ya’yanmu sun zama masu biyayya ga shuganni (na jiha) masu tarbiya kamar yadda tsarin mulkin kungiya ya tanadar, wanda shi ya jawo hukuncin da a ka dauka a kan Rahama.”

Daga nan sai sakataren na MOPPAN ya ja hankalin hukumar da cewa, ta dawo kan tafarkin tsarin aikin gwamnati, kamar yadda dokoki su ka tanada, ya na mai kara wa da cewa, cigaba da bijirewa yin hakan ya na iya haifar da da mai maras idanu ga gwamnatin Khadimul Islam Mai girma Ganduje.

Officer ya kuma ja kunnen hukumar a karkashin Afakallah da cewa, “aikin gwamnati tunda mu ka taso mu ka shige shi mu na yi mun san ba sana’ar ‘interior decoration’ ba ce sannan ba ‘set design’ ba ce bare idan ka ga wani (abu) bai yi ma ka ba ka rushe ka gyara.

“Gwamnati ‘laws, procedures’ da ‘limitations’ ce, wadanda kowa a haka ya same su. Idan kuwa wata rana ta sa wani ya canza ‘there will be a day that it will surely backfire’.”

Idan dai za a iya tunawa, tarihi ba zai manta yadda zafin takaddama tsakanin tsohon shugaban hukumar tace finafinai na jihar, Rabo Abubakar Abdulkarim, da ’yan Kannywood ya haifar da zazzafar adawar da ta kai ga masu sana’ar ta fim din Hausa su ka rika yiwa gwamnatin zambo da alkaba’i iri-iri ba; sannan su ka koma su ka tare a gindin tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, lamarin da a karshe ya kai ga faduwar gwamnatin dungurigum a 2015.


Advertisement
Click to comment

labarai